HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Deeni bashi da rauni a addini,asali ma sanin addini yasa shi yi mana biyayya duk da mun fi ba da karfinmu ga neman ilimin duniya shi da kanss ya dage da neman lahira,don haka anan mu muke da rauni ba shi ba.

Ya yi amfani da iya ilimun da ya nemawa kansa na addini ,yana kokarin neman ilimin ne kuma muka raba masa hankali tare ds daga masa hankali akan karatun jami’a ,din haka ya qatsar ya koma bokon.

Raunin Deeni guda daya ne a rayuwa FARIDA.”

Sai a lokacin Dr. Bahijja ta ce wani abu tunda ta fara magana ,ta ce.

“Farida ?””

Mama ta girgiza kai ,tacd ,”kwarai farida,in akwai abinda Deeni yake so a rayuwa da muradi a rayuwarsa to farida ce. Dukkan ZURI’AR mu ba wanda bai san da haka ba,tun yana yaro har ya girma ya mallaki hankalin kansa,abinda yake so daya ne Farida,ita ce rauninsa……….

A hankali Hajiya ta labarta komai tun daga farko har karshen abinda ya faru.

Bahijja taji jikinta ya yi sanyi,ta matukar tausaya masa sosan gaske.

“Allah sarki bawan Allah.” Ta fada tana kallon mama .

” Tabbas ba ku kyauta masa ba ,mahaifansa ,dan uwansa da masoyiyyarsa,tabbas wannan cin amana ne mai girma,dole ya ji dukkan wata dangantaka ta fita ransa.

Tabbas ya yi kokari ma da ya tsaya a haka,Deeni jarumi ne,na jinjna masa,kuma  Nsha Allah zan taimaka masa ya fito daga cikin wannan kejin ya zo yayi rayuwar sa kamar kowa.

Kila da mutuwa farida tayi,zai iya daukar kaddara ya jure, da farida ce masa tayi Deeni bana sonka wani zan aura zai jure ya hakura,amma wannan abinda ku ka masa ya masa ciwo wanda ciwon da cin amanar shi yafi zama a zuciya da kwakwalwar sa fiye da Farida.

Yana jin cewa iyayensa basa son sa,ba sa kaunar sa,sun ci amanar sa. To in iyauenka za suki ka su ci amanarka zaka dinga jin to kai ina zaka shiga ? Ya zaka yi da rayuwarka ?

Abinda ciwo matuka,zaka iya jure tsana da kiyayyar kowa amma ban da mahaifanka,saboda mahaifanka ,’yan uwanka su ne kai,su ne rayuwarka.

Abinda Deeni yakeji, ciwon da ke cikin cikinsa da ni daku duk ba zamu iya sani ko fahimta ba sai shi sai Allahnsa. Ina fata Allah Ubangiji ya bashi lafiya,ya bani iko da taimakon iya taimaka masa,ya cire masa wannann ciwon da ke zuciyar sa.”

Ta mike ,’Ni zan wuce ,zan dawo gobe in Allah ya kaimu . Sannan zan ci gaba da bincike akansa daga gare ku,da fatan zaku bani hadin kaii””

Mama dake sharar kwalla ta ce,”insha Allah za muyi duk abinda ya kamata ,mun gode ”

Nan sukayi sallama ta tafi.

Alhaji dake tsaye yana jinsu hankalinsa ya matukar tashi,tsananinnadama ya kara shigarsa,tausayin dansa ya kama shi. Ya iso falon hankalinsa a tashe ,ya kalli hajiya.

” Ki yafe mun abinda na miki ,abinda na yiwa danmu ban kara fahimtar illar da na yiwa yara na ba sai yanzu.

Hajiya tsayawa tayi tana kallonsa,don kuwa a tsawon shekarun da sukayi na aure bai taba budar baki ya bata hakuri ba komai girman laifin da ya mata,haka bai taba nadama akan wani abu daya zartar don ra’ayinsa ba ….

*****       *****     *****

 

Washegari karfe sha daya ta nufo gidan,bayan ta gama zagaye marasa lafiya a asibiti.

Kamar yadda ta same shi jiya haka ta sake samun sa a yau,hannunta rike da tray.

” Asslamu Alaikum  Nuraddin”

Dago kai yayi ya kallera ya watsar,ta kalle shi ta girgiza kai..

*Ka.manta me nafada maka jiya? Ka dinga bude (window) ,kaga yau ka kara min aiki,dole in dinga zuwa bude maka (window ) tunda ina son abokina ya shaki iskar duniya.””

Nan ta zage komai kamar jiya ,sannan ta zo ta hada (coffee) ta mika masa. Ko kallonta bai yi ba balle ya karba,ya dage kai…

Bata hakura ba ,”kayi kokarin sha (I’am a very good coffee marker ).oh na gane ,ko sai na sa maka a baki ne ?

Nan tayi kokarin kai cup din bakinsa,ya yi saurin doke hannunta sai da cup din ya fadi kan tiles ya kashe har ruwan coffee din ya dan kona ta.

“”Auchhhh!!! Tayi kara.

‘”” In ba zaka sha ba meye na bigewa ? Kaga yanzu ka kona ni, ( u re such a bad friend ) “”

Har yanzu bai kulata ba,nan ta hau tattara glass di. Da ya fashe,bata ankara ba kuwa ya yanke ta. Ga mamakinta ta ga ya mike ya dauko (first aid box ) yayi dressing wurin ..

Ra jima tana kallonsa tana mamaki ,saboda bata zaci hakab ba.

Ya kalleta fuska a murtuke ,” Wai me kike so ne gare ni ? Na ce miki bana son ganin kowa a inda nake,bana bukatar wata DANGANTAKA !!!!

ya fada cikin tsawa da huci..

Kinji ciwo saboda ni,ban so,don haka kar ki sake kuskuren zuwa inda nake.””

Da karfi ya fisgeta zai yi waje da ita ,sai yaji kansa yana wanj irin sarawa ,yana masa azabar ciwo . Nan ya saketa ya rike kai yana nishin azaba tamkar mai shirin barin duniyar….

Hankalinta ya tashi ,tayi saurin ciro wasu allurai guda uku a cikin jakarta tayi masa a hannu,ta taimaka masa zuwa gado ya kwanta,bacci mai karfin gaske ya dauke shi. Ta jima tana zaune tana kallon sa cikin damuwa da tausayawa,sannan ta mike ta karasa abinda take yi a dakin ,sannan ta fita.

Haka Bahijja ta kasance kullum sai ta zo gidan du Deeni duk da baya son hakan,baya kulata,haka zata yi ta masa surutu tana masa hira,har ya soma sabawa da hakan.wataran cikin dabara zata dinga jefa masa magani cikin (juice) ko abinci.

Ganin har yanzu bata samu yadda take so ba tsawon qata uku amma Deeni ba shi da niyyar canjawa,don haka tayi niyyar sake canja salo,ta cewa hajiya tana son zuwa har kaduna gidansu Deeni inda ya zauna da inda ya yi rayuwa ,sannan tana son ganin farida don mata wasu tambayoyi akan deeni.

Hajiya tace,’Da zai yiwu da na rakaki,to amma ba inda zan iya rafita in bar Deeni,don haka zan yi waya in sanar da su Shamsu zuwanki,zan baki cikakken (address) ba zaki fuskanci matsala ba insha Allah “.

Ta mike ,”Na gode Hajiya da yarda da kuma hadin kai da kike bani.”

Hajiya tayi murmushi tace ,” Nice da godiya,ba abinda zan miki sai addua,Allah ya ska miki da lakhairi””.

Sn rabu akan zata yi kwana biyu kafin ta dawo…

****        *****        ****

Kwance yake yana ta juye-juye a gado ,ya rasa me ke masa dadi,tun dazu yake sauraron zuwanta amma shuru. Ya riga ya saba da tana zuwa kullum dai dai wannan lokacin,amma yau har yamma shuru..

Nan ya mike ya zuge labulen dakin kamar yadda ta saba masa,nan ya dinga kaiwa da komowa . Can ya bude kofar dakin ya fita abinda ya jima bai yi ba tunda ya dawo daga asibitin yana nan a cikin dakinsa.

Hajiya na tare da Alhaki a falon kawai sukaga Deeni bazata yana leke-leke ,a tare suka mike cikin mamaki …

” DEENI”

Suka kira sunansa a tare.

Ya kalli Hajiya yace ,”Mama ba wadda ta zo gidan nan yau?”

Kallon sa take da mamaki ,ta jima sosai rabon da taji Deeni ya kirata balle.magana,kuka zatayi ko dariya? Ta rasa.

Bai bata amsa ba ya koma ciki ya tuea kofa ya kwanta,kwanciyar da yaji bata masa dadi ba ,ya mike ya nufi bakin window ya tsaya yana kallon motoci dake wucewa bisa titi……….

Se anjima jama’a

Taku har kullum…

Sumy luv ????????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by  SAADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

ASTAGHFIRULLAH WA’ATUBU ILAIK

Allah kayafe mana kura-kuranmu,,,,Ameen

 

 

39

Zaune take a falo tana jiran isowar masu gidan,yayin da take kallon yadda aka tsara ginin gidan da yadda aka tsara falon.

Farida ta iso tare da ‘yan yaranta guda biyu suna ta tsalle-tsalle Deeni karami da Aisha,ta tarbi Bahijja cikin fara’a ,itama ta amsa tana daria ,suka gaisa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button