MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana shirin barin falon ya ci karo da su umma tare da baba ,da kuma Abba da umma ,wato mahaifiyar farida.
Ashe Alh Umar ya yi waya can America aka ce masa ai tun tuni Deeni ya taho nigeria,tun daga nan hankalin sa ya tashi ya aina tsawon lokacin da aka ce masa ya taho yasan tabbas ya iso,haaka nan tunda bai je gida ba ko gidansu farida ,to tabbas yasan gidan shamsu zai nufa. Ranar da suke gudun zuwanta ne dai ta zo.
Tunda mama ta sami labari hankalinta yai mummunan tashi,Alh ya tattaro su duka don su yiwa Deeni bayani,su fahimtar da shi ,wanda a zatonsu zai fahimta,(hmmmm atunaninsu akwai wani bayani da deeni zai fahimta ne????),to amma mama tasan dama za’a rina…..
Mama na ganinsa da yanayin da ya shiga hankalinta ya kara tashi,ta jawo shi ta rike gam tana fadin .
Deeni addu’a zaka yi kaji,ka dinga maimaita hasbunallahu wa niimal wakil,ko la’ilaha illah anta subhanaka inn kunti minazzalimin””
Gaba daya kansu suka yi kowa da irin abinda yake fada masa ,da irin bayanin da suke masa . Sai dai deeni ya dawo kamar zararre,tamkar mara hankali,kallon su kawai yake bakinsa na motsi amma baya ma jin me suke fadi balle ya gane.
Ya kalli mahaifiyarsa yace,,Mama kinada kudi ki bani in biya me mota lr da ya kawo ni ?
Deeni na biya shi,har mun sa ya sauke maka kaya ya sa a motar mu,zo mutafi gida””
Deeni ya kalleta,”Mama farida ,jini na zuba a jikinta ku kaita asibiti”
Sai a lokacin suka mai da hankalin su kanta,umma ce da mama sukayi kanta,suka dagota hankalinsu a tashe suna salati,sukai mota da ita. Tare da Abba suka tafi,yayin da baba ya tsaya tare da shamsu da deeni,ya jawo su duka.
Bayani ya fara da nasiha ,da kuma fadin ba laifin shamsu da farida bane ,su suka yi hadin nn saboda wani dalili nasu,su kuma suka musu biyayya.
Bana son ji Baba ,duk wani abu da zaka fadamin ko wani dalili bana son ji,ka rike dalilinka,duk abinda zaka fada ba zai cire min ciwon da nakeji yanzu a zuciyata ba. Kasan me nakeji Baba ? Da kasani da baka tsaya yi mun wani magana ba …
Baba ka sama mun magani ,ciwon da nakeji a kwalkwata da zuciyata yanzu za su iya kashe ni,Baba yanzu ina jurewa amma anjima ba zan iya jurewa ba. Baba zai kashe ni ka kaini asibiti ko ka min addu”a ,kamin duk abinda zaka iya mun ko zan samu saukin ciwon da nakeji …..
Kai Babana nw ,ME SONA ,me yanke dukkan wani hukunci na rayuwa saboda ka kawo ni duniya ,ka bani ci da sha, ka kula da lafiyata da karatuna ,ya zamar min dole in maka biyayya.
Nayi biyayya baba da abinda kayi ,sai dai baba ka taimake ni wannan abinda nakeji baba ban taba jn irinsa ba,baba bana ganinka sosai ,duhu na rufe mun ido,ina jin duniyar na zagawa dani ….
Kama kansa yayi da karfi,basu ankara ba sai ganinsa sukayi ya fadi ,ya zube kasa a sumeeee………….
????????????????????????????????
Allah ya bamu alkairi jama’a ,,dan wlh nima hannu na rawa yake kar ayo biyu,,ga deeni a sumee nima wayata karta fadi……
Sumy luv????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????
writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤
ASSALAMU ALAIKUM
Yan uwa!! Mata ce ta cewa mijinta ya saketa,shi kuma yaki ,hakan yasa ta dakko wuya wai idan be saketa ba zata kashe kanta.
Shi kuma ganin haka yasashi sakinta. SHIN YAYA HUKUNCIN WANNAN SAKIN DA YAMATA ? TA SAKU KO BATA SAKU BA ?????????
Sai naji daga gareku….nagode
27
Wasa gaske al’amarin Deeni ya tsananta,wani lokaci ka ganshi lafiya wani lokaci ya haukace musu,gana daya baya hayyacinsa,bai san me yake yi ba,hankalin iyayensa da masoyansa ya kai kokuluwar tashi. Daga karshe Alh ya fita dashi kasar india ,anan aka ci gaba da duba lafiyar kwakwalwar sa,saboda abin yamatukar raba masa kwakwalwa,kwakwalwarsa ta kasa dauka da jurewa wannan damuwar.
Ana duba lafiarsa a asibiti kuma ana masa rokon Allah,tare da sauke masa Alkur’ank ,da haka da taimakon ubangiji Deeni ua soma dawowa hayyacin sa. Sai ya zamana ya daina surutu tunda suka dawo gida,ba ya kula kowa ,baya cewa kowa komai. Kullum yana zaune a dakinsa,baya fita sai dai wani ya tafi masallaci ya dawo. In an kai masa abinci wani lokaci zai ci ,wani lokaci kuma haka abincin zai kwana wani ya tarar da wani.
Lokaci guda rayuwar Deeni ta canja ,ya yi baki,ya rame ,kuma baya aikin komai sai kwanciya da zaman gida. Ya dawo rayuwar sa sam bata da wani manufa.
A duk lokacin da Deeni zai kwanta bacci,to yakan rufo ido ya hango shi da farida,lokacin da hoton farida da shamsu zai bayyana a fuskar sa yakan yi saurin bude ido wanda a nan za su rine suyi ja,yaji kansa ya fara sarawa ,ya kama kai da kirji . Wani lokaci sai dai a shigo a same shi a sume.
Halin da Deeni ya shiga ya daga hankalin kowa a zuri’ar su,musamman iyayensa da kuma shamsu da farida. Wani lokacin mahaifin sa sai ya zubar da hawaye saboda bakin cikin halin da dansa ya shiga. Rayuwarsa ta dawo useless bata sa wani amfani ,ya yi da na sani tare da jin bakin cikin abinda ya yi.
Kulum yana binciken asibiti ko masu maganin gida da za su dawo da shi dai dai,sai dai abu guda yake ji kullum,shi ne abin ya mugun taba masa kwakwalwa da zucya,wanda fitar sa a wannan hali sai a hankali . Sai dai dayawa masu magani ko likitoci na bashi shawarar cewa ya canja masu wuri,wato ko dai ba ya bar garin ko kasar ,ko dai wani wurin da zai nesanta deeni da rayuwar da yayi ta baya.
Wannan yasa Alh Umar ya tattara nasa ya nasa da kasuwancinsa ya raba su biyu ya koma lagos ,ya yin da ya barwa Shamsu sauran kasuwancin sa a kaduna .
Alh Umar ya tattara iyalinsa,wato hajia A’i da Deenj da lukman suka koma garin lagos ,ya bar Arewa gaba daya. Saboda ya san Deeni yana da sha’awar zama a garin ,sannan yana ga zai ji dadin tafiyar da kasuwancin sa. Haka Deeni zai samu kyakkyawan canjin yanayi ,yayin da ya bar Shamsu da Farida a kaduna.
Tabbas Alh.Ahmad ya yi bakin cikin rabuwa da abokinsa,makwabcinsa,wanda yake kamar dan uwansa Alh. Umar . Ya daukar masa manar dansa da kuma hakkin kula da shi da kasuwancin da ya bar masa,da ya dinga kokarin sa ido inda yaga ya karkace ya yi masa gyara.
Farida da mama sun rabu cikin kuma tare da bakin cikin rabuwa da juna.
*** *** *** **** **
“”ALHAJI ! ALHAJI !!
Haj. A’i ta shigo falonsa tana kwada masa kira .
Ya kalleta a firgice ,” lafiya cikin daren nan ?
Ta mika masa wani farin takarda ,ya kalleta cike da mamaki.
“Menene wannan ?
Tace ,Address ne na samu,inda zamu kai Deeni,yanzu na kasa bacci na kunna tv kenan naga suna tallen wurin nan. Na lura masu matsala irinta Deeni sun samu waraka..””
Ya kalleta ransa bace ,ya ce,”Dana ba mahauci bane ,kuma ba dan shaye shaye bane da za a kaishi REHABILITATION CENTER
Cikin nuna damuwa Haji. A’i tace. Alhaji ka duba ka bincika ,wannan wurin ba mahaukata ko ‘yan shaye-shaye bane,kafin in baka sai da nayi bincike naji komai akan su. Abinda yafi jan hankalina gare su ahi ne,sun hada da Addini da kuma magungunan musulunci . Deeni yana bukatar taimako na Addini da na asibiti duka,wanda duk sun hada.
Dakyar ta samu ta shawo kansa ya yarda zai binciko,in ya masa yadda hankalin sa zai dauka to zai yi tunanin tura Deeni wurin…..
Gaya nan ayi breakfast????????????
Sumy luv????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????