MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

“”Please my dear” ka tashi mna,kana da baki ”
Bai saurareta ba sai kokarin jawota jikinsa da yayi yana narke mata a jiki,ya cigaba da kwanciyarsa a jikin ta,yana jin sonta na karawa baccin nasa dadi.
Girgiza kai tayi tana murmushita kwace jikinta tare da sa hannu tana jan hancinsa,tana wasa da shi .
My dear please ka tashi ka duba time fa karfe sha daya na safe ,baccin ya isa haka. Ba don ruwan sama ba da fa ka fita tun karfe takwas.”
Cikin muryar bacci ya ce,”shiyasa nake son damuna ,yana bani hutu ,ina samun nutsuwa da Bahijja na,amma ina!! Wannan likitar ba zata bar wannan likitan ya huta ba.
In barka ka huta daga baya kace me yasa ban tashe ka ba ? Ka fa tuna me kace mun ”
,” Komai bacci me dadi da nake ki tashe ni ko da kamshin jikinki”
Rungumota ya sake yi ya cigaba da kwanciyar shi”
Bata kulashi ba ta mike ta nufi gadon Muhammad da taji alamar ya tashi yana ta ciccilla kafa yana wasa tare da surutai irin na yara. Yana ganinta kuwa ya wangale baki yana mata daria,yana sanye da body suit dinsa masu kyan gaske da ban sha’awa .(hmm, kaga dan likitoci ,????)kaunar dan nata taji ya kara shiga zuciyarta ,dariyar da yake mata ya sa taji kaunar danta har cikin zuciyarta tare da godewa Allah da ya azurta ta da kyakkyawa kuma lafiyayyen da son kowa.( dama ahalin likita na cuta ne ????????ciwon ma tsoran gidan likita yake)
Tasa hannu ta daga shi,yaro ne da bai wuce wata shida ba ,ta rungumo shi a jikin ta ,ta ce.
Ni dai na kasa tashin Abbanka ,amma ni da kai zamu tashe shi tare.
Nan taje ta ajiye shi a kansa,nan da nan ya wangale baki har da tsalle saboda ya ga abokin wasansa. Nan ya hau sukuwa a kansa yana jansa tare da masa yaren su na yara ,dolensa ya bude ido yace.
” Ta nan mommyn ka ta bullo ko ? Ta hada ni dambe da kai,to bari in mike muyi.
Nana ya tashi ya biyeshi suna wasa yana cilla shi sama ,shi kuwa yana ta dariya,itama ta taya su. Sannan ta barsu ta nufi toilet don shirya masa bayi ,ya yi wanka . Tazo ta barki Muhammad ta kai shi gurin baba Andi,dattijuwa me kula da shi in bata nan. Sannan ta dawo ta taimaka masa ya yi wanka,ya shirya kusan komai ita ta masa,hatta turare ita ta fesa masa ,gyaran fuska da komai ,sannan ta kalleshi ta ce .
Perfect!!! Mijina is d best” Ya jawota jikinsa yace,”A’a mama ta is d best ,,ina sonki Bahijja na,ina son ki sosan gaske ,musamman in kina sakaltani ,ina jina kamar dab baby. Zan iya yin tiyata inyi allura in bada magani in duba mara lafia,amma ba zan iya kula da kaina ba,ko daurawa kaina tied bazan ita ba balle shafar mai ko sa kaya. Ko siyen sutura nawa ban iyawa saboda Bahijja na ta bata ni,ban iya komai nawa.
Allah ya bar mun ke Bahijja na,Allah ya miki albakrka ,Allah ya hadani da ke har a gidan aljannah”
” Ameen my dear””
Ta fada a lokacin da take kokari. Kwanciya a jikinshi,idon ta a lumshe ,ta ce.
Wa zan sakalta in bata in ba mijina ba ? Kai ne first baby na,babyna na farko kafin Muhammad,kaine zuciyata, kaine rayuwata,kaine mutumin da bazan taba gajiya da masa hidima ba har iya karshen tmrayuwata. You are my world nd my happiness duk wani abu a duniya bayan Addini na to komai ya biyo bayan kai da Muhammad ,bani da kamar ku.
Aure na da rayuwarsa gaba daya na daukeshi ibada ne,sai nayi dace da samun soyayya da kwanciyar hankali da duk wani abu da mace zata bukata a rayuwa . Na gide Mislihu ,Allah ya saka ma da gidan Aljanna. Duk wani abu da nake maka ban yi rabin wanda kake min ba .”
Yayi murmushi ,A duk lokacin da na kalle ki da Muhammad da kuma asibitina,yadda kike taimako na ,kika fahimce ni,yadda kika yi spporting dina sai naji tamkar Allah ya biya mun dukkan wani bukata ta na rayuwa,sai fatan Allah ya hadani da ke har a Aljannah. Ina alfahari da ke Bahijja.”
Tayi murmushi ,Nima ina alfahari da kai Mislihu..”
Nan ta ja shi zuwa dining area kamar kullum kamar yadda suka saba,ta tabbatar ya ci ya sha abinda ya kamata ,sannan ta raka shi har kofar ya fita wurin bakin sa. Sun rabu cikin soyayya da kaunar juna kamar yadda suka saba.
Dr Mislihu ya samu bakinsa a falo Alh. Umar ne da amininsa Alh. Tahir suka zo da maganr Deeni . Nan ya nemi jin abinda ke damun sa ? Me ya faru dashi ? Dan yana son ganin medical report dinsa wanda ya tabbatar musu da sai in yaji case din irin wanda suke maganin matsalar sa ne ,to zai karbe shi.
Alh. Tahir ya masa bayanin komai sannan suka yi alkawarin kawo miahi medical report dinsa washegari. Da wannan suka rabu akan za su hadu washe gari a cikin asibiti……… .
To nan muka kawo karshen wannan kashi…..
Sai kuma ku tara a nan gaba ,wanda zamuci gaba ranar monday in Allah ya kaimu..domin gobe sunday ranar hutu nace ????????????
Nagode ,taku har kullum,,,
????????????????????????MISBAH????????????????????????
writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
=================== GIDAN NOVELS ====================================
30
Bahijja mace ce abarbso ga kowa balle mijinta. Macece da tasan hakkin mutane da basu hakkin su, tare da tsananin kulawa da nuna damuwa ga mijinta. Tasan yadda zata kula da kanta da kuma mijinta da duk wanda yake tare da ita ko yake karkashinta, don haka ma’aikatan su ke matukar jin dadin aiki da ita.
Komai tsananin abu ta iya mai dashi mai sauki, mace ce mai so da kuma kokarin aika gudunmawarta ga alumma, a duk lokacin da ta samu wata yar dama komai kankantar ta tana amfani da ita don tura sakonta ga al’umma a
fili ko a boye, a zahiri ko a badini. A duk lokacin da taso tura sakon da bata so a santa ko a san ita ce, to takan yi amfani da sunan MISBAH, wato ta hada sunanta da na mijinta, farkon sunanta da farkon sunansa.
Shikansa Dr Muslihu bai jima da gane wacece MISBAH ba. Saboda bata fada masa ba, a fadinta tace ba tayi dan a santa ba, sai dan bukatarta ta biya, ta tura sakon da takeso turawa kuma ya isa. Wanda ladanta gun Allah takeso ba mutum ba.
Wannan halaiyar tata shike karawa mijinta sonta, yake gani kamar ba irinta a duniya. Bahijja baice ta hada komai ba dan ‘yar’adam take (She is not 100%) amma halayenta masu kyau da niyyarta sun maidata 100% da har ba’a kula da sauran illolin nata.
Bahijja (MISBAH), macecemai aiki da niyya, mace mai akida da ka’ida, mai yin abinda tace da abinda tayi niyya. Intai alkawari zata cika, in kuwa tayi magana gaskiya ce zata fito daga bakinta. Bayan aikint babu inda take samun matukar nishadi da jin dadi kamar ta tsinci kanta a gaban (computer) tana bincike ko ta fada duniyar rubutu, tana aika sakon zuciyart da iliminta da iya fahimtarta ga al’umma.
Tana kula da bangaren mata a asibitinsu, shi kuma bangaren maza. Suna kula da damuwar juna da farin cikin juna, suna bawa juna lokaci da kula, suna tsananin farin ciki a duniyarsu.
Lokacin da ta cika shekara goma da aure Allah ya azurtasu da haihuwar da namiji mai kama da Bahijja, yayin da ya biyo mahaifinsa ta hanyar halittarsa. Farin cikinsu ya karu, suka yiwa Allah godiya.
Bahijja ta rungumi danta da mijinta wanda suke sune duniyarta da farin cikinta gaba daya.
Bahijja ta sami dukkan abinda takeso, saidai ta inda tayi rashin sa’a ta bangaren dangin mijinta, wani lokaci uwar mijinta da ‘yan’uwansa zasu zo har gida su zageta suci mutuncinta gaban ma’aikatanta. Suna tunanin ta mallake Muslihu, gata tsintacciyar mage bata da asali. Ba irin cin mutuncin da basa mata, amma bata taba nunawa Muslihu ba balle ta fada masa, har ya gane da kansa, saidai bai nuna mata ba tunda ya lura bata so ya sani balle har ya nemi fad da ‘yan’uwansa akanta. Dan haka yai yadda takeso, bai musu maganar ba balle su sami rashin fahimta.