MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tuni jikinta ya mutu,taji wani irin sonsa me karfi yana tsuma ta ,ta dinga jin tamkar ta rungume shi,ra zauna a jikinsa har abada.
Ta kwantar da kai tana masa kallon kauna tace ,,” deeni kamin alkawari as long as ina rayuwarka bazaka sake karanta littafin MISBAH ba ,komai koyarwarsa ,komai ilimin dake cikinsa ,saboda littattafan MISBAH sun zama kishiyoyina ,shi ne abu na farko dana taba gani yana kokarin janye hankalinka a gare ni. Deeni bana son ganin abinda zai janye hankalinka daga kaina….
Copied sumy luv ❤❤
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Writting by SA’ADATU WAZIRI
COPIED BY SUMAYYA SA’AD (sumy luv❤)
03
Kamar yadda kace baka da damuwa da MISBAH sai brains dinsa ,to nima bani da damuwa dashi,damuiwata shine deeni,in kuwa labaransa na dauke hankalin deeni a kai na ,to inada matsala da hakan ,don haka inada matsala da brain dinsa,da intellegent dinsa,i have a problem wit his stories”
Ta dan fadada murmushinsa tare da fadin “” anyi an gama ,daga yau bani ba karanta littafin MISBAH ;nayi alkawari””
Tayi daria har da tsallen farin ciki ta ce ” shiyasa nake son deeni na ,he care for me yana jin maganata ya damu da farin ciki na ,,my deeni is d best”””
Dariya yake mata shina yace my farida is d best”ki tsaya a gabana in ta kallonki ina jin dadi . Haka kawai kin hanani jin dadi da sukuni ,kwana uku ban ganki ba ,meyasa kika ki zuwa ki ganni ? Kinsan baba kulle yakemun inmun fara jarrabawa ya hadani da wannan manya manyan takardun ina karantawa, bana ganewa,daga na bude littafin sai inga furkar farida tanamun murmushi,bana iya komai sai kallon fuskarki a littafin “tayi murmushi tace meyasa baka dirko ta window ba ?
Yace ” so kike in karye a ce mijinki gurgu?
Tayi daria tace “to ina ruwansu ,inma gurgun ne ba mijina bane ? Deeni na ne ni daya ”
Yace haka farida na ni daya “”
Farida ta dubeshi taxe deeni yaushe zamuyi aure ? Ya kalleta ya ce ko yau Abbanki ya shirya aura minke zan aure ki ”
Ta masa hararar wasa ta ce ina zaka ajiyeni baka da gida baka da aiki ? Ya ce,shine damuwarki ? Kalli girman dakin nan bazai ishemu ba ? Ya jawota ,”zo kiga yawan abincin da mama take samun kullum so uku so hudu a rana ,ko ke rumbu ce zaki koshi. Awani lokaci mama nasamun abinci fiye da kala hudu a rana ,wani lokaci ma bana ci ake fita dashi .
Bari in fada miki ni mrs deeni NURADDEN dan gatan mama da baba ne auren gata zatamun dakina ya ishemu,abincina ya ishe mu ,balle ma inkin zo mama zata kara kara. Kayan sawa zan sai miki ko wanne ,inada kudi enough a account dina ,kullum baba samun yake bana kashesu . Zan iya kula da lafiyarki ,babban shine zan kula da farin cikin ki,kullum zan dunga saki daria ,har funny faces zan dunga miki in kina so .
Zan so ki sosai my farida ,ki rayu a dakina ,gado na,wardrop dina,toilet dina ,komai na baki . Ni zan rayu a jikin kj” yana magana yana lumshe ido.
Murmushi tayi ,kinya tasa ta sunkuyar da kai.
Ya kira sunanta yana mata murmushi,wannan tunanin da halayyar tasa yake kara haukata zuciyarta cikin soyayyarsa, itama murmshin take masa,ganun yana matsowa gareta yasa ta fara ja da baya ,tayi hanyar fita tana kallonsa,bataki tai ta kallon sa a haka ba. Sai dai ya zama dole tayi gidan dan an fara kiran sallar magriba,za’a nemeta a gida in anji shuru bata dawo ba . Haka tana tsoro kar mama ta leko su .
Bata ankara ba kuwa taji tayi karo da abu,da sauri ta juyo tare da daga kai. Yaya SHAMSU ne yayan deeni ,ya kalleta .
Haba farida yi a hankali maba,bakya gani ne?”
“Yi hakuri yaya ai duk laifin deeni ne ” ya zaro ido ,sharri zakk mun ? Yaya laifinta ne” girgiza kai ya yi tare da murmushi ,ya ce “Deeni da Farida sai Allah ,ba’a gane muku kuma ba’a shiga tsakaninku . Ni kan nayi masallaci ,maza kaima kayi harama ,kema ki shige ciki ayi sallah,in yaso kuyi soyayyar daga baya ”
Kunya tasa ta rufe fuska ,ta fita da gudu ko sallama da mama batayi ba, deeni yabita da kallo yana murmushi ,sonta na bin jikinsa . Ya Shamsu ya kalleshi yace wai wani irin so kake wa farida ne ?
“Yaya nima ban sani ba ,ni kaina na rasa wane irin so nake mata da yawansa ”
Girgiza kai shamsu ya yi ya wuce ya barshi a wurin …
Cpied by sumy luv❤❤
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Wirtting by SA’ADATU WAZIRI
COPIED BY SUMAYYA SA’AD(sumy luv ❤)
05
Gidansu farida cike yake da mata da maza da kuma matan aure uku,farida ta kasance yar amarya Alh Ahmad,wato mahaifinta,kuma ita kadai ce a gurin mahaifiyarta . Haka hankalin Haj A’i yafi zuwa dana mahaifiyar farida ,dan haka shkuwarsu da zumuncinsu yafi karfi da mahaifiyar farida Haj bilki akan sauran mata Alh Ahmad din. Haka nan burinta farida ta zamo surikarta saboda salihar yarinyace ,zata zamo mace ta gari kuwa uwa ta gari. Don haka sun dade suna tsara yadda zasu hada auren deeni da farida.
Duk wani dan yasan deeni to da farida ya sanshi,haka duk wanda yasan farida da deeni yasanta ,sun zana identity na juna . Ahalin yanzu deeni nada shekara ashirin da daya yayin da farida take shekara sha bakwai,tana aji shida na secondry, su kuma yan katsina ne.
Farida na shirin jarrabawar gama secondry ,,shi kuma deeni ya na shirin jarrabawar shiga aji biyu na jami’a. Haka wannan lokacin zuciyoyinsu nada burin auren juna a wannan shekarar,sabida aladar gidansu farida be aurar dasu suna gana secondry sch ba cigaba se a gidan miji. Wannan ya karawa deeni karfin gwiwar yin karatu da naci domin mahaifinshi ya cika masa burinsa. Dabi’ar deeni na son karatu yasa shi cin karo da littafin MISBAH, wanda shahararren marubuci ne na harshen hausa dama turancin duka,,idan yayi littafi da turanci yakan fassarashi ta harshen hausa,wannan ya nuna cikakken bahaushe ne,,sai dai bayaga sunan sa da email din sa bawani abu da ya nuna shi din waye ko dan ina ne”” bawani tarihinsa ko wani abu game dashi,banda sunan labari da email address dinsa sai sunan sa,,ba information akansa sai na email address din sa dayake bayyane a zahiri,,amma kuma ya boye kansa.
Yawancin labaransa ya kunshi irkicin da samari da yammata suke suntar kansu a lokacin tasowarsu da irin matsalolin da suke fuskanta ,sai kuma abinda suka shafi shauki emotions dinsa ,yadda kwakwalwa ke ban bamta da zuciya,,da yadda suke tafia tare kwarai.
Akwai ilimantarqa sosai a littatafansa ,daga rubutunsa zaka fahimci mutun ne me ilimi da sani,,da kuma bincike akan abinda yake rubutawa ,haka nan zaka san tubutu passion dinsa ne,wani abu ne dayake so kuma yake jin dadin rubutawa,hakan ya zama tamkar wani bangare na rayuwarsa,yana nuna hikima sosai a rubutunsa ,,ga bincike ta fuskar addini da boko, ga sanya irin matsalolin da mutane ke fuskanta . Hakan yakansa mutun yaki tamkar dashi yake,ko ya taba wata matsalarsa.
Wannan yasa deeni yake ba karatunsa muhimmanci fiye da na sauran marubuta.
Abinda yakara jan hankalin wannan karan shine yadda marubucin yake fada wasu halayyar da kwatance tamkar irin nasa,marubucin na rubutu tamkar ya sanshi,da tunani irin nasa,da hobbies dinsa, da kalar soyayyarsa,irin yadda yakeson rayuwarsa ta fati,,da irin matsalolin da yake fuskanta a halin yanzu ,,da irin rayuwar auren da yakeso yayi da farida………wannan kenan