HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Deeni da na sani da tsafta da son gayu komai fes-fes ba ma jikinsa ba,dakinsa ,kayansa komai fes-fes suke,kuma cikin tsari. Amma yau rayuwa ce ta mai da Deeni haka kuma ni ne sanadi””.

Ya yi haske amma ya fada,yayi wata irin rama mara kyau ,hasken da ya yima albarkacin zama wuri daya da take yi ne,da kuma yanayi irin na lagos. Tunda suka zo garin ko kofar gida bai fita ba ,yana nan a dakinsa da aka ware masa.

Mama bata fasa masa addu’a ba da nema masa sauki, da mafita a wurin ubangiji.

Deeni “” mahaifin nasa ya kira sunansa.

Juyowa ya yi suka yi ido biyu,tuni kuwa ya kara daure fuska tamau,idanunsa suka juye alamar bacin rai ya bayyana karara a fuskar sa ,ya yi saurin dauke kai.

Mahaifin nasa ya fahimci har yanzun yana cikin fushi dashi ,ya matso dashi.

Kayi hakuri Deeni,na maka laifi ,zan yi iya dukkan kokarina inga na  gyara kuskuren da nayi,Deeni kar ka hukuntani ta hanyar tsanantawa kanka da bata rayuwarka a banza,Deeni wanne farin ciki ka tsinta a irin wannan ratuwar da kake ?

Deeni nasan ba zaka so ba kuma ba zaka yarda ba,dai dai zan fada maka ina son kaika inda raguwarka zata dai daita,wanda bayan nan na maka alkawarin ba zan sake maka shisshigi a rayuwarka ba,zan baka dama kayi rayuwar ka yadda kake so kuma yadda kaga dama. Ina so ka shirya mu tafi don Allah…””

Jin kalamansa  da yayi na karshe ne ya juyo ya kalle shi,ya ce.

” Kai mahaifina ne ,ba sai ka rokeni ba zan maka biyayya . Ina kake so inje ? Zan je zan je amma karka taba zaton wai don kaina ne sai don kanka,kamar yadda ka dauko mana tun farko ka sabar mana ,bamu da zabi sai naka,to yanzu ma haka ne. Saboda ni kan yanzu a rayuwa ba abinda ya saura zaka min ,baka da abinda zaka iya sake min ko bani ya sani farin ciki,ba abinda zaka min ya goge min bakin cikin da bacin ran da ke cikin kwakwalwats da zuciyata .

Wanann abinda kuka hadu kuka mun va zai taba barina naji wani dadi ba a ratuwata ba,ba yadda za’ayi in samu wani farin ciki ko kankani bayan cin amana da rashin kauna da kuntata mini da yaudarar da iyayena da dan uwana da wacce… ………

Maganar ta sarke ,numfashinsa ya dinga fita sama sama,vai ankara ba sai ganinsa yayi ya fadi ya suma . Cikin tashin hankali da damuwa sukayi asibiti da shi,asibitin da bai shiga yana cikun hankalinsa ba sai a sume.

Dokar farko ta fara aiki akan su,wato su ajiye shi su tafi su barshi ,kuma ba zasu sake waiwayar sa ba sai bayan wata shida wanda in ya samu wannan wata shidan zasu iya zuwa bayan wata daddaya.

Haka haji. A’i da Alh. Umar suka tafi suka bar dansu cikin mawuyacin hali da ciwk ,mama tayi kuka har ta gode Allah ,yayin da Alh. Umar bai yi ba,sai dai abinda yake ji a zuciyar sa yafi kuka ciwo.

Doctor Mislihu ne tsaye kan Deeni tare da sauran likitoci da ke aiki a karkashinsa,da sauran ma’aikatan asibitin suna iya dukkan kokarinsu don ganin ya farfado.sai dai fa abin ya ci tura,va irin dabarar da basuyi ba hakan yasa ya nemi taimakon gaggawa dafa sauran ‘yan uwansa wadanda suke manyansa ne ta hanyar wayar sadarwa.

Tabbas duk kokarin ka da kwarewar ka wataran sai aikinka ya kunyata ka,kwarewa da dai dai sai Allah,Dr. Mislihu bai kasa va kuma bai yi kasa a gwiwa ba ya ci gaba da ba da himmar sa da kokarin sa,bai ji dar ko tsoro ba,sai dai abin ya matukar daure masa kai,saboda shi yasan ya sha fuskantar masu ciwo irin na Deeni.

Da taimakon Allah yana addu’a tare da yakini a zuciyar sa ya samu deeni ya farfado da wani bakon yanayi,yana cikin tsananin ciwo da rudani,idanunsa sunyi jawur ,hawaye kawai ke zubaa ba kakkautawa,haka nan ya rike kansa gam alamar yana jin azabar ciwo,abin har ya kaishi ga yana doka kansa jikin karfen gadon da yake kwance.

An masa allurar da ya kamata ayi masa ya samu nutsuwa kadan,da kyar suma samu bacci ya dauke shi. Baccin da yakamata yayi na wuni guda kafin ya farka,amma awa biyu zuwa uku kawai allurar take masa aiki ,haka magani ba ya aiki a jikinsa.

A wannan dare Doctor Mislihu ya koma a gajiye tare da wannan damuwar a tare da shi. Bahijja na ganin sa tasan ba lafiya ba,ta riga da tasan yanayin aikin nasu ,akwai gajiyarwa ,sabida jikinka da kwakwalwarka da zuciyar ka duk sai sun jigata,sun wahala.

Ta shirya masa ruwa yayi wanka,bayan ya fito tayi kokarin sauke masa gaijyar sa da (tension ) dinsa ta hanyar masa matsa a gabban jikinsa da kansa,tana (massaging )cikin nutsuwa yadda zaiji dadinsa,kuma ya yi masa aiki.

Yaji dadin hakan kwarai,ya jawo hannu ta.

Na gode Bahijja ,naji dadi sosai, naji dadin wannan abinda kike min don ya bani nutsuwa tare da sauke min wani (tension)din . Tayi murmushi tare da shafa shi,ta ce .” Burina kenan inga na rage maka damuwa,naga yau kana cikin zafi ,bari in kawo maka abincinka daki.

Nan ta fita ta dawo hannunta dauke da babban (tray ) ta shirya masa duk wani abinda zai bukata. (Coffe) mai zafi ta fara bashi sannan ta zuba masa abincin wanda kadan ya ci shima don ta matsa masa ne,kafin ma ta ce wani abu aka masa waya ya nufi asibitin a rude..

Wannan al’amarin ya daurewa Bahijja kai,”” To shin meke faruwa ne ?

Nan ta buga waya asibitin don jin meke faruwa? A nan aka bata labarin sabon mara lafiya da aka kawo wanda ya ta da hankalin oga.

Haka ta dunga kawai da kawowa har ya dawo ,ta tare shi da tambayoyi amma bai amsa mata ba ya nuna ta kyale shi akwai binciken da zai yi ,in ya gama zai sanar da ita.

Wannan abu ya daure mata kai ,sam bata jin dadin ganinsa haka. Ya dawo kullum yana cikin karatu da bincike saboda matsalar Deeni ta zame masa sabo,ya zama kamar (challenge) ne a tare dashi..

Abokinsa Doctor yasir ya nemo wanda suka yi karatu tare ,kuma sunyi aiki tare a dashi lokacin da suke ( teaching hospital) wanda shi bayan bude asibitin su ne suka rabu. Sai dai dama lokaci lokaci sukan hada kai suyi karatu.

Dr. Yasir kamar aboki ne a gare shi,kuma abokin aikinsa,don haka ya roki alfarmar ya zo su binciki case din deeni tare.

Da farko ya so yasa Bahijja ciki,sai dai baya sob wahalar da ita,sannan tana cikin hutu ne,gara ta zauna ta bawa muhammad kyakkaywar kulawar da yake bukata. Kuna yasan Bahijja sarai da daukan zafi,tana iya watsar da komai ta tsunduma kanta ciki,don haka ya yanke shawarar ya yi aikinsa da kansa.

Wata guda suna bawa Deeni(treatment) amma ba wani cigaba ,babbar damuwar sa yana cikin ciwo balle har a samu nutsuwar da za a sai ta hankalinsa da tunaninsa,balle har a san matsayin da kwakwalwarsa da zuciyarsa suke ciki. wannan abu ya mummunan daga hankalin Doctor Mislihu da sa shi cikin damuwa,duk maganin da ya bashi baya aiki dai dai a jikinsa yadda ya kamata yayi.

Gaba daya y rasa nutuwa da kwanciyar hankali,kullum bashi nan bashi can neman yadda za a samu waraka ,haka ya dauki (case)din deeni da zafi tamkar na wani dan uwansa na jini,ya ci alwashin sai inda karfinsa ya kare.

Ya dawo ba ya bawa kowanne mara lafiya kulawa kamar yadda yake bawa Deeni,tausayin sa da kaunar sa ya shiga ransa,musamman in yaga yadda wataran Deeni ke zura masa ido yana kallon sa tamtar mai kokarin fada masa wani abu,tamkar yana ce masa ka “”ka taimake ni,”” tamkar dukkan tsammaninsa na kansa. Haka wani lokaci hawaye zai yi ta zuba masa,lokaci guda kuma ya kuma rikecewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button