MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abin na Deeni gaba-gaba yake,don haka Doctor yasir ya bashi wata shawara akan abinda zasu masa,amma fa sam ya ki yarda ,yaki amincewa ,saboda yana ga akwai garaje ciki,sannan ciwon Deeni bai kao har hakan ba. Amma a hankali Doctor yasir ya dinga nuna masa dukkan wani (treatment) da zasu mada sun masa,amma baya (respondng) wannan shi ne option da ya rage dashi.
Ya tuna ya yiwa kansa alkawarin yin duk abinda zai yi don ya taimaki shi ,haka iyayen yaron na da dukkan wani tsammaninsu akan shi. Da kyar Dr. Yasir ya shawo kansa ya amince………..
Barkanku da rana jama’a
Sai ayi wa deeni addu’a za’a yi masa theatre Allah yasa a dace ????????
Sumy luv????????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by. SUMAYYA SA’AD❤❤
33
Nan ya hau shirye-shirye ,yasa lokaci da rana,ya gama amimcews kansa amma duk da hakan sai yaji zuciyarsa na fada masa ya nemi shawarar matarsa,ya sanar da ita,ko ba komai rana da ilimi akan cuwon Deeni sosai kamar yadda yake da shi. Da wannan tunanin ya dauki waya ya bugawa Bahijja.
“Bahijja”
“Yes my dear,kana hanya ne na jira ka shuru,hope dai lafia.”
Ya yi mata murmushi tamkar tana kallinsa,ya ce
“Lafiya Bahijja ,wani aiki ne yasha kaina da na gama zan taho. Dama ra’ayinki nake son ji akan wani abu da zan yiwa patient dina.”
Tayi masa daria tace ,”Zan yi farin ciki da baka shawara mai kyau ,na lura kana cikin damuwa akan wannan mara lafiyar ,kar ka damu nasan ko me zaka yi ( you re the best on it).
Yace,”Duk da haka dai ina neman kwarin gwiwar a wurin ki.”
Ta ce,”To ina jinka,mene ne matsalar ka?
A hankali ya labarta mata case din Deeni da yadda yayi ta fama da shi.
Ta dan yi dogon shuru tana tunanin ai indai wanda ta karanta file dinsa ne case dinsa ba haka bane,abinda reporrt dinsa ya ce daban abinds kuma Doctor ya fada mata yanzu da irin treatment din da suke masa daban .
“Bahijja ”
Muryarsa ta katse mata tunani.
Kina jina kuwa?
” Eh ina ji”
Ta fada cikin muryar damuwa,sannan ta ce.
To yanzu wane shawara ka yanke? Me kake ganin zaka masa?
“Shawarar da muka yanke yanzu ni da Doctor Yasir shine,zamu masa (E.C.T)
“”WHAT!!!!!!!!
Ta fada da karfi cikin zare ido tamkar yana ganinta,hankalinta ya tashi.
Ta ce please Doctor kar kuyi masa,kasan dangers na wannan therapy din”
“Bai kai stage din da za a masa haka ba.
” Da hankalinka,da tunaninka?
“Me kike nufi? Kina so kice bani da hankali ko ban san me nake yi ba ? Laifina ne ba naki ba da na fada miki ,dama na lura komai ke kina son nuna kin fi kowa sani.”
Tayi kasa da murya ,Kayi hakuri my dear ba haka nake nufi ba,nasan kai fini ,kasan komai ,amma ina so ka fahimci danger din dake cikinsa ne,kar muyi wasa ko garaje da rayuwar wasu. Ka tuna amana da yarda yasa iyaye da ‘yan uwa ke kawo mana marasa lafiya,kasan yadda (electro convulsive therapy )yake,idan ya yi (seizing ) kwakwalwar sa gaba daya fa?
A tunanina baya bukatar wannan,ina gain (right medication) da (couseling ) ya ishe shi ya dawo dai dai ,wato maganin da ya dace.
Maganganunta yasa shi kasala ,ya ce.
Na bugo ne ki bani kwarin gwiwa ba kisa na karaya ba,ni kike yiwa maganar (right medication)?Don baki ganshi a gabanki bane da irin kokarin da nayi akansa da ba zaki fara fada min haka ba. ”
Doctor duty na ne in tsaida ka,please na rokeka kar kayi,ka sake tunani.
Kashe wayar yayi ya kyaleta cikin rudani tana ta buga wayar tana ihun kar yayi amma bai dauki wayar ba ma. Hankalinta ya matukar tashi,ba shiri ta dauki hijab ta nufi cikin asibitin da sauri.
Sai dai kafin ta zo Doctor yasir yayi nasara akansa na cewa.
Kasan halin mata da tsoro ,da gajeriyar kwakwalwa .”
Ya amince amma maganar Bahijja da dalilan da ta bashi na yawo akansa,don kuwa yasan matarsa Bahijja bata cikin mata masu tsoto ko gajeriyar kwakwalwa amma da yake ya riga da ya yanke hukuncin sai ya yi din . Don haka kafin Bahijja ma ta iso dun riga da sun yiwa Deeni abinda suka yi niyya.
Yana kwance a wurin kamar gawa,dukkan gabobin jikinsa sun amsa,duk jikinsa ya sassake ,bawan Allah shi kadai yasan wahalar da yasha. Gashi jikin Deeni jiki ne da bai saba da wahala ba,bai ma santa ba gaba daya don haka abin ya fi wahalar dashi fiye da yadda ya kamata. Tuni ya manta kansa da duniyar da yake ciki.
A lokacin da Doctor Bahijja ta shigo zama tayi ta kama kai tana kuka .
Doctor me yasa kayi haka ? WHY!!!!!!
Tuni ya harzuka ,”Me kike nufi da (why)? Ban san me nake yi bane ? Me kike so kiyi (proving) da kika shigo kina min tsawa gaban abokan aikina da ma’aikatana ? Me kike ji da shi ? Wa ya baki izinin fitowa ki zo ?
” Doctor (please ).”
Ta fada cikin kwantar da kai .
( This is not you)wannan ba kai bane,ba haka na sanka ba ,kai mutum ne me taka tsan tsan da rayuwan alumma. Wannan ciwon nasa da ya zamo maka sabo ba firgita ka ya kamata yayi ba,ko kuma wani abin cews sai naga ya warke ko ta halin kaka kar a ce na gaza .
Ka tuna asalin purpose dinmu shi ne mu taimaki mutane ba mu wahalar da su ba ,ba muyi wasa da rayukansu ba. Yaushe tunaninka ya kauce,ya canja ? Yau ina cikin bakin ciki da na kasa tsai da ka,na kasa hana ka yin abinda ba dai dai ba,sai addu’ar Allah ya tashi kafadar wannan bawan Allah.
Bai kulata ba sai sa kai da yayi ya fita cikin bacin rai,yayin da sauran suka rufa masa baya………….
Shin wai wani irin aiki doctor mislihu yayiwa deeni ,,wanda har ya sa shi hatsaniya da matarshi… ????????
Sumy luv????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤
Bismillahirrahmanurrahim
RABBANAGFIRLI WAL-WALIDAYYA WALIL MU’UMININA YAUMA YAKUMUL HISAB…………AMEEN YA ALLAH.????????Allah yasa mu dace duniya da laira..
34
Ta mai da hankalinta kan Deeni ,taje tayi dukkan iya kokarinta domin ta samu ya dawo hayyacinsa,ya farfado kafin ya yi nisa. Sai data dauki tsawon awa uku akansa kafin ta samu ya bude ido sannan ya sake rufewa,numfashinsa ya daidaita. Sannan ta dan samu kwanciyar hankali da nutsuwa kadan,ta koma gida hankalinta a tashe ,tayi ta fama da Doctor Mislihu .
Fada yake mata ta inda ya shiga bata nan yake fita ba,ta lura yana cikin tsoro da tashin hankali ,sai dai yana kaucewa hakan da fada.
Bata ce masa kala ba sai rungumar sa da tayi sosai a jikinta,ta riga da ta fahimci (fears) dinsa da tashin hankalin daya shiga.
Kwantar da hankalinka ,insha Allah komai zai dai dai ta ,baa abinda zai faru (he will be fine) . Kuskure be kowa yana yi a rayuwa ,sai dai muyi kokarin kare faruwar haka a gaba. Bamu da damar yin wasa da rayuwa wasu.
“Bahijja ban san me ke faruwa ba,na kasa gane komai. Nasan cewa duk wani (treatment) da nake masa dai dai ne ,sai dai ban san me yasa ba ya (responding) ba,kuma ban yi niyyar wasa da rayuwar sa ba har zuci,ina son taikamakon sa ne. Ina ganun wahalar da yake sha,ina jinsa kamar dan uwana,sannan inason raikamakon mahaifinsa shi yasa duk abinda zanyi ya kare na dauki wannan (option )din. Ban yi tunanun komai ba ,sai dai nasan wanann a cikin (shock treatment ) wannan (is the most safest and effective).
Na sani my dear ,amma wannan ciwon sa(disorder) din da yake da shi ba na wannan treatment din ba ne. A ganina kun yiwa abin gaggawa ,kuma naga kamar baku yi shi dai dai ba,dole akwai wani kuskure a wani wurin ( something wrong somewhere ). Wa ya baka wannan ( idear ).?