MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

CIGABAN LABARI
????????????????????????MISBAH????????????????????????
writting by SA’ADATU WAZIRI
COPIED BY SUMAYYA SA’AD(sumy luv❤)
04
Nuradden da farida sun kasance makwabtan juna,gidajen su na kallan na juna ,haka nan akwai mutunci da zumunci me karfi a tsakanin gidajen,akwai abota a tsakanin iyayen deeni da na farida,,haka iyayensu mata wanda zaman unguwa daya ne kawai ya hada su,duk da yanayin rayuwarsu da dukiyarsu ya ban bamta,,wannan be hanasu abota da zumunci da juna ba.
Mahaifin deeni mutum ne dan kasuwa ,mai dukiya. Rayuwar gidansa kuwa zamu iya cewa rayuwace ta yan bariki tsantsa,dayawa sukan masa lakabi da bakin bature ,saboda yanayin rayuwar sa .
Matar sa daya hajia A’i da yaransu maza uku rak. Shamsudden shine babba, sai Nuruddeni da kaninshi lukmanudden wadan nan sune yara hajia A’i .su biyar dinnan su ke rayuwa a gidansu,sai ma’aikatansu,sai dai lokaci lokaci yan uwa na kawo musu ziyara..
Alh Umar mahaifin deeni duk da turancinsa da bokon sa bashi da wani mugun hali, ko wani mugunta . Mutum ne me kirki da alkairi ga mutane,jamaar unguwa sunajin dadin zama dashi da mu’amalar sa da su . Shi dai kawai baya so a shigar masa rayuwa,ko wani shisshigi ta fannin gidansa ko iyalinsa. Haka mutum ne me yanke shawara akan abinda ya ma sa ta harkar gidansa ko iyalinsa,mutum ne ne ra’ayi da akidar tsiya.. bai shiga harkar rayuwar wasu haka nan beso a shiga nashi. Mutum ne da in ya yanke abu ba wanda ya isa ya canja mishi ra’ayi..
Duk wani abun jin dadin rayuwa ya mallakawa iyalinshi,,matarsa da yaransa,,haka sauran dangi da iyayensa ya wadata su da duk wani abu da zasu bukata. Sai dai fa yaransa da matarsa shi ne me yanke musu hukunci,duk wani abu dazasuyi kamar ta fannin karatunsu,me zasu karanta ,a ina zasuyi karatun ,da sauran su…
Shamsu babban danshi yasa shi ya karanta fannin kasuwanci domin taimaka masa wurin business dinsa,yana da shekara ashirin da bakwai a duniya ya kammala masters dinsa,yana aiki tare da mahaifinsa a kamfaninsu.
Suna zaune cikin garin kaduna ,sai dai mutanen gombe ne ,,gaba dayan zuriarsu suna can gombe.
Shamsu yayi karatunsa a waje ,sai nurudden da mahaifinsa ya ce medicine zaiyi duk da kuwa baya so,sai dai bai masa musu ba saboda sanin hali irin na mahaifinsa.
Tun suna yan yara shine me yanke hukunci ,ko da abincin da zasuci ne ,hatta suturar da zasu sa shike yanke musu hukunci . Sai dai wannan shekararsa ta biyu ,amma abin ya gagara ,duk nacin sa ya kasa,har yanzu yana aji daya ,duk yan ajin su da suka fara tarw sun wuce sun barshi.
Mahaifinsa yaso turashi waje kamar yadda yayiwa shamsu ,sai dai ranshi nason deeni da yawa da bazai iya nisa dashi ba. Cikin yauansa yafi kaunarsa,ba mahaifinshi kadai ba duk wanda ya zauna dashi sai yaji ya shiga ransa,yana kaunar sa.haka nan Allah yamasa wannan baiwar. Halayyarsa da dabiunsa abin so ne da shaawa ga kowa,dan haka yasa duk tsananin Alh umar amma yana dagawa deeni kafa..
Wannan karan deeni zai sake jarrabawa ta shiga aji biyu a ABU zaria,yayin da babanshi ya mishi alkawarin yi mishi duk abinda yakeso matukwar yaci jarrabawarsa. Haka nan deeni ya dage domin a zahiri ba abinda deeni yakeso kamar farida,,zai yi dukkan iyawarsa dan mahaifinshi ya bashi farida ,ya aura masa ita .
Soyayyar farida da deeni da shakuwarsu ya samo asali,tun suna yara ,tare suka tashi suna girma,saboda zumuncin da iyayensu mata sukeyi…. Deeni ya girmewa farida da shekara hudu ,tun suna wasan yara har takai ga suka fara girma da abota,har ta juye soyayya da shakuwa me tsanani,,wanda mutum bazai gane wayafi son wani ba a cikinsu. Iyaye da yan uwansu duka ba wanda beson maganar soyayyarsu ba . Mahaifiyar deeni na matukar son farida sabida kaunar da sukewa juna,da kuma irin tarbiyyarya da nutsuwarta . Ta fita daban da yan uwanta.
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Writting by SA’ADATU WAZIRI
COPIED BY SUMAYYA SA’AD(sumy luv❤)
06
Tunda deeni yadawo daya masallaci bayan sallar isha ya zubawa wannan littafin na MISBAH ido,wanda faruda tayi wurgi dashi ,labarin ya taba zuciyar sa da tunaninsa,yanason sanin ya aka kare amma kuma alkwari yayi ,haka nan farida na gava da wannan labarin .
Yasa hannu ya dauki littafin yasa shaida a inda ya tsaya ,ya rufe yana kallon littafin har yasa shi cikin wata karamar drower ya rufe ,yana tunanin kalmar nan ta sauyin SHAUKI anya kuwa ?change of emotions gaskia hakan bai yiwuwa ba,gashi shi yakan gasgata duk wani labaran MISBAH ,yana da yakinin duk wani abinda ya fada yana iya faruwa,infact yana ma faruwa gana gani ,to amma wannan karon yana da ja ,sabida bai taba yadda shauki yana canjawa ba ,musamman ma shauki irin nasa,shauki na gaske ,shaukin da ya jima yana gina shi gini me karfi da tushe ,rushe shi abune da bazai taba yiwuwa ba balle a akai ga canji ..
Nan ya yi saurin canja tunani ya dakko littafin sa yana karantawa ,amma fa karatun babu abinda yake tunawa sai littafin . Tuni haushin kansa ya kama shi , ya ma zaayi ya bari haka ta faru dashi ,?
Zuciyarsh yaji tana zafi ,,deeni akwai dan banzan zuciya,tuni yaji tana hawa. Rufe ido yayi yana addua cikin zuciyarshi,sannan yayi saurin mikewa yabar study room din ,ya nufi cikin dakinsa ya dakko laptop dinsa yana kallon hotunan farida yana murmushi,,wasu hotunan nata tun tana jairirya,wasu kuwa tana yarinya ,,wasu kuwa suna tare tun suna yara har zuwa girmansu..
Waya ya dauko ya buga mata ta dauka tana murmushj tare da kashe murya tana mishi kalaman soyayyar da yake so,wanda suke kara haukata zuciyar sa da soyayyarta.
Lumshe ido kawai yayi yanajin kaunarta na bin jikinsa,yana ratsawa tare da hango su suna gudanar da wata aurw ne tattare da tsananin so da kauna,,tarw da farin ciki mara iyaka.
Bayan sun gama wayar ne ya tirawa MISBAH labarinsa kamar yadda ya saba ta email dinsa,yana yawan sharing feelings dinsa da kuma experience dinsa akan soyayyarsa da rayuwarsa ,da tarin tunaninsa da kuma hangensa, harma yayi challengn sabon labarin sa da ya rubutu na CHANGE OF EMOTIONS .
Duk da MISBAH bai taba bashi amsar emails dinsa ba bai sa ya fasa rubuta masa ba ,,saboda yasan ba dole ne saya karanta ba,kuma in ya karanta din ma ba dole ne yabashi amsa ba. Irin su misbah dole za suyi jin kai da miskilanci,duk littattafansa yana nuna illar girman kai,,don kuwa Allah ke bada daukakar da mutum zai yi takama dashi,in yaga dana zai iya kwacewa darw daya,wanda a wannan lokacin muamalarshi da mutane zai iya taimakonsa,sai Allah sai dai yasan akwai mutane dayawa da suke da bambanci a rubutunsu.
Rashin amsar da misbah baya bashi be damshi ko ya bashi mamaki ba ,saboda dama ya zaci haka daga gareshi. Yasha masa tambayoyi amma shuru ,dan haka ma wannan karan yana gama tura masa email din ma ya rufe . Da da jyar yasamu karatun ya fara shiga yana fahimta kadan kadan har bacci ya dauke shi ..
Deen matashin saurayi ne dogo ba baki,kyakkyawan gaske . Ba kyanshi zai sa kasoshi ba se halayyarshi ,yana da shiga zuciya . Matashi ne da yake da kula da addininsa sosai,ya yarda cewa Allah zai taimakeshi a rayuwa,zai cika masa burinsa na samun mace saliha,kamila ta gari…
Bayan bautar ubangiji da biyayya ma iyaye deeni bashi da wani buri da wuce yayi aure ,rayuwar cikin aurw da yadda ya tsara zai yi shi,rayuwa ce me cike da soyayya da kuma ibada irin wadda annabin mu (SAW )ya yi da matansa,dan haka kullum adduarshi Allah ya cika masa wannan burin nasa tarw da farida.