HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kafin ya rasu burinsa ne ya ga ya taimaki Deeni,sai dai burin nasa bai kai ga cika ba ta Allah ta kasance akan sa. Ina fatan cika masa wannan burin don haka nake son taimakon Deeni da dukkan kokarina har dai naga ya samu lafiya.

Bama bukatar taimakon ki”””””.

Sukaji muryar Alh. Kamar daga sama .

Dukkansu suka mai da kallon su kan Alhaji,ya ci gaba da fada.

“Yau ce rana ta karshe da zaki sake tako gidan nan ,kowa yasan irin yadda ku ka kara dagula rayuwar Deeni,ku ka yi wasa da lafiyar sa. Ku godewa Allah da banyi kararku ba.

Cikin sadda kai da girmamawa Bahijja ta ce.

“Alhaji dukkan mu ba wanda yaso abinda ya faru,kuma bamu yi haka da ganganba sai don wata kaddara da ta fada mana. Burin mu ne daga ni har marigayi maigidana mu ga muna taimakon mutane,haka taimakon danka yana daya daga cikin burin,don haka nake me rokon ka da ka kara bamu dama ,insha Allah zamu yi kokarin mu akan danka ya samu lafiya.

Alhaji dai ya dage Bahijja ma ta dage da kyar da kyar ta sha kansa ya yarda ,sai dai ta dinga zuwa duba shi har gida . Bata musa masa ba saboda tana son taimaka masa,don tasan an musu laifi ,sannan zata karasa abinda mijinta ya fara kamar yadda ya UMARCE ta.

Hajiya ce tayi mata jagora har zuwa bangaren Deeni,ta nuna mata kofar dakinsa. Nan ta cewa  hajiya ta koma ita zata shiga. Hajiya bata musa mata ba ta juya,ita dai addu’ar ta Allah ya bawa danta lafiya.

Tura kofar dakin tayi wanda yake mamaye da duhu,duk da rana ce amma ya rife ko ina kif. Yanayin garin kuma dama inba a kunna wuta ko bude windo ba babu ta inda haske zai shigo. Hakan yasa ta kara bude kofar don taga haske,nan ma ta hango window din dakin.

Kai tsaye ta nufi window din ta sa hannu ta zuge labulen tare da bude (windows) din daki duka ,tuni haske da wani irin iska mai sanyi ya dinga ratso dakin,nan ta maida kallonta gare shi ,yana zaune tsakiyar gado kamar kullum ya hade kai da gwiwa yana kife wuri daya.

Cikin nutsuwa ta matso gare shi ta tsaya tana kallon sa tare da nazarin halin da yake ciki . Kamshin turarenta tare da iska mai sanyi ne suka soma ziyartar sa,wannan ya dawo da shi daga wata duniya da ya fada.

Assalamu Alaikum Nuraddeen “. Ta fada cikin sassanyar murya.

Jin murya da bakon yanayi yasa shi dago kai suka hada ido,tayi masa murmushi ,shi dai kallonta yake.

Ta sake kiran sunansa,”Nuraddeen ,na maka sallama baka amsa ba,kasan kuwa shaidanun mutane ne kawai ba sa amsa sallama ? Kai kuma nasan ba ka daya daga cikin su,kai salihi ne,bawan Allah(you re a gentleman) nasan nan gaba in na shigo zaka amsa sallamata. Ni sunana Doctor Bahijja,amma zaka iya kirana da Bahijja . Ni sabuwar kawarka ce,abokiyar ka,naji baka da aboki haka kake rayuwa kai daya,nima bani da kawa don haka na cewa hajia me zai hana mu zama abokan juna ni da kai,? Ka fadamun damuwarka ,in fada maka nawa,mu bawa juna shawara. Ina  fata zaka amshi abota ta ?

Kallonta yake fuskarsa daure,sannan da alamar mamakin ganinta duk da yana jinta amma bai kulata ba ,daga karshe ma ya kau da kai daga gareta saboda Allah Allah yake ta fita ta bashi wuri,saboda ba abinda yafi kauna irin ya zauna shi daya ya fada wata duniya daban wacce take da bambanci da wacce mutane ke rayuwa.

Ganin ya juya kai yasa ta sake zagayawa ta fuskance shi,ta ce.

” Hakan na nufin baka amince da abota ta ba? Duk da baka amince da ni ba ni dai ba zan fasa zama abokiyarka ba,saboda Niraddeen shj kadai ne abokin da nake so nayi a duniya,saboda daga ji da ganin Nuradden (is special) .

Zan fara aikina daga yanzu kafin ka amince,shawara ta farko ka dunfa barin ( freash air ) yana ratsowa cikin dakinka,zai baka (good company) kuma zai kara maka lafiya ( it will keep u healthy nd cheer you up).

Na biyu,ni bana abota da kazamai,wannan dakin da kake zaune cikin kura ga kayanka a zube (,toilet )dinka datti,kai baka gyara ba,sannan ka hana a gyara maka. To in kanaso mu zama abokai sai ka koyi tsabta,kasan mu likitoci bama shiri da kazamai,din haka ka tuna kai abokin likita ne.” Tana maganar tana tattara dakin.

Ba shiri ya dazo kai yana kallonta,da ta ishe shi,yaji ranshi ya baci,ya mike a zuciye ya fisgi hijab dinta,yaja ta har kofar ya cillar ,fuska murtuk yace.

“” Waye abokin ki ? Bana son kowa,bana bukatar kowa arayuwata ,bana son kowa,ina so in rayu ni kadai,in kika sake zuwa nda nake zan kashe ki.

Bata yu mamaki ba ,dama ta zaci haka daga gare shi…

Murmushi ta masa,tace,” Shi yasa nake  son ka zama abokna,zan dawo gobe in Allah ya kaimu sai ka fada min damuwarka (and yes ) bana so in dawo in same ka da kazanta,ka tabbatar da kayi wanka.”

Rufe kofar ya yi da kardi ,ta jima tana tsaye tana kallon kofar,yayin da kwakwalwarta ta shiga zarya tana tunanin ta hanyar da zata bullo masa har taja ra’ayinsa.

Alama ta farko ta nuna mata yana cikin fushi da zafi ,na biyu kuma kamar yana cikin wani fargaba. Na uku ,alama ya nuna ya yanke kauna daga dukkan wani farin ciki da rayuwar duniya. Wannan ya nuna rauninsa akan addini a zahiri.

Ta jima tana nazari kafin ta juya ta samu Hajiya tana kaiwa da kawowa alamar jiran fitowar ta kenn,tana ganinta kuwa ta nufi wurinta da sauri. ”

“”Likita yaya kika ganshi ????

Bahijja tace,”kwantar da hankalinki Hajiya ,zauna zan miki bayani””.

Ta ce,”Insha Allah Deeni zai samu lafiya,zai samu sauki. Sai dai sai na danyi fama da shi,saboda na lura mutum ne me zafin zuciya da zafin rai,sannan yana tattare da wani fishi da bacin rai a tare dashi…

Sannan akwai wani (memories)* a kwakwalwar sa da yake son shafe su,ya mance da su. Yana so ya shafe wani bangare na rayuwar sa a baya wanda suke masa ciwon gaske. A kokarinsa na wannan yasa kwakwalwarsa ta kamu da ciwo ,rashin lafiya. Ba wai hauka yayi ba,kamar yadda Kai, ko zuciya ,ko ciki suke yyiwa mutum ciwo a jikinsa, haka kwakwalwa ma tana ciwo wanda dole sai ya sha magani zai samu waraka da yardar Allah. Sannan kuma ya kaucewa wannan tunanin.

Na biyu ,matsayinsa na musulmi ya samu rauni,na uku, na lura yana da matsala da duk wata dangantaka a duniya wanda ya jawo yasa ya tsani kowacce irin dangantaka ,har yasa baya kaunar kulla dangantaka kowacce iri ce da kowa ,yafi so yayi ta rayuwa shi daya.

Don haka Hajiya deeni na bukatar taimako kwarai wanda zan yi iya kokarin nayi,sai dai ba mai sauki bane. Mutum ne mai taurin kai da zafin zuciya ,tankwara shi ko juya shi abu ne mai wahala. Ina son jin tarihin deeni kakaf da ainihin shigar sa wannan halin ,saboda in san ta ina zan soma bi in taimaka masa..

Hajiya ta ja dogon numfashi ta kalleta ido cike da tsammani ,tace.

“Zan fada miki komai,tabbas Deeni danmu ne amma bamu kyauta masa ba ,bamu masa adalci ba. Zan baki dukkan wani hadin kai da kike nema domin inga dana cikin walwala…………

Please nagaji wlh ,,kuyi hakuri se da safe…………

Sumy luv????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

38

Deeni mutum ne wanda yake (full of life)kullum yana cikin dariya da zolaya gami da kyautatawa kowa,duk da yana fmda zafin rai yana da zuciya da fushi da kuma ra’ayi amma yana wuyar gaske ka fahimci haka,saboda kullum yana cikin wasa da dariya.

Duk wani abu da deeni yake so mu ba shi muke so masa ba,don haka muka sa shi yin abinda muke so musamman mahaifinsa ya danne abinda yake so yana yin abinda muke so saboda biyayya. Sun sha samun sabani da mahaifinsaakan abu da yawa ,amma daga karshe zai hakura yayi abinda mahaifinsa ke so.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button