HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan son Bahijja yana mugun ganin girmanta da darajarta, wani lokacin yakan rasa mai zai mata dan ya nuna mata jin dadinsa da farin cikinsa da soyayyarsa gareta, kome yai mata sai yaga yayi kadan, dan haka yake ronkon Allah ya bata farin ciki da kwanciyar hankali duniya da lahira. Allah ya daukakaa,  ya daukaka darajarta a duniya da lahira,  Allah ya bata Aljanna.

A halin yanzu Bahijja na hutu tunda ta haihu ba ta koma aiki ba,saboda Mislihu ya hanata,ya ce sai ta huta nabtsawon shekara guda.

Bata musa ba tayi yadda yake so. Sai dai fa Bahijja Bahijja ce ,bata san zaman banza ba,don hka ta bawa jikinta hutu amma kwakwalwarta kullum tana cikn rubuce – rubuce ,daga na turanci har hausa,daga na addini har na zamani.

Wani lokaci (poem )take rubutawa daga na hausa har na turanci,wani lokaci kuma ta zauna tana koyon abinda bata iya ba matsayinta na mace,kamar girke girke ,iya kwalliya ,(dressing) da sauransu. Don Bahujja kam tana da mugun rauni a wurin, wani lokaci takan fi sati bata shafa ko (powder )a fuskarta ba ,balle jan baki da sauransu.a

Wani lokaci Mislihu ke zama yana mata kwalliyar,har gyaran gashi. Wani lokaci yakan tsokane ta,ya ce sai ya auro wacce ta iya kwalliya da gayu.

Ta kanyi murmushi tace,”Wa ya hana ka ? Ni duk abinda kake so ina maraba da shi.”

Yakan jawota jikinsa ya tallafi kanta,ya ce.

Ga abinda nake so, wannan halayyar,wannan (personality ) din ba kwalliyar fyska ba . Ina miki fata da addu’ar ki zauna a yadda kike kar ki taba canjawa. Ina son wannan Bahijja kullum kwanan duniya ina da da sonta.”

Takan rungume shi tace,”Ina sonka Mislihu na ,ka kasance dani har karshen rayuwata.”

Yakan amsa mata da,”Insha Allah .”

Asibitin su Bahijja Alh. Umar ya yanke hukuncin kawo Deeni,saboda yadda ya buncika yaga ingancin asibitin ,da tasirin da yayi sosai a cikin al’umma ,da kyakkyawan shaidar da suka samu.

Shi kanshi yadda ya ga tsarin asibitin da ayyukan su sai ya ji sun burge shi, har ma ya yiwa dansa Deeni sha’awar bude irinsa in Allah ya bashi lafiya.

 

Kamar yadda sukayi alkawari,washegari Alh. Umar ya kawo wa Doctor Mislihu (report)din Deeni na duk wani asibiti da suka taba zuwa,daga gida Nigeria har na waje. A nan Doctor Mislihu ya bashi kwana uku cewa zai neme shi bayan ya karanta (report) dinsa.

Tunda ya karbi ( report din bai samu zama ya karanta ba ,saboda ayyuka da suka masa yawa,kuma gashi kwana ukun da ya basu saura kwana daya,don haka ya yanke hukuncin dawo da su gida ta duba ,duk da baya hada lokacin iyalin da na kowa don haka baya dauko aiki ya kawo shi gida,haka itama Misbah. Wannan dama ka’ida ne a gida basu da lokacin komai sai na kansu,sai dai ko in baya gida ita takan yi wasu ayyukan ,in ta gama da ayyukan gida . Lokaci na farko kenn da Doctor Mislihu ya taho da aiki gida……..

Pls ayi mun hakuri na rashin posting din jiya ,,,wlh gaba daya service dina ne ya dauke ……Nsha Allah yau sai kun gaji da karatu

Sumy luv ????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting by SAADATU WAZIRI GOMBE.

Copied by SUMAYYA SAAD❤❤

31

Ya dawo gida a gajiye ,Misbah tayi masa abinda ya kamata,suka yi hirarsu irinta ma’aurata masu matukar son juna.

Can ta jiyo Muhammad yanata rigima a gurin baba Andi,hakan yasa ta fice wurinsu,lokacin Doctor Mislihu ya samu damar dauko (report ) din Deeni yana karantawa yana bin (history) na ciwon nasa da matsalar sa.

Ya yi nisa sosai wanda har Bahijja ta shigo kusan sau ukku amma baiji shiguwarya ba,ita kanta tayi mamaki,abinda bai taba yi ba. Yawanci ma in yana da aiki yakan je (office ) dinsa ya zauna koman dare,amma baya dawowa da shi.

Shigowar da ta sake yi na hudu ne ta samu bacci ya kwashe shi da takardun a gabansa. Murmushi tayi ganin yadda ya karya wuya kamar wani karamin yaro yana bacci.

Bayan ta kwantar da Muhammad a gadonsa ta zo ta gyara masa kwanciya tare da lullube shi,nan kuwa ta ga ya kara gyra kwanciya ya jawota jikinsa yana fadin,,,”Na gode Bahijja,Allah ya miki albarka.

Murmushi tayi ta kara manna shi a jikinta yadda zai ji dadin baccin ,har itama baccin ya fara daukarya. Nan ta farka ta zame jikina a hankali sannan ta tattara takarsun tare da canja kaya ta sa na bacci,har zata kwanta sai kuma wannan file din yaja hankalinta,wanne irin muhimmanci yake da shi haka yasa Doctor dawowa da shi gida ?

Nan ta bude ta fara bi a hankali tana karantawa ,kamar wasa gaske ta tsunduma cikin karatun ,tana kokarin fahimtar case dinsa.

Tuni taji zuciyarya ta karaya ,ta tausaya ,duk da ba ainihin tarihinsa taji ba amma (report ) dinsa ya nuna ya kamu daa ciwon (emotional disorder)tabbas yana bukatar taimako,yana bukatar (couseling )musamman ta fuskar Addini .sannan yana bukatar a nuna masa reality gaskiyar rayuwa ta canja masa,saboda tsawon shekarun da ya dauka a cikin wannan yanayi amma ba canjj,ya rayu cikin bakin ciki,bacin rai. Wanda wannan ba karamin ciwo bane kwarai.

Ta so tasa kanta cikin (case) din don jin me ya jawo masa wannan (emotional pains ) din ? Amma tayi shiru ta yarda da mijinta fiye da kowanne likita,fiye da ita kanta ,ta tabbatar zai taimaka masa . Nan ta tattara ta rufe ta ajiye file din gefe guda,yayin da ta kwanta da tunanin abin a ranta.

Washe gari da safe bai fada mata ba,ita kuma bata tambayeshi ba,ta tabbatar in yana bukatar taimakobta zai fada mata.

Kamar yadda suka yi alkawari a washegari  ya nemi su ,wanda yayi dai dai da kwanakin da ya basu,anan doctor ya basu form su cike ,sannan wata takarda wadda take cike da sharudan asibitin kafin su karbi mutum,da kuma in sun karbe shi. Idan sun amince da sharudan su to su sa hannu su kawo shi,in kuma basu amince ba to kar ma su dawo.

Tun a wurin Alh. Umar ya karanta duk da halayyar da Doctor Mislihub ya nuna musu ya yi kama da gadara,amma ba yadda ya iya sai ya bi dokar don ya lura ba maganar alfarma wa kowa a bisa dokar su da akidarsu. Bashi da zabi saboda yanada bukatar taimakonsu,ya yarda da sahihancin su da gaskiyar su,hka akwai tsaro na sosai .dole ya amince da dokar su.

Doka mafi tsauri a cikin dokokinsu shi ne ba a dauke mara lafiya har sai in. Su suka sallame shi bayan ya warke,haka nn basu da wani sauran iko ko isa akan mara lafia da suka kawo,basu da ikon wani yanke hukunci akansa.

Alh. Umar ya so yaja baya ,sai dai a lokacin da ya rufe ido ya tuno halin da Deeni yake ,sai yaji hankalinsa ya tashi,tsananin tausayinsa ya ratsa shi,soyayyar dansa da tausayinsa yasa shi zub da hawaye tare da dora laifin halin da dansa ya shiga akansa. Haka nan zuciyar ya amince da wannan asibitin, yana da tsammanin Deeni zai samu lafiya a wurin. Don haka wannan ya bashi karfin gwiwar sa hannu,ya yi cike – ciken da duk ya kamata tare da karbar (sliip) don biyan kudin jinyar Deeni. Sun rabu akan washegari zasu kawo shi…

Sumy luv????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting by SAADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SAAD❤❤

32

 

A hankali ya turo kofar dakin nasa tankar mai jin tsoron kofar,zuciyarsa na tsinkewa saboda tunanin wane hali zai samu dan nasa ? Tsawon sati guda kenn bai leka shi ba,saboda gudun wani hali zai same shi.

Kamar kullum ya same shi makure a lungu guda tamkar mai jin tsoron kar azo a kama shi,fuskar sa daure tamau ba alamar fara’a tare dashi. In bai manta ba kayan da ya barshi da shi wancan satin har yanzu sune a jikinsa. Tuni idanunsa suka kada suka yi jawur.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button