HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

=================== GIDAN NOVELS ====================================

26

Alh Umar ya mugun rudewa ,rabon sa da ya zubar da hawaye har ya manta,amma a wannan lokacin sai da ya zubar da hawaye,hankalin sa ya mugun tashi.ya tsorata da lamarin Deeni,haka shamsu duk jikinsa ya mutu,ya rasa me ke masa dadi,ga halin da Deeni ke ciki ,ga na farida.

Tare suka nufi asibiti dashi,in da faridan take nan suka je,sai dai ita an dace an shawo kan alamarin ,sai dai tayi barin cikin har an mata wankin ciki tare da bata magunguna da allurai.

Tana kwance tana hawaye ,mama rungume da ita tana bata baki da nuna mata ta ci gaba da dauriya da cijewa kamar yadda tayi a baya,,zai wuce.

Umma rike da Deeni karami tana kallonsu,ta kasa fadin komai sai tsabar tausayin ‘yarta da ya kamata,ta ahiga halin tsaka mai wuya.

Nan ta matsa itama tayi mata nata nasihar ,sannan ta ce zata wuce gida da Deeni,sannan zata shirya musu abinda za su ci ta aiko asibitin. Mama kuwa tacw zata zauna da ita.

A nan ta samu damar kwaniciya a cinyar mama tayi kukanta sosai,mama bata hanata ba sai dai bata fasa lallashi da bata baki ba.

Suna cikin wanann halun shamsu ya iso yana rude ,mama ta kalle shi tace,,,,

Ka dauki abin nan a hankali,komai ta yi zafi magninsa Allah.”

“Mama Deeni yana kwance a emergency tun dazu muna can likitoci a kansa sai yanzu muka samu ya farfado,”

Hawaye ne ya gangaro masa,ya ce,”Mama Deeni yana cikin wani hali wanda mu ne dalili.”

Da sauri mama ta mike ba tare da ta karasa jin me yake fadi ba ta fita wurinsa,Shamsu ya matsa gaban farid yana fadin . “Ban baki kulawa ba lokacin da kike bukata,saboda Deeni yana bukatar kulawata fiye sa ke. Farida ban kaea sanin cewa bamu kyautawa Deenj ba sai yau da naga halin da yake ciki ,halin da ya shiga yana cikin tsanani da firgita tare da zafin zuciya da kwakwalwa””

Ta fashe da kuka ,”Ya shamsu ba abinda zai samu Deeni ko? Ya shamsu munci amana..”

Ta fada a lokaxin da ta kara fashewa da kuka .

‘Ya Shamsu ba zan iya fuskantar Deenj ba har abada,fatana Allah ya bashi lafia,yasa kuma ya manta sa ni da wannan cin amana da muka masa.”

” Ba mao sauki banw farida ,tabbas bamu kyauta masa ba ,har ga Allah bamu kyautawa Deeni ba ”

Nan suka lallashi juna ,daga karshe Shamsu ya kama ta suka nufi gurin Deeni a emergency.

Tana hango shj ko daga nesa ne,hango shi tayi yana kwance idonsa biyu sai dai ya kau da kai hawaye kawai ke zuba masa,ransa a mugun bace,hankalinsa a tashe.

Tausayinsa da tsohuwar soyayyar sa taji sun taso mata suna tsuma zuciyarta,tayi saurin dafe kirji tana hawaye,ta lura ya kara girma da haske hade da wani irin kyau duk da yana cikin tashin hankali.

Ta lumshw ido tana jin wani abu mai ciwo da radadi yna ratsata.

“Ka yafe min Deeni na ci amanar kauna ,sam ko kadan ban yi fighting wa soyayyar mu ba,nayi saurin mika wuya . Na cika makiyarka da nayi sanadin jefa ka a cikin wannan halin,nasa ka dandani wannan zafin zuciyar. Allah ya baka wacce ta fini,ni kam ban dace da kai da rayuwar ka ba da soyayyarka,tunda can ma kila shiyasa Allah ya rabaka danj. Na tabbatar Allah zai baka wacce tafi dacewa da kai,sai dai ka sani Deeni ba zan daina sonka ba ,hae abada soyayyar ka zata kasance a cikin karkashin zuciyata. Sai dai zan danne ta in ci gaba da rayuwa ta da mijina gami da faranta masa iyakar iyawa ta..””

Muryar mama ce ta katse mata maganar zucin da take yi,ta mai da hankalinta kansu.

Mama ke masa magana cikin kwantar da murya,tana shafar kansa kamar karamin yaro tace,,”” Deeni kayi hakuri ,bani da abinda zan iya baka sai hakuri ,ba wani bayani ko kokarin kare kanmu da zan maka. Magana guda ce ,mun maka laifi duk da muna manya kai kana karami ,amma min maka laifi,mun zalunce ka,kayi hakuri ka yake mana,kar kayi fushi damu.”

Deeni yayi murmishin kardin hali yace,”Fushi “” ? Da wa zanyi fushi ? Kima ni waye da zan yafe muku ? Ku iyayen mu ne,kuna da damar yin yadda ku ka so. Da mahaifin farida zanyi fushi don ya zabawa ‘yarsa miji ? Ai bani da hujja.

Da farida zanyi fushi ,masoyiyata ,wacce ta min alkawarin soyayyarta da kanta ,wacce tun muna yan kanana muke wa juna son da bamu san irinsa ba ? Ko da yayana da na bawa amanar masoyiyata ,wanda yasan duk wani sirri da tarihin son da nake wa farida ? Ko da nahaifina da ya yaudare ni ya min karya? Ko da mutumin da na dauke shi tamkar mahaifina yace min ya mun alkawarin bani yarsa har inje in dawo ? Ko da mamana mahaifiyata da ta boye min gaskiyar magana?

Mama da wa zanyi fushi a cikinku ? Kuma meye riba ta in nayi fushi da ku ? Abinda ya faru zai canja ne ?

Ya mike cikin zabura da zafin zuciya ,ya ce.

“Damuwata shine yadda zan share wannan mummunan al’amarin daga kwakwalwata da zuciyata ..””

Ya kalli likita dake tsaye a kansa tare da mahaifansa ,ya ce

” Doctor ,kaga nima doctor ne ,likita ne cikakke,sai dai ban kware ba,ni ba professional bane,hala likiminka ya kai inda za’a iya yiwa mutum wankin kwakwalwa?ka  bude mun kwakwalwata da zuciyata ka wanke mun su tas ,ina son manta dukkan mutanen nan a rayuwata,bana son tuna su balle in tuna abinda ya faru. Kaga wannan painful memories din abinda ya faru dani ,ina so ka bude ka wanke mun su duka saboda ba zan iya rayuwa da su ba,suna min ciwo sosai ,baza su barni in rayu ba ,ni kuma inaso in rayu. Please Doctor ka taimake ni..””

Tun yanayi a hankali har ya fara da tsawa,lokaci guda ya haukace musu,da kyar ak samu aka masa allurar bacci ya kwashe shi.

Ba mama ba har baba ya shiga cikin mummunan tashin hankali da Abba ,har suka yi nadamar abinda suka aikata masa.

Mama tana kuka tana tofa masa addu’a haka daga farida har shamsu kuka suke bamai lallashin wani…………..

Hmmmmmmmmmm????????

Sumy luv????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting buSAADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

28

Ruwan sama ake tsugawa sosai ruwa irin na lagos,wanda idan ya fara sai anga tsawarsa. Iska ce me hade da feshin ruwa ya shigo ta windo ya wanke mata fuska,hakan yasa tayi saurin bude ido hade da addu’a.

Ta mike ta nufi jikin window din ta lumshe ido tana shakar daddadar iskar da ke dukan fuskarta tana jin yana ratsa ta ,yanayin da tfi so fiye da kowanne yanayi kenn.tuni taji zuciyarta tayi mata fari,ta tsinci kanta cikin wani nishadi.

Karar door bell ne da aka danna ya ja hankalinta zuwa kofa,Doctor Bahijja kenan tayi saurin zarar hijabinta ta nufi kofar falon , a nan mai gadi ke fada mata suna da baki da ke son ganinsu,sunje cikin asibiti aka ce basu iso ba ,shi ne suka biyo su gida,sun ce wai yana da matukar muhimmanci suga likita.

Tayi mirmuahin da tasaba wanda kullm yana makale a fuskarta ,ta ce

” Kaisu falon baki,kace su jira ko ?

To madam

Ya amsa tare da juyawa ,duka cikin harshen turanci suke maganar..

Nan ta juya ta nufi dakin barcinsu,kai tsaye ta same shi har yanzu bacci yake duk da iska mai sanyi da ke ratsa dakin ,yana ratsa fuskar shi bai sa shi farkawa ba .

A hankali ta sa hannu tana jan bargon da yake lullube tana murmushi ,amma sai ta ga ya dunkule guri guda ya ci gaba da baccin sa tamkar wani baby.

Ta kalli kyaykkyawar fuskar sa me kunshe da annuri da lafiya ,tare da kwanciyar hankali . Soyayyar sa taji ya kara tasiri a zuciyarta ,cikin muryar shagwaba tace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button