MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zura masa ido tayi tana kallon sa,’Ina sauraron amsar ka””
Bai bata masa ba sai jan pillow da tayi ya hadasu waje daya yayi matashi dasu,ya dago kansa tare da dora kafs daya kan daya. Ya kalleta yace.
“Ina jin ki”
Tayi murmushi,’inason (style ) dinka da (attitude ) dinka “”
Tayi saurin ciro wani card da biro a jakarta.
“. Samin hannu mana (autograph)in zama mutum ta farko saboda nan gaba in ka fita kana yiwa ‘yan mata wannan halin zasu haukaxe akan ka,kasan “yan mata na son namiji mai aji (classic tall ,handsome) sannan ga (attitude);yana musu jun kai yana shan kamshi,maganaa ma tsada take masa,yanzu zan zo ince in suna son zuwa kusa da kai to su zo ta wajena,saboda ni abokiyarka ce,ta hannun damarka,har (Autograph )dinka ina dashi. A lokacin ni zan zaba maka irin matar da ta dace da (personality ) dinka ,wacce za ku dace,zata haifa maka (cute cute little angels)”
Tsayawa yayi yana kallonta kamar wata t.v,yana mamakin ra.
Cikin tsawa da daga murya yace ,”Zaki karanta ne ko a’a ? Na rasa wane irin tunani ne dake”
Ta harare shi,kai ,karfa kaga na ce ni abokiyarka ce ka nemi ka raina ni,ni yayarka ce,na girmeka (at least respect my age) ka daina min tsawa “”
Juya mata baya yayi ya kyaleta,dariya ma ta bashi,ya hau murmushi shi daya………..
RAF. RAF. RAF
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
A tafawa MISBAHA ,tasa deeni murmushi wanda ya rasa shi tsawon shekaru har ya fidda tsammani da kuma yin sa…
Sumy luv ????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤
40
Juya mata baya yayi ya kyaleta, dariyq ma ta bashi, ya hau murmushi shi daya.
Lekashi tayi tace, “laa ! murmushi nake gani a fuskarka ? Amma shan kamshin nan yafi maka kyau, gaskiya zaka daina murmushi kar ya bata maka kwatancen ka na (Mr. Attitude).
Karamin pillow dake gabansa ya dauka ya wurgeta dashi, tai saurin cafkewa tana dariya tace: “to tsokanar ya isa lokacin karatu yayi”. Nan ta dauko wasu littattafanta ta fara karanta masa. Ya juyo ya kalleta, “sabon littafin MISBAH”.
Nan tahau ‘yan kame-kame tana zare ido, ka bari wannan sai gobe, bari in fara maka da wani. Ban so, ya fada kai tsaye sai kin fara wannan. Sai tace naji (Mr. attitude).
Nan ta dauko wani littafin da tayi BALLE ta karanta masa, don haka kawai ta juya masa baya ta fara kirkiro masa sabon labari a lokacin, saboda duk littafin da zata karanta masa nata ya sani, kuma ba yadda za’ayi ta karanta masa labarun wasu tace nata ne, don haka tai dabarar kirkira ta hada masa labari a lokacin.
A hankali yaji labarin na ratsa shi yana taba zuciyarsa, yaji yana sashi nishadi, baisan yaushe ya juyo ba ya samata ido, dukda ta bashi baya, ya lumshe ido yana sauraronta. Dr. bahijja na ta kokarin hada labari kiran Sallah ya katsesu, tayi godiya ga Allah ta juya ta kalleshi. Lokacin Sallah yayi. Ya bude ido kinyi alkawarin ci gaba ? Ta girgiza kai, amma bayan ka dawo daga masallaci.
Mikewa yayi ya fita daga dakin ya nufi masallaci, sabanin da da yake sallah a daki.
Fitar sa ya bata damar gyara gadon, da kade kurar da take gadon, ta tattara dakin sannan ta fita ciki tayibdakin am don yin sallah.
Mama tasa aka kai masa abincinsa dakinsa, yayin d suka zaunanda Bahijja sunanhira wanda duk ya kare akan rashin lafiyar Deeni ne da irin canjin da aka samu sosai a tare da shi.
Deeni ya dunga kaiwa da kawowa cik8n dakinyqnq jiran dawowar Bahijja a haka ta same shi.
” kaci abincin kuwa ?
“sai kin karasa mun’”
Ta nade hannu, sai ka ci abinci”
” Banzan ci ba.. ”
“Nima bazan karasa ba ”
Nan ta bude abincin ta zuba nasa ta mika masa, karba yayi da karfi yana ci.
“Bi a hankali, karka kware, bakasan cewa akwai (manners) na cin abinci ba ma ? ”
“Ban sani ba mana na, sai kin fada mun”.
Ta girgiza kai,”za dai ka iya kirana yayarka amma banda mamanka”.
Murmushi yayi ya girgiza kai, ya kyaleta har ya gama cin abincin ya mika mata.
Tayi daria, (good boy) ,”Karbi magani kasha”
Bai musa mata ba saboda burinsa taci gaba masa da labarin da ya tsaya masa a rai, yayinda Bahijja ke tunanin ta ina zata fara karasa masa ? Haka dai ta zauna tana hado labarin tana jan ransa har bacci mai karfi ya fizge shi alamarmaganu da yasha ya fara aiki ,ta kimtsa dakin ta tattara jakarta (box) din maganunsa ta adana waje guda, tazo fita ta tsaya tana kallonsa.
“Ina tayaka murna da sabon canji da ka soma samu a rayuwarka, na fahimci kai mutum ne mai kirkin gaske da saukin kai duk da zafin zuciyarka”.
Sau da dama Bahijja kan debewa kanta kewa ta hanyar hidimar Dini da asibiti wanda ta lura suna taimakon juna ne ta sami abuda ke debe mata kewa, ta mance damuwarta da kuncin da take tsintar kanta na dan wani lokaci, yayin da inta koma gida da dare ne komai ya zam a mata sabo, soyayyar mujinta da danta ya dawo mata sabo.
A haka kullum Bahijja ke yi da Dini, har timetable na karatu ta sa musu, in sukayi karatu na addini kamar Alqur’ani da sauran takardu, sai tai ta kokarin hada masa labarin da take kirkira, daga nan sai shawarawri ya biyo baya. Cikin dabara da hikima da kwarewa irin nata ta ringa masa (brain therapy), tana bashi addu’o’i da magani na asibiti da Islamic medicine kamar su habbtis sauda da zaitun da makamantan su, tana bashi shawarwari masu amfani da misali kalakala.
Haka nan cikin dabara ta dinga dangana labarin da take masa na kirkira da labarin rayuwar sa, a hankali ta dinga saita tunaninsa har ya soma manta damuwarsa da bacin ransa. Ya tsinci kansa da rungumara sabuwar rayuwar da ya tsinci kansa, wacce yake jin dadinta. Kana ganinsa za kaga alamar sauki atre dashi, saidai a duk lokacin da yaga mahaifinsa ko yaji sunan dan’uwansa Shamsu yakan tsinci kansa cikin bakin ciki da damuwa.
Kamar kullum yau da ta shigo ta samu yayi kaca-kaca da jakar takardunta da suke karatu yana ta bincike..
” Meye haka Deeni? Me kake nema?
“Naji sauki ne nake neman littafin da kike karanta mun na MISBAH in karanta,meye sunan labarin ma ?
Ras !! Taji gabanta ya fadi.
Ya tsare ta da ido,”Ina littafin ?
Tayi saurin kau da kai ,xBan sani ba,don kawai kana neman littafu sai ka wargaza mun kaya? To sai ka tattara.”
“Bazan tattara ba.” Ya bata amsa kai tsaye.
Ba zan tattara ba ,kuma sai kin bani littafin nan.”
In naki fa ?
‘In kinki yau bazaki fita a dakin nan ba”.
Hannu yasa ya daddanna (password) din kofar.
“Ba zaki fita ba sai kin bani”
*Deeni “”Ta fada cikin zare ido.
“Baka da hankali ne ?
“Bani dashi ”
“Please ka bude ”
” In kina son tafiya ki bani.
Ya juyo ya kalleta ,”Kar ki damu ba abinda zan miki ,ni kanunki ne.”
Nan ya dare gado ya hau ya juya mata baya tana ta masa masifa amma bai sairareta ba.
Nan tayi ta kokarin daddanna numbers din tana kokarin canka,yace.
In kika yi sau uku ba dai dai ba to ko ansa na dai dai din ma bazai bude ba,kinga zama daram ni dake (my sweet)yaya.” Ya fada cikun zolaya.
Nan ta hau masa magiya har yamma ,tace masa ta tafi da littafin gida ta manta ,gibe zata kawo masa.
Nan ma bai kulata ba ,nan fa ta hau lallaba shi tana lallashi,duk wannan bai yi aiki ba.
Ta ce,”Deeni in na tafi fa ba zan sake zuwa ba,ka manta sharadin mu zaka dinga jin magana ta ??”