HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya juyo ya kalleta,”Maganar ki wanne ne banji ba ? Na sha magani,na ci abinci irin wanda kike so,na sa kaya irin wanda kike so,na saurari shawarwarinki ,kullum muna karatu tare sannan yanzu mu abokai ne ,surutun da banayi kinsa na fara magana ,tun banaso har na fara so,menene baki sani nayi ba Doctor Bahijja………..Oops Abokiyata Bahijja?

Ta daka masa harara ,”Akwai abinda ya saura baka yi ba,shi ne kunce abotar mu,daga yau na daina abotar ,kuma ta window zan fita kaje ka nemi wata abokiyar ta karanta maka labarun ,don ba zan baka littafin ba ,kuma ko ina zaka shiga ba zaka samu ba.””

“Me yasa?

Ya bata amsa,,”saboda ke ce MISBAH da zaki hana ni ko kuma zaki boye mun labarin. Sannan batun neman wata abokiyar bazan iya ba,saboda ko bakomai a tare da ke akwai muryar da take taba min zuciya in kina karanta min labarin, don kuwa ko shi MISBAH da ya rubuta labarin in yaji yadda kike karantata shi da dukkan (feelins) dinki da (emotions )dinki zai ji kamar ba shi ua rubuta ba.

Sannan batun fita ta window kuwa Bismillah,iyakaci kugunki da kafarki daya ta karye,iyaka ta in sai miki ayaba da lemo””.

Harara ta galla masa,ta kuwa nufi window gadan-gadan zata fita ,ya yi saurin fisgota fa rigarta.

Ta daure fuska ,”Ka kyale ni””

Zuwa yayi ya bide mata kofar ,”Fita,kin kira kanki da abokiyata amma ba zaki iya daukar wasa da nake miki ba.””

” Eh bana son irin wanan wasan. “”

Nan ta sa kai ta fice ,ya lura ranta ya baci,sam baiji dadi ba.

Kwana uku Bahijja bata zo ba,Deenj ya rasa me ke masa dadi? Ya samu sabuwar rayuwa tare da ita da (company) dinta.

Hankalin sa ya matukar tashi da rashin ganin Bahijja ,ya kasa hakuri har sai da ya tamvayi mama ina ne gidansu ne ? A wanne asibiti take aiki ?

Mama ta kalle shi,Deeni kenan yanzu duk zuwan da Bahijja yake gidan nan baka taba tambayarta ita wacece ko daga ina take ba ?

“Mama ki ban amsa.”

“”Nima ban sani ba ,sai na bincika. Zan tambayi mahaifinka””

Ranshi ya baci,ya juya ya koma ciki. Wanan ya bata damar yowa Bahijja waya ta fada mata halin da yake ciku.

Bahijja tace,””Mama ina ga lokaci yayi da Deeni zai soma zuwa asibiti yana shiga cikin ajin da muke musu (lecture da ba da shawarwari,ya kamata ya fara shiga mutane. Munyi mai wuyar,kiris ya ragewa Deeni. Kafin ya samu waraka sai ya dai na  kebe kansa a gefe……

Wannan kenan

Sumy luv ce dai har kullum????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA  SA’AD❤❤

Assalamu Alaikum

Gaskiya ina matukar jin dadin yadda jama’a da dama ke binmu da nuna jin dadin wannan labari,hade da qara min kwarin gwiwa,da addu’o’i da nake samu,duk da wasu sun san cewa bani na rubuta ainahin labarin ba……….????????????????????????????????

42

Bahijja tayi kokarin janye kanta daga gidansu Deenj saboda tana gani lokaci yayi da zata janye daga gareshi,yanzu ya sona dawowa hayyacin sa. Abu kalilan ne ya rage masa yawan nasiha da masa tuni akai-akai, don haka ta bada shawarar in yana zuwa daukan darasi a (couselin center ) dinsu zai mike.

 

Mama ta same shi a daki ta mika masa (address)din su Bahijja,ta lura yana cikin damuwar rashin zuwanta,tabbas Bahijja tayi tasiri a rayuwar Deeni.

 

Tunda ya karbi (address) din yake tunanin yaje ko a’a ? Haka zuciyar sa da kwakwalwarsa suka dunga tun zura shi da ya je.

Washegari ya shirya ya fita,tunda ya shiga wurin kwakwalwar sa ta dinga tunano masa da abunda ya faru. Hankalinsa yaji yana tashi, yaji kamar ya koma,ya tsaya shi dai bai shiga ba shi bai fita ba.

Wani ma’aikacin wurin ne ya masa magana.

“Malam wa kake nema ? Ba a tsayawa a nan,ko shiga ko fita””.

Deeni ya kalle shi ya mika masa hannu suka gaisa,sannan yace.

“Ina tambayar Doctor Bahijja ne “”

Mutumin ya kalle shi yace,”Madam tana can bangaren koyarwa ,tana cikin aiki amma ka jira in ta gama zan mata magana,in kuma kana sauri sai ka dawo gobe da wuri kafin ta fara aiki.

Deeni yace ,”In ba zaka damu ba ka raka ni zuwa inda take sai in jirata a can””.

Tare suka jera da mutumin zuwa ciki,suna fatiya yana kalle-kallen yadda wurin yake,da irin jama’ar da ke zarya a wurin.

(Hall) ne dan madaidaici cike da majinyata kuma dalibai,Bahijja tsaye gaban su tana ta bayani,tana ilmantar da su tare da wayar musu da kai,su kuma suna mata tambayoyi tana basu amsa,yayin da ta dinga binsu daddaya tana tambayarsu matsalolinsu suna fada mata tare dsmusu misalai da mutane daban-daban. Wani lokaci takan koma tarihin Annabawa,Sahabbai da manyan bayin Allah da irin gwagwarmayar da suka sha a rayuwa. Don haka ba wani bakin ciki ko bacin rai da zai saka tsayawa da rayuwarka bayan kana da Allah da addini,kuma Allah ya baka yadda zakayi in ka koma ga Alkur’anj ,sannan zaka ga kai baka da matsala ma kan tasu ko na wasu.

Allah ya mana kyautar rai da lafiya ne don mu bauta masa,don samun rabo duniya da lahira,ba zamu samu wannan babban rabon ba sai mun kula da kanmu da lafiyarmu,sannan muji dadin kyautata idar mu.

Nan ta basu addu’o’in da za suyi na cikin Hisnul muslim,wanda yake cike da azkar din da Annabin mu yayi,kuma ya yi umarni da a yishi.

Deeni ya harde hannu a kirji yana tsaye ya kwanyar da kai yana jin ta da saurarenta,maganganunta na ratsa shi. Hikimar ta na iya zance da iya fahimtar da mutane ya burge shi,iliminta da fahimtar ta yasa shi jin wani sauyi.

Ya zura mata ido yana kallonta yana murmushi,wai da wa wannan likitar ke masa kama ? Yanayinta,koyarwarta,hikimarta akwai inda ya sansu.

Kamar da wasa ta juyo sukayi ido biyu,ta hango shi tsaye gabanta. Nan ta dage kai kamar bata ganshi ba.

Murmushi yayi ya kutsa kai ajin ,ya wuce kai tsaye gabanta ya kama kunne.

“Sorry”

Bata kula shi ba,ya juya ya kalli ajin ,”Sannun ku ‘yan uwana dalibai majinyata,wannan. Malamar ta ku kuma likitar ku nima malamata ce kuma likita ta,na mata laifi na zo bata hakuri kuma nima daga yau zan fara zuwa ajinku,ku tayi ni bawa malama hakuri na dawo dan uwanku kuma abokin ku.”””

Nan suka hada baki suka ce,,”’muna maraba da sabon abokin mu..””

Suka kalleta ,”Malama kiyi hakuri..”

Nan suka sake hada baki suna ta bata hakuri har sai da ta amsa ta hakura,Deeni ya kafa mata ido yana mata dariyar zolaya. Bata kula shi ba har suka tashi ya bita har (office)a nan ya sata gaba yana ta mata naci tayi hakuri.

” Ba zan kyaleki ba kamarnyadda baki kyale ni ba kwanakin baya,kiji ya fitinar take ? Gara ma ki hakura mu shirya.”

Ta kalle shi ba alamar wasa,ta ce.

“Mr . Deeni ,nan ba gida bane,wurin aikina ne inda ma’aikata na ke ganin girma na da girmamani ,don haka ban son wasa. In har zaka ginga zuwa daukan darasi to ba wasa,muna da (discipline)da dokokin da zaka kiyaye. Ba latti,ba fashi,kuma ba yin yadda kake so..””

Dauke kai yayi ya bata fuska,”Bana son (classes) din naki.””

Ganin yadda ya juya ya murtuke ,lokaci daya kamanninsa suka canja ya  firgita ta,ta mike .

“”(Please )mana Deeni ,ka saurare ni”

Damuwa ta bayyana karara a fuskarta.

Nan kuwa ya kwashe mata da dariya yana tsokanar ta.

“Na firgita wata .””

“Deeniii “””””

Ta fada tana zare ido.

” Kai ki,zan kama ka ne .

Dariya yayi yabfita yana fadin,” Gobe karfe tara na safe (i will be here )ba latti ba karya doka,ba fashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button