MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bahijja tayi kuka tayi kuka har taji ba dadi. Kafin a yiwa Doctor wanka da sutura ‘yan uwansa suka iso daga kano ,mahaifiyarsa da danginta tare da dangin mahaifin sa tare dasu akai masa sutura aka kaishi gidansa na gaskiya,yayin da mahaifiyarsa ta yafe masa tare da binsa da addu’a.
Gidan Bahijja suka dawo aka yi ta karbar gaisuwa ,yayin da maganar rasuwar ta baza ko ina,saboda Doctor mislihu yaui suna kwarai ,haka yana da jama’a . Ya yi suna ba don yana kudi ba sai dan kwarewarsa ta wurin aikinsa da sunan da yayi saboda asibitin su.
Kwana uku aka yi ana karbar gaisuwa ,mahaifiyar sa tace su za su tattara su koma kano,don ita har yanzu ba wai tana son Bahijja ba ne ,asali ma ta dauka nauyin mutuwar danta akanta saboda ta ce ita ta sa shi zama a lagos yaki komawa can gida kano,ya guje su. Tunda tayi sanadin sa to zasu kwace danshi su tafi da shi ta dinga ganin jikanta. Kuma ta ce ko da wasa Bahijja kar tayi tunanin cewa zata zo ko da ganinsa balle daukar sa.
Anan fa ciwon yayiwa Bahijja bibbiyu,hankalinta ya mummunan tashi. Ta yaya za a rabata da Muhammad da bai fi wata takwas a duniya ba ??
Ba irin rokon da bata yi musu ba har ta musu alkawarin kawo shi idan ta yaye shi,amma fur mahaifiyar mislihu ta ki. Haka ta tattara shi suka koma kano yana kuka Bahijja na kuka suka rabu.
**** **** *****
A wannan lokaci Bahijja tayi dan karamin hauka ,ko dai ta dinga jin muryar Doctor ,ko kukan Muhammad. Zuciyarta tayi rauni sosai,kullum tana cikin kuka,bata iya kulla komai. Daga karshe ita ke tashi ta share hawayenta,tayi karfin halin lallashin kanta.
Ta so ta bi iyayen Mislihu kano ,sai dai kuma ta tsai da kanta,ko me za su mata ba zata taba fada da su ko shari’a dasu ba albarkacin dansu da take so take ganin girma da darajarsa fiye da kowane namiji a duniya. Don haka ta sawa kanta hakuri,kamar yadda ta jure rashin mijinta shima dan nata zata jure rashin sa,in da rabon haduwarsu kuma da rai da lafiya to Allah zai hada su wata rana.
Haka Bahijja ta hau takaba ,kullum kwana take tana zubar da hawaye tana yiwa mijitan da danta addu’a tare da fatan Allah ya kara mata hakuri da juriya.
Daga ita se Baba Andi a gidan wacce take mata rainon Muhammad,kasancewar kyautatawa da take mata ta dauketa kamar uwarta,yasa itama ta zauna tare da ita tana mata hidima tare da bata shawarwari da bata baki da lallashi. Tana matukar tausaya mata.
Bahijja ta kasance bata da kawa ko wata ‘yar uwa ko wata da suke da kussanci na sosai,saboda a RAYUWAR BAHIJJA ba (space) na kawaye ,wato ba fili ko lokacin yin kawance a rayiwarta,saboda ayyukanta da rabuce-rubucenta. Mijinta da danta sune kawayenta,sune rayuwarta.
Don haka yanzu rayuwa tayi mata wahalar gaske wanda daga rubutun har aikin sai da suka gagareta,damuwa da yawan tunani suka sako ta a gaba,ta rasa inda zata sa ranta taji dadi . Tuni ta kma ga Allah ,kullum tana cikin karatun Alkur’ani da addu’o’i tare da yawan istigfari don neman waraka daga halin da ta shiga..
Wani lokacin takan rufe ido ta dinga tuno da kalaman Doctor wanda suke kara mata karfin gwiwa ,taji tana son mikewa tayi wani abu me amfani da rayuwarta bayan kuka da bacin rai.
Da haka a cikin wannan halin da yanayin ta gama takabar,sai dai duk da hakan ba tayi yunkurin fita fara wani aiki ba….
Sumy luv????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤
36
Bayan rasuwar Mislihu Alh. Umay ya samu labari don haka ya zo ya dauki Deeni bayan ya farfado ya samu sauki na jiki amma fa kwakwalwarsa tamkar ya farka da sabon abu ,kullum yana cikin firgita da yin wasu abubuwa tamkar yana tsorace.
Haka mahaifinsa yasa ana yi masa addua su ma suna masa ,har ya dan samu sauki,amma kam har yanzu da matsala . Yayin da kotu ta yankewa Dr. Yasir da sauran ma’aikatan asibitin hukuncin daurin rai da rai. Allah ka tsare mu da son zuciya..
Asibitin ya tsaya na dan wani lokaci saboda abunda ya faru da gidan da asibitin duk sun shia gado ,sai dai dama asibitin nasu ne su biyu da shi,sannan itama tana da gadonsa. A takaice dai wurin ya dawo nata da danta Muhammad ,wanda tayi alkawarin kula masa da shi ta damka masa kayansa wataran in tana da rai. Don haka ta shirya komai a rubuce saboda mutuwa ta kuma nemi lawyer na musulunci da Alkali suka zama shaida.
Watanni shida da rasuwar Doctor Mislihu bayan gama takabarta ta hau shirye-shiryen yadda zata farfado da asibitin yafara aiki,ya dawo kamar da,a niyyarta ma har yafida,saboda tsaro da tantance ma’aikata sai yafi nada.
Bahijja kenan mace mai kamar maza,haka ta dage tana ta shige da fita ba zama ,tana neman taimako da yadda zaayi komai ya farfado ,wanda gudun tunani da bacin rai yasa ta dage da zama(busy) yau bata nan gobe bata can har sai da ta tabbatar komai ya dai daita mata kamar yadda takeso ,komai ya farfado ya soma aiki,sannan ta samu nutsuwa kadan.
A kullum ta zauna maganar Deeni ke fado mata,da sakon da amanar taimakonsa da mijinta ya damka mata.
“Ya zama dole in nemo shi inji ya ya kare ? Sannan in sake duba (case) dinsa inga wane irin (treatment) ya kamata a masa.”
Bata bata lokaci ba ta fara binciken file din Deeni wanda ta riga da dama tasan wannan case din,sai kari akan (wrong treatment ) din da aka yi ta masa.
Nan ta bincika address dinsa,sannan ta sake zuwa asibitin da aka kwantar dashi tare da Doctor ta sake bincike akan treatment dinsa ,sannan ta sake tabbatar da address dinsa. Daga nan ta daura damarar niyyar taimakon sa har sai inda karfinta ya kare,in ta tabbatar ya samu lafia zata samu kwanciyar hankali ,burinta da na mijinta ya cika,daga nan zata ci gaba da cika burin mijinta da nata har ta Allah ta kasan ce akanta,idan kuwa Muhammad ya girmata damka masa dukiyarsa,ta ci gaba da masa addu’a da shi da mahaifinsa. Wannan shi ne burin Doctor Bahijja da kuma kudurinta ,bayan shi ba komai a zuciyarta da tuaninta ,daga aikinta sai rubuce rubucenta…..
Hmmmmm ,,Doctor MISBAH KENAN
Please kuyi hakuri aiki ne yamun yawa ????????????????????????
SUMY LUV ????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Written by. SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by. SUMAYYA SA’AD❤❤
37
Haj. A’i na zaune a falo ita daya tayi nisa sosai a tunani,tana tuna yadda rayuwarsu take da da ta yanzu,lokaci guda rayuwarsu ta canja ,sun baro yankin su cikin ‘yan uwa da abokan arziki,inda suka saba da rayuwarsu da komai ,sunyi nesa da dansu da ‘yan jikokinta guda biyu da duk da suna zuwa lokaci-lokaci,ga rayuwar Deeni ta canja gaba daya . Duk kokarin da suke yi akan Deeni ba wani canji,yadda Deeni yake rayuwa yana matukar kona mata rai. Lukman ne take dan gani taji dama- dama,shima tunda ya kammmala katarunsa na jami’a kullum yana tare da mahaifinsa wurin harkar kasuwancin sa,rayuwar su na cike da kewa da wani walwala.
Mai musu aiki ce ta katse mata tunanin,’”Hajiya kna da bakuwa”.
“”Wacece haka ? Daga ina take ?
Gata nan .” Ta bata amsa,sannan ta juya.
Bahijja tayi sallama tare da karasowa cikin falon, Hajiya ta amsa tana mata maraba tare da mta kallon rashin sani.
Bayan sun gaisa Bahijja ta kalleta,ta ce.
“Nasan zaki yi mamakin ganina,saboda baki sanni ba. Sunana Doctor Bahijja ,ni likita ce a asibitin da aka kai Deeni kwanakin baya,asibitin doctor Mislihu . Ni matarsa ce da muke aiki tare ,bayan rasuwarsa ni na ci gaba da kula da asibitin.