HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

” Doctor yasir ;;” ya fada kai tsaye .

Ta dafe kai cikin takaici ,ta ce. Haba doctor !!

” Har yaushe ka fara amfani da basirar wasu maimakon taka?

Kin san mutumin nan likita ne dan uwana ,meye a ciki in munyi (studying case ) na mara lafiya,munyi (sharing idea)?

” Baa laifi bane,amma abin akwai daure kai”

A wanann dare daga Dr. Mislihu har dr. Bahijja ba wanda ya runtsa ,suna tunani tare da juya al’amarin a cikin ransu wanda Dr. Muslihu ya kasa jurewa gari ya waye,a daren ya fita domin zuwa ya sake ganin Deeni.

Ga mamakin sa yana kofar shiga dakin yaji muryar Doctor yasir da wasu ma’aikatansa guda hudu wanda amintattun ma’aikaransa ne,yaji dr. Yasir yana raba musu kudi na aikin da suka masa. Ba farko sunyi ta canja duk wani magani da allurai da ya ce su kawo a dinga bawa Deeni. Wanda wannan yasa jikin Deeni ya kara rikicewa maimakon samun sauki. Saboda yana so ya batawa dr. Misilhu suna don ya jima yana jin haushin cigaban da ya samu ya barshi. Abu na biyu shi ya so Alh. Umar ya damkawa Deeni a asibitin su saboda ya ci kudinsa sosai ,amma sai Alh. Umar ya ci mutuncinsa ya ki. Tun daga lokacin ya dau lwashin sai ya dau fansa,kuma ya batawa doctor mislihu suna. Don haka ya bawa ma’aikatansa cin hanci.

 

Da farko kun ki,amma ganin yawan kudin da ya saye imaninsu suka manta amana da yarda dake tsakaninsu da mai asibitin. Ya ce kuma in aiki ya yi zai kara musu .

Lokacin da Dr. Mislihu ya gama jin abinda suke fadi ya ciro wayar sa ya kira (police) sannan ya kira Bahijja yana fada mata.

“Doctor yasir ya ci amanata ,Bahijja gaskiyarki ne,akwai abinda ua faru wanda ban fahimata ba sai yanzu”.

Yana cikin magana da ita ya jiyo motsin su zasu tafi,ya yi saitin banki kofar ,bai bata lokaci ba ya cakuno wuyan rigarsa tare da shakar masa wuya yana zaginsa.

“Yau sai na kashe ka ,maci amana. Ku kuma sai nasa an kulle ku,kun ci amanar yarda,kunyi wasa da rayuwar wani sabida abin duniya.”

Ganin yadda ya haukace musu Dr. Yasir ya ce.

Yaa zama dole muyi maganinsa kafin ya fallasa mu”

Tuni suka hadu akansa,hayaniyar su ya ta da Deeni ,ya yin da yakr ganunsu hazo-hazo ,duk da baya magana da Dr.mislihu ya saba da shi da dawainiyar da yake masa. Sannan da ikon Allah da taimakon da misbah tayi masa ya masa amfani ,ya dawo hayyacinsa.

Gani yadda suka toshe bakin dr. Mislihu suna dukansa tare da kokarin toshe masa hanci yasa ya mike ya nufi inda wani bell yake wanda alama ne na danger in an danna,ya yi sauri domin dannawa ,anan daya ya hango shi,ya yi kansa suna ta kokawa,yayin da dr. Yasir ya dauko wani almakashi ya soma cakawa Dr. Mislihu tuni jini ta wanke wurin . Yana kokarin guduwa ya ceci kansa ko ta halin kaka,yasan in Dr .mislihu ya kubuta to asirinsu zai tonu.

Deeni bai san yaushe ya bude baki a firgice yana ihu bmtare da neman taimako ba,yana fadin .

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!!!!

Nan sukayo saurin toshe masa baki da hanci har sukaga ya dai na nunfashi. Za su fita kenan sai ga ‘yan sanda sun iso,kafin su gudu kuwa aka cafke su,yayin da akayi kokarin daukan doctor mislihu zuwa emergency tare da deeni……

Lokacin Bahijja ta iso a rude tamkar mahaukaciya ,ganin mislihu cikin jini ya bala’in firgita ta da razanata. Tashin hankali ne wanda bata taba fuskantar irinsa ba,duk kuwa karfin hali da karfib zuciya irin nata a wannan rana sai da ta karaya ,hankalinta ya nemi barin jikinta.

Tayi kan dr. Mislihu jikinta na bari,ta rasa ma me zata mishi? Ta rude sai kiran sunansa take tana salati.

Tare akayi wani asibiti da su da wasu yan sanda dob basu taimakon gaggawa ,likitoci sunyi kokarin tsai da jinin dake zuba a jikinsa wanda a wuyansa suka caka masa da gefen ciki amma jinin bai tsaya ba,haka aka dinga masa kari wani ni fita wani na shiga. Suna iya dukkan kokarinsu akanshi.

Bahijja dai alwala tayi ta zo ta fara sallah,daga karshe ta hau addu’a saboda ta rasa nutsuwar yin sallar.

Wani likita ne ya zo ya kirata mijinta ya ce yana son ganinta. Jiki a sanyaye ta isa dakin tana kuka kamar ranta zai fita,ya kalleta cikin galabaita da kyar ya iya bude baki.

Kar kiyi kuka Bahijja ,ko yanzu ko bayan raina ,kituna yanzu nauyin asibiti da sauran al’umma da ke cikinsa na kanki,ki tuna mafarkin mu ne da burin mu wannan asibitin. Sai dai ki kula kar abinda ya faru dani ya faru da ke,mutum yana nan yana rayur sa bai damu da wani ba ashe makiya suna nan sun sa masa ido suna neman yadda za su cutar da shi.

K tuna nauyin asibiti da Muhammad na kanki,sannan in bani da rabon haduwa da mama in ta zo kun hadu kice ta yafe mun “”

Bahijja dai kuka take kamar zata hallaka ,ga tsoro da fargabar rasa mijinta ,ga maganar sa mai kama da bankwana,ga azabar ciwon da ta ganshi a ciki.

” Dole ne in maka kuka my dear,dole kuma in yiwa kaina kuka . Mutanen nan sun cuce mu,sun rusa mana ‘yar karamar duniyar mu da muke farin ciki a cikinta ..”

” Sun cuci kansu dai Bahijja ,ki tuna kece me lallashin wasu da ( couseling ) dinsu in sun shiga hali makamancin wannan ,yau rana tazo da zaki yiwa kanki wanann tatan.

Bahijja kada ki karaya kima fi yadda na sanki da,kiyi addu’a Allah na tare da ke ,kada ki taba jin ke kadai ce a duniya. Ki tuna duniya taki ce da mutanen arzikin da suke cikinta ,duk wani Musulmi dan uwanki ne .

Abu na karshe Bahijja,wannan. Bawan Allah da ya shiga rudanin rashin lafia da karin ruda masa jiki da kwakwalwa da ya samu ta sanadina ,ina fata zaki taimaka masa ya warke da iyakar iyawarki . Ina fata zaki gyara kuskuren da nayi.”

Tayi karfin halin share hawayen da ke zuba mata tare da yi masa murmushi , tace,,

In sha Allah my dear zan taimaka masa har kaima ka samu lafiya mu taimaka masa tare,mu cigaba da kula da asibitin mu da Muhammad,a duniyarmu zamu sake ginata tare da kai insha Allah.”

Duk da yana cikin ciwo sai da yayi mata murmushi alamar gamsuwa da maganarta. Nan ta kwantar da kai a gefen pillown dake jike da jini,tana rike da hannunsa,ita kadai tasan irin radadin da zuciyarta ke mata ,tana masa addu’ar fatan samun sauki da lafiya.hawaye na gudu a idonta ba kakkautawa,tana tunanin duniyarta ta zo karshe a duk lokacin da ta rasa doctor Mislihu .

** Ya Allah nasan baka barin wani don wani,ya Allah ka bani karfin imani da karfin zuciyar daukan duk wani ikon ka da aiwatar akan mu”

Da irin wadannan addu’o’in a zuciyarta bacci ya debe ta bata sani ba …………….

Hmmmmmmm.

Sumy luv????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

Please kuyi hakuri na rashin jina jiya ,,bikn aminiyata ake shiyasa na mnta daku????????????

35

Da irin wadannan addu’o’in Bahijja a zuciyarta bacci ya debe ta bata sani ba,sai farkawa tayi taji hayaniya akanta. Sauran likitocin asibitin ne suke bata hakuri mijinta kam ta Allah ta kasance akansa,ya bar duniya.

Jin abin ta dinga yi ba zata,kamar mafarki. Wani jiri taji yana dibanta tana salati tana kallonsa tamkar mai bacci.

Wayyo duniya,duk wanda ya dauke ki da zafi tabbas yana cikin masu asara. Jiya tana yare da mijinta ,abokin rayuwarta,gatanta a duk duniya ,amma yau baya duniyar.

Hawaye na zuba ta ce,Allah ya jikanka Doctor ,Allah ya maka rahma,ya yafe maka kurakuranka,yasa ayyukanka na alkhairi su bika” .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button