HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sallamarta yasa shi daga kai yare da amsawa,ganinta a yanayin da bai zata ba yasa shi kasa karasa sallamar. Ya yi saurin kau da kai zuciyar sa na bugawa,tuni ya ji ya rude musamman da ya jita dab da shi.

Hannu tasa ta karbi ipad din ta ajiye a gefe ,ta dare bisa cinyarsa tare da jawo shi jikinta ta rungume shi . Nan ya bata hadin kai ,shima ya kara mannata a jikinshi sosai yana shakar kamshi tare sauke wani irin ajiyar zuciya yana jin tsananin son ta da sha’awarta suna shigar sa.

Cikin muryar rada idon sa a rufe yana manne a jikinta yace…

Farida kin amince dani,ba kya tunanin dee…..

“” shhhhhh”

Ta fadi gami da saurin rufe masa baki tace ,,

Karkace komai,na mika rayuwata da kaina ga mijina wanda shamsu shine mijina,gaskiyar rayuwata. Ni matarka ce,kanada hakki da damar yin duk abinda kake son yi dani,buri na a yanzun kawai in kyautata maka . Ina neman yardarka ,saboda Allah ya yarda dani.

Nan ya dunga sauke ajiyar zuciya ,shi kadai yasan me yakeji a zuciyar sa da jikinsa.

Bai bata lokaci ba ya dada cusuwa a jikinta ,tuni suka manta komai suka fada wata duniya. Farida ta mallakawa mijinta shamsu kanta ,, yayin da shimanya mallaka kansa da komai nasa ,yana mai sa.mata albarka gami da alfahari da ita .

Tuni suka rungumi auren su suka rike hannu bibbiyu,suna kula da juna tare da tarairayar juna,suka bude sabon shafi na rayuwar su,iyaye na sa musu albarka.

Ba wanda ya kai mama farin ciki da kuma fargaba ,a kullum Deeni ya yi waya sai shamsu da farida sun tsinci kansu cikin sabon  tashin hankali . Sai dai a kwana a tashi har sun saba da hakan ,don kuwa mahaifin deeni ya hana ko da wasa a fada masa gaskia ..

Lokacin da karatu yayi wa deeni yawa ma yana dadewa bai yi wayar ba.mahaifinsa yana yawan ziyarar sa,yana ganin yadda ya cigaba sosai a karatunsa,ya yi nisa kuma tana kokari sosai ,ya kwantr da hankalinsa,,saboda ko da wasa bai san me ke faruwa ba. Kullum da burin auren farida yake kwana yake tashi……..

Bye

Mu kwan lahia jama’a

Sumy luv ????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

25

Can dai deeni ya yanke hukuncin zuwa gidan dan uwansa ,ya cewa direba ya juya. Dama ya riga yasan gidan da mahaifinsu ya bawa shamsu,don haka ya yanke hukuncin wucewa gidan shamsu ya ga mai sunansa Deeni da dan uwansa,ya yi masa murnar aure,ya ga kalar matar da yayansa ya aura…????

Yana daria ya fito hannunsa dauke da akwati wanda cike yake da kayan sawa da kayan wasa na mai sunansa Deeni karami. Nan ya cewa mai taxi din ya jirashi zai shiga ciki ya amso masa kudinsa. Nan ya yi ciki ya bar sauran kayansa a motar.

Tura gate din gidan ya yi yana jan akwatin da ke hannunsa,yana ratsa tsakiyar gidan,yana kallin ginin da cikin gidan yana murmushi. A ransa yana fadin,kwannan shima zai mallaki nasa gidan tare da farida.

“Anya kuwa in na auri farida ina da wani sauran buri kuwa a rayuwa?

Yana cikin wannan tunanun yaci karo da security na gidan wanda dama ya shiga ciki kai wani sako ne ,ganin Deeni yasa shi washe baki yana dariya saboda dama tsohon mai gadinsu ne Alh ya bawa shamsu shi yana masu gadi.

Nan ya karbi akwatin tare d a bude masa kofar falo,anan ya ci karo da Deeni karami a tsakiyar falon ,an baza masa toys yana wasa .

Da sauri ya isa gare shi yana dariya,yasa hannu ya daga shi, Deeni kuwa kamar ya sanshi ya wangale baki yana dariya.

Deeni yana zura masa ido yana kallon irin kamar da yake yi da shamsu,son yaron da kaunar sa yaji ya shiga zuciyar sa,nan ya dinga masa wasa yana cilla  sama shi kuma yana daria.

Nana ya bude akwatin ya ciro masa sabbin toys din da ya siyo masabya bashi,anan wurin deeni ya zauna yana ta wasa da Deeni. Shi dai megadi ya tafi ya barsu don Deeni ya hana ya musu magana ,ya ce suprise zai basu.

Tsawon minti goma yana da Deeni har ya soma mamakin me yasa yaji tsit ba wanda ya fito duba Deeni karami shi daya?

Nan ya daga shi ya nufi falon ciki yana fadin…

” zanci tarar iyayenka ,sun barka kai kadai na tsawon lokaci ba wanda ya leko ka,kar ka damu ga uncle Deeni ta dawo ,zai dauke ka ya tafi da kai su kuma suyi ta zaman su a ciki….”””

Deenibdai sai dariya yake masa tare da fadin mommy ko daddy.

Ya ce “uncle zaka ce,uncle Deeni ”

Nana ya yi kokarin kwaikwayon sa ya fada cikin maganar yara ‘yan koyo. Shekararsa biyu amma ba baki sosai,sai girma da yayi kamar dan shekara uku.yaro ne lafiyayye mai ki da karfi. Da alama ya samj kyakkyawan raino da kula daga iyayensa.

” Salamu Alaikum ,mutanen gidan suna nan kuwa ko sai na tafi muku da yaro za ku fito?

Deeni ya fada yana kokarin kutsawa cikin daya falon tare da daga labule.

Wani abu idonsa ya gane masa me kama da mafarki ko almara,,wani abu da kwakwalwa ko hankalinsa ba zai iya dauka ba.

Farida ya hango kwance jikin shamsu ,shi kuma ya rungumota yana ta kokarin massaging kanta,yana matsa mata kai alamar yana mata ciwo ,tana ta zuba shagwaba.

” Daddy kaina zai tsage,daddyyn deeni inajin murda;;””

Yi hakuri mommyn Deeni,zai bari,kwanta ina ci gaba da matsa miki tunda kin sha magani zaki samu bacci yanzu,kiyi shiru kar ciwon kan ya karu”

” Daddy deeni fa ?  Ta fada cikin shagwaba da kuma ciwo .

Yana can yana wasa ,ki samu bacci zan fita da shi in kaishi gun mama tunda ka kya jin dadi. Wannan babyn namu dai da yazo yanzu yana wahalar min da farida na,sai mun masa bulala in yazo.

Tayi murmshi ta ce , Ya shamsu macw zamu haifa mai sunan mama,kaga kuwa ba a yiwa mama bulala ba,in kuwa ka mata sai hannunka ya nade”

Dariya sukayi duka,sam basu kula da Deeni da ke tsaye a kansu ba,wabda tsananin firgita da kaduqa da abinda ya gani sai da ya saki deeni ya sha kasa ,bai ma san yayi hakan na. Gaba daya hankalin sa ya bar jikin sa,baya hayyacin sa.

Ihun deeni ya jawo hankalinsu ,shamsu ya mike a firgice gabansa ya mummunan faduwa,yayin da farida ta ji wani irin hajijiya ,sabon zazzabi ya lullubeta ,tsananin firgita da ganin Deeni bata san lokacin da taji mararta ta juya ba ,wani azabar ciwo taji ya kamata,tuni jini ya soma bin kafarta yna gudu ,alama ne na cewa cikin jikinta wanda bai wuce wata biyu ba ya bare saboda tsabar tsorota da tashin hankali data shiga. Haka nan shamsu duk kokarinsa ya kasa ko da motsi a wurin ,kansa sunkuye ya kasa hada ido da Deeni,ya kasa ko da motsawa balle yaje ya daga deeni dake ta kwala ihu a wurin

Farida dai dakyar ta samu ta zauna bisa kujerar da suke da sabida hajijiya da wani abu da taji yana yawo a tsakiyar kanta ,ki ciwon marar ma bata lura da shi ba sai dai tabbas tasan abu na bin kafarta wanda bat san menene ba.

Tsawon minti biyar suna cikin wannan halin,duk wani farin ciku da murnar da jin dadin da ya dawo da shi nigeria sai da ya neme shi ya rasa,kunci ,bakin ciki ,takaici, da bacin rai ya maye gurbin su.

Halin da ya gansu ya ganar da shi dukkan abinda yake faruw ,ya fahimci cin amana da. yaudarar da farida da shamsu suka masa.wani abu da bai taba zata ba balle tsammanj ,ko a mafarki ko. A tunaninsa bai taba giftawa ba.

Wani abu yaji ya tokare shi a zuciyarsa,haka ya dinga jin wani azabar radadi a kansa,wani irin azabar ciwo da bai taba jin makamancin sa ba . Amma duk da halin da yake ciki sai ya sa hannu ya dauki Deeni ya nufi gabansu ya mika musu shi,sai dai dukkansu ba wanda ya iua motsawa balle ya sa hannu ya karbe shi. Hakan yasa ya ajjye shi. Akan cinyar farida ya juya ya fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button