MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nan ta bishi da kallo taba dariya,har ya tafi ya dawo.
“Zan sami littafin nan ki sunan littafin ??””
Juyawa tayi bata kulashi ba ,ta rufe kofar office din. Don haka Deeni ya dage da zuwa kullum ba fashi,haka kullun yana mata nacin labarin nan ko sunan sa,amma bata saurare shi ba,va irin nacin da bai yi ba har ya hakura. Har (internet )ya shiga yana (searching)sabbin littafan MISBAH amma bai samu ba,tun na karshe da ya sani da ba sunan wani sabo a cikin list din littattafansa.
Abun yana matukar daure masa kai,duk nacinsa da kokarinsa ya kasa samun ko mutum daya da yace ya samu sabon littafinsa.
Haka Deeni ya samu sabuwar rayuwa tare da sabbin mutane da suke tare da Doctor Bahijja,killum takan musu darasi tayi musu tambayoyi,duk wanda ya ci takan fita da su yawo zaga gari,da zuwa ziyarar wuraren tarihi na ilimi. Duk wanda ya warke gaba daya a sallame shi
Anan Deeni ya dunga taimaka mata da wasu ayyukan kasancewarsa likita,duk da kwarewar sa da karatun da bai kai nata ba zama da ita yau da gobe yasa ya fara sabawa da koyon aiki sosai ,daga dalibi ya bige da (praticing)da (training).
Bahijja takan yi mamakin kokari da nuna kware na Deeni gashi da saurin fahimtar aiki,tabbas da ya jima yana aiki da karo karatu da ba karamin taimako zai yi ba …
A kwana a tashi Deeni ya ya warware ,shakuwa da sabo yana karuwa tsakanin sa da Bahijja ,zukan wuni tare a asibiti suna aiki tare.
Sai dai har yanzu Deeni bai taba fada mata damuwarsa ba wanda ke cinsa,abinda iyayensa da farida suka masa ya kasa mantaws da wannan cin amanar,haka kullum gudun haduwa da su yake,gudun maganarsu yake ko jin labarinsu. Wanda Bahijja kuma ta dage sai ya fuskanci abin ya wuce ya huya,sai dai duk kokarinta ya kauce….
Bai taba tambayarta ta tarihinta ba ,haka bai taba fada mata nasa ba,a haka suke zaune ,haka nan har yanzu bai fasa binciko labarin MISBAHA ba………
Yaseen ya nagaji zan je hutun sati????????bayana ya rike????????
Sumy luv????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA
SA’AD❤❤❤
Assalamu Alaikum
Masha Allah!!! Bisa ga hutun zango da muka dauka ,yau Allah ya dawo damu…Nagode da kulawarku a gareni ,Allah ya kara zumunci. Masu cewa ko lafia aka jini shuru ,,,wlh lafia lau sai dai Dan Adam da baa rasa shi da wasu yan hidimomi nashi na daban …
Sannan dan Allah ina fatan baza’a kuma samun miskila kamar yadda aka samu a baya ba ,,wannan abu nina sa kaina pls nd pls abarni murabu lafia da kowa kamar yadda aka fara tun farko….
Ina godia ga big Aunty Allah ya barmun ke bisa ga jajircewarki wajen ganin nacigaba da wannan rubutu(Aunty zee )maman nawal❤❤❤❤love u wujiga wujiga????????????????????
42
Wata safiya Bahijja da Deeni bayan sunyi aiki sun gama da marasa lafia,suna zaune a (free time )dinsu ,Bahijja ta kalleshi .
”Deeni, me yasa ka ke gudun mahaifinka ? Me yasa baza fuskanci gaskia ba da abinda ya faru ? Abinda ya faru ya wuce,kayi hakuri ka yafewa dan uwanka,wannan kaddara ce,bashi da laifi . Farida taci gaba da rayuwa,tana rayuwarta da mijinta da yaranta,me yasa zaka yi ta kuntatawa kanka ?
Idanunsa ne suka kada sukayi jaa,ranshi ya mummunan baci,duk da haka bata fasa maganar ba.
Deeni (you have to let go of ur past )ba zai yiwu ka rike su a zuciyarka ba kana wahalar da kanka,please ka yafe musu….
Nan kuwa taga ya haukace mata yana zazzafa mata bala’i….
Bazan yafe ba,saboda me zan yafe ? In ma na yafe nusu kina nufin zan iya mantawa da abinda suka mun in zauna lafia da su ? Ko na yafe musu bani ba su,bana son jin maganar su a ratuwata,na tsane su,zan iya kisa idan na ganus gabana…
Ta kalleshi cikin fuskar damuwa ta tsiyaya masa ruwa mai sanyi a cup ta mika masa,tace..
Please Deeni zauna… Ya zauna amma bai karbi ruwan ba
Saurare ni Deeni,in har ka dauke wannan zafin a ranka ba zaka iya yafe musu ba ,ko tsana ne ko so je ka sake shi a ranka,ka fiddashi a zuciyarka akansu. Ganun su ko maganarsu dole ne ,dan uwanka ne uwa daya uba daya,zumunci dole kayi,Allah ne ya ce kayi.. Gaba ma ba zakayi da musulmi dan uwanka ba balle dan uwa na jini.
Farida kuwa akwai lokacin da kyakkyawar dangantaka ta hada ku,yamzu kuwa matar yayanka ce,dole ka yarda da wannan….
Mahaifinka kuwa in kayi fada da shi baka da riba ,duk kai zaka sha wuya kaita wahalar da kanka…
Kayi hakuri Deeni,Allah zai baka ladan hakurin da kayi,ya kuma baka sakamako mai kyau a duniya da lahira….
Tana maganar kamar zata zubar da hawaye….
“”kamar kani kake a gareni ,ba zan so ganin kanina cikin wannan halin ba…
Tsura mata ido yayi yana kallonta,maganarta na ratsa shi,haka nan ya dinga jin maganganunta na masa tasiri a zuciyar sa ,yaji zuciyar sa ta sauka ,tayi sanyi..
Ya dauki ruwan sanyin yasha ,ya kalleta ya mata murmushi tare da mika mata tissue.
“” Gashi ,share hawayen da ke shirin zubo miki,kar su zubo in miki tsiya nan gaba…….
Murmushi tayi ta amsa,”Deeni ba zaka canja ba,tashi yau kaine best student koyarwar da na maka ya shiga kwakwalwarka da zuciyarka,don haka yau da kai zamuje outing..
Yayi daria ,”yau ta ina rana ta fito Abokiyata DoctorBahijja zata fita dani yawo ??
Murmushi tayi bata kulashi ba ,taje ta dauko mota ya shiga suka fita…
Kai tsaye suka wuce asibitin gwamnati na garin suka dinga bi tana nuna masa marasa lafiya,wasu gasu nan kwance cikin azabar ciwo ba lafiya wasu ga ciwo ba kudin magani,wasu na son yin ibada da sauran ayyuka ba lafiya. Abin tausayi kala-kala da ya fara sa jikin Deeni mutuwa,daga nan suka wuce sauran asibiti na masu kudi su kuma ga kudin ga komai amma lafiya da saukin Allah bai nufa ba…
Daga nan suka zarce gidan marayu,marasa galihu ,masu neman taimako basu da kowa bansu da komai sai Allah, sai abinda gwamnati taga dama ta san musu,suna watse basu da mai tallafa musu,ba uwa ,ba uba da zasu lallashe su,basubda wanda suka damu da su da rayuwarsu. Anan Deeni ya ga abun tausayi sai da ya zubar da kwalla…
A mota duk jikinsa yayi sanyi ,Bahijja ta kalle shi tace,
“” Yaya bakin cikinka da dacin ranka yake da na wadannan bayin Allah ? Baka ganin ni’imar da Allah ya maka,kana da lafita da karfinka da gatanka da iyayen da suka damu da kai…
Anta baka ganin matsayin iyaye ya kai suyi mana yadda suke so ko da bata mana rai ne suna da hakki?? Deeni rayuwar nan tayi kadan mutsaya muna bata lokacin mu akan wani bacin rai ko tsana,gaba ko wata kiyayya…
Ka godewa Allah da ni’imomin da ya maka,in ya jarrabe ka sai kayi kokarin ka ci jarrabawar . Ka yarda da kaddara,ka saki ranka kayi hakuri Allah yana tare da masu hakuri(innallaha ma’assabirin????)…
Yayi murmushi idon shi jawur,hawaye ya gangaro masa,ya ce.
“Nagode Bahijja ,tabbas kin cika abokiya tagari,likitan da tasan hakkin patient dinta,sannan ke mutumiyar kirki ce,Allah ya miki sakayya da abinda kika mun. A yau kinsa naji wani kunci da nauyi ya bar zuciyata ,duk wani fushi da kiyayya da nake ji a raina ya tafi …….
Tabbas nayi nadamar bata lokacina da nayi,sai dai insha Allah zan gyara gaba ,daga yau,daga yanzun nan Deeni ya zama sabon mutum wanda ba ya rike da kowa a zuciyar sa,ba ya fushi da kowa. Ina jin zuciyata fara , zanyi kokarin gyara rayuwata da tsakanina da iyayena da ‘yan uwa na…