HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Deeni karami ne ya gaisheta,ta amsa tare da jawo su tana musu wasa da dariya ,tana tambayarsu makaranta suna bata amsa.

Farida ce tace,to maza a je ciki ayi wasa a barni zanyi magana da Aunty ko?

Nan sukayi ciki sannan ta maida kallon ta ga Bahijja tace,

“Hajiya tamun bayanin zaki zo,sai dai bata fada mana ko mene ne ba ”

Bahujja tayi murmushi tace,” Abu me muhimmanci ke tafe dani,sunana Doctor Bahijja,kamar yadda na fada miki ni likitar Deeni ce.

Jin sunan Deeni yasa fatida taji zuciyarta ta tsinke,hankalinta ya tashi. Nan da nan Bahijja tayi mata murmushi.

Keantar da hankalinki,ba wani abu me wahala yake tafe dani ba,illa iyaka inaso ki tainake ni in taimaki Deeni. Inaga wannan shi ne iya abinda zaki iya masa ki taimake shi shima yaci gaba da rayuwa kamar yadda kika ci gaba da naki rayuwar..”

Kanta sunkuye jiki ba kwari tace,”A shirye nake da in baki ko wani irin taimako ,zanyi farun ciki in har akwai taimakon da zan iya wa Deeni.”

Bahijja tace ,”Naji dadin hakan ,ina so ne ki fada min komai akan Deeni ,ina nufin ,halayyarsa,me yake so ? Meye baya so ? Banda wanda nasani ,a ganina kece mutum mafi kusa da Deeni,wacce tasan kananan abubuwa akansa wanda wasu ba za su sani ba. Komai ina son sani,me yafi sashi farin ciki,? Ya yake rayuwar sa? Kamar ( hobbies ) dinsa ,wane abinci yafi so ? Wanne yanayi yafi so? Me yafi sa shi nishadi da farin ciki ?

Farida tayi shuru ta fada duniyar tunani ,rufe ido tayi tana tuno komai a game da shi,tana tuno wasu yanayi da suka yi tare a da.

Ta bude ido jikinta a sanyaye tace,tashi mu shiga ciki”

Nan ta ja ta sama zuwa bangaren da Deeni yake ,ta bude mata dakinsa,ta kunna wuta haske ya bayyana ,ta ce.

Ga dakin Deeni wanda ya shirya shi da hannunsa,ina ga ganin wannan ko ban fadi ba zai fahimtar dake ko wanene Deeni.

Bahijja tayi murmushi tace,”Kwarai ddakinsa ta bayyana shi a zahiri,daga (study room) dinsa na fahimci Deeni mutum ne me son karance-karance.”

Farida tayi dariya,”Kwarai yana son karance-karance da binciken takardu tin daga kan na Addini har na boko.

Deeni ma’abocin ilimi ne ,ma’abocin soyayya. Yana samun farin ciki a kananan abubuwa,mutum ne me son zama cikin dabbobi,tsuntsaye da son kiwon su.

Deeni yana son (spat) yana son (swimming),yana matukar son MISBAH da labaransa”

Ras! Ras!!  Ras!!! Bahijja taji gabanta ya fadi,ta maimata

**MISBAH**

Ta tambaya cikin mamaki.

Farida ta girgiza mata kai ,’Kwarai MISBAH (the author )wannan marubuci Deeni yana sonsa da labaransa. (Ideologies ) dinsa suna matukar burge Deeni,a kullum in munyi fada da Deeni to akan littafin MISHAB ne ,har na dauki littattafansa kishiyoyina saboda ba abinda ke dauke hankalinsa daga gareni sai takardun MISBAH.

Tana maganar tana bude mata wani drowar dake cike da takardun MISHAB,gaba daya ba wanda bashi da shi,daga na hausa har na turanci,daga na labari har na addini.

Shuru tayi tana jnjina soyayyar da yakewa takardunta,ko ita bata da wasu copies na takardunta sai dai original dake cikin computer dinta…..

Lafiya Doctor ??;

Farida ta katse mata tunani.

Ta girgiza kai,,”Ba komai””

Farida taci gaba ,”Deeni yana son rayuwa mai sauki,haka nan yana son ganin ya taimaki marasa karfi. Deeni bai dauki rayuwa da zafi ba””

Magode kwarai da wannan bayanai naki da hadin kai da kika bani.”

Farida ta kalleta ,(please ) likita ki taimake shi””

Bahijja ta girgiza kai,”Nsha Allah.

Bahijja bata bar gidansu farida ba wanda ainihin cikin gidan su Deeni suka dawo tunda zuka koma lagos,sai da ta sa Bahijja taci abinci tayi wanda da sallah sannan suka rabu.

Bahijja ta gama abinda take a garin kaduna ,washegari ta hau jirgi ta koma lagos,tare da sake sabon shiri wa yadda zata tafiyar da Deeni.

Asslamu Alaikum”

Ta fada lokacin da take kutsa kai cikin dakin .

Yana tsaye bakin window bai juyo ba,ta karasa dab da shi.

” Deeni sallama nake ”

Nan ya juyo ya kalleta a yatsine ya watsar , sannan ya amsa ciki -ciki .

Tayi murmushi,yau ce rana ta farki da ya amsa sallamarra.

Tayi murmushi ,a ranta tace,”Wanann akwai son nunawa mutane isa.”

Gado ya nufa ya kwanta,ya juya mata baya. Ta matsa kusa da gadon.

Deeni abokina ba gaisuwa ? Ko fishi kake dani ne ? Sorry ”

Ta kama kunne,”Na tafi na bar abokina ,to ai ba laifina ba ne,in na zo baka kula ni,baka jinm maganata,ba ka taya ni aiki,shi yasa na dai na zuwa. Ina zaune yau a gida sai mind dina ya dinga fada mun Deeni abokina yana missing dina ,kuma gashi na zo ka juya mun baya..””

Duk surutun nab da takeyi bai ce mata kala bahar ta gaji ta kyale shi,can ta canja salo.

Naji labarin abokina ma’abocin son karance-karance ne,ko zaka iya fada min waye (favourite author ) dinka?

Har yanzun bai kulata ba,nan ta mike ta bar inda yake ta zauna kan kujerar dakr dakin,ta jawo jakar data zo da shi tafara ciro littattafan da ke ciki tans dubawa,har yanzun ya juya mata baya. Waya ta dauko tayi kamar tana magana.

‘”Naga kun samin sabbin littattafai har wanda bana karantawa,wa ya ce kusa min littafin MISHAB? Ni bana son karanta labarinsa,yabi ya ishe mu da labaran rikicin rayuwa ,duk labaransa na bakin ciki shi kullum sai wahalar da mutane ,kullum yana hada mutane da matsaloli.

In soyayya ce ma yayi ta wahalar da su,mutm ba zai samu wanda yakeso ba.” Tana maganar tana satar kallonsa.

Gani tayi ya juyo ya mai da hankalin sa kanta gaba daya,ganin ya mai da hankalinsa gareta tasa ta ajiye wayar ta juyo da sauri suka hada ido,ya yi saurin kau da kai.

Tayi dariya ta mike ta matso kusa da shi hannunta rike da littafin .

“Kasan labaran marubucin nan kuwa ?

Ya dago idanunsa ya tsareta dasu,”kar ki sake””

Ya fada yana kallonta har ta so ta rikice,akwai wani abu a muryar sa mai sa a saurare shi,kuma ayi yadda yake so. Zai iya controlling mutum da muryar sa kawai wanda za mu iya cewa baiwa ne da Allah ya yiwa Deeni…..

Tayi saurin cire idanunta cikin nasa,tace.

” Kar in dake me ?

*Zangin (best author ) dina MISHAB . Dazu kin tambayame ni waye beat writer na,to MISBAH NE”

Ta dan yi murmushi tace,”Ai ba zaginsa nayi ba,gaskia na fada”

Ba gaskiya bane,me kika sani akan rubutun MISBHA ?

“Fadamun ina son sani.”

Haka nan yaji yana son biye mata,yace.

“Ba zan fadi ba sai dai in kina so mu zama abokai kamar yadda kika nema ki dauko sabon littafin da kika ce ya yi sabo ki karanta mun,saboda yanzu ina da ciwon kai ba zan iya karatun ba. Kinga kema in kin karanta za kiji wani darasi ne dabirin (logic )hikimar da ke cikin rubutun sa.”

Tayi murmushi,”Me zai hana ? Zan karanta maka ,amma ba don mu zama abokai ba,,saboda na riga na zama abokiyarka tun tuni. Sharadin karanta maka labarin MISBAH shi ne,zaka dinga jin maganata,zaka dinga fada min damuwarka,sannan zaka yarda in dinga duba lafiyar ka”””

Lafiya ta ? Ya tambaya yana kallonta.

“Ban fada maka abokiyarka Bahijja likita bace? Kuma na lura abokina baya cikin koshin lafiya,kamar ciwon kanka,inka bani hadin kai cikin kankanin lokaci zamu yi maganin sa. Sannan kana fada min damuwarka in baka shawara ,kaga riba biyu ,yi sauri ka amince ,yi sauri ka yarda…”””

Kallonta yake yana mamakin ta,ita ko wace iri ce ? Bata fushi bata gajiya da magana,duk da baya kukata ba ta gajiya da duj halin da ya nuna mata,gashi har ta koya masa ya saba da ita da halayyarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button