HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Yau ce rana ta farko da nakeji da son fuskantar yaya Shamsu da Farida ba tare da wani bacin rai ko tsanar su ba, na yarda na amince haka Allah ya hukunta mun. Na gode Bahijja …

Lumshe ido tayi hawaye na gangara wanda bata san yaushe suka zo ba ,tana fadin..Alhamdulillah “”.. A ranta..ya tsura mata ido yana kallonta,kamar wata bakuwa ko sabon halitta,kaunarta yaji ta shiga ransa,haka yana bata wani girma na musamman.   Ta mike,”Yau ranar farin ciki ce garemu da ni da kai,sai godiyar Allah .yanzu saura guri guda zan kaika,ina fatan zaka ji dadin zuwa wurin “”

” Me zai hana ?” ya bata amsa ..

“”Musamman inda ke a wurin..

murmushi tayi ta girgiza masa kai suka tafi..

wani tafkeken farm house ta kaishi  na (lagos state government )ba abinda babu ciki,kaji ne,dabbobi ne ,shuke-shuke ne,tsuntsaye ne,kala kala a wurin ..

Wani farin ciki da jin dadi ta gani ya bayyana a fuskarsa,ya dinga ratsa cikin gonar yana bin kan dabbobin dabtsutsayen yana shuke-shuken dake wurin sun matukar burge shi, bai san lokacin da ya fara dariya shi daya ba. Irin abin da yake so yaga ya yi,ya kafa a rayuwar sa. Ga bishiyoyi,ga shuke-shuken ‘ya’yan itace kala daban -daban …

lumshe ido yayi ya ware hannun yana shakar iskar wurin yana jin yana ratsa shi,yana jin wani irin tsananin dadi a ransa irin wanda ya jima bai ji ba.

Zuwa tayi gabansa ta harde hannu tana kallonsa tana murmushi,tana jin dadin yadda ta ga tayi sanadin kawo farin ciki a rayuwar sa. Nan ta dinga jin wani irin farin ciki a ranta ,wannan dama shi je burinta a rayuwa ta ga tana sanya dariya da farin ciki a rayuwar mutane ,anan take samun nata farin cikin da nutsuwa da jin karfin gwiwar cigaba da rayuwa…….

sry nasan zaku iya samun mistake ko typng erro ,,wlh typing din dare nayi kuma ban kuma bi nayi editing ba kawai nayi posting,,wlh nagaji ne kuma burina kawai nima inga yau nasaku farin cikii  (kamar dr da patient dinta????????)

Tnks

Sumy luv????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

43

Kamshin turarenta yaji iska ta debo yana sauka kan fuskar sa yana shaka yana ratsa jiki da zuciyarsa,yana shiga yana ratsa shi. Soyayyar tace mai zafi da sanyi tare da dadin gaske yaji yana shiga yana kama zuciyarsa da dukkan ilahirin jikinsa yana ratsa shi tare da saukar masa ds wani irin farin ciki da ni’ima mai dadin gaske…..

“Alhamdullah”,Allah na gode maka.”

Ya bude ido yaci karo da fuskarta tana masa murmushi,shima ya hau mata murmushin  Suka kyalkyale da daria duka,tace. “Wow! In kayi dariya kana cikin farin ciki (u rilly look great)””.

Ya kalleta,”(thanks to u )Bahijja.”

Ta girgiza kai,”Mun godewa Allah,don haka Mr. Deeni daga yau kasan inda ka kama,kasan inda kasa gaba,(u belong here)…… Ta nuna masa gonar.

Ba gidan magani da allura ba,duk da likita kake amma kafi kyau da dacewa da nan gidan gonar,inda farin cikinka,jin dadinka da passion dinka yake,to me zaka jira? Ko ka nemi aiki anan ko kayi kokarin bude naka,duk wanda kakeso zaka iya””…

Yayi dariya,” Na gode da shawararki ,tabbas a nan passion dina yake ,(thank u so much)Bahijja . Daga yau din nan na miki alkawarin bude sabon rayuwa ,kuma zan fara yin wani abu me ma’ana da rayuwata insha Allah.

Amma ina so ki min wani alkawari, ki zama abokiyata mai ban shawara ,yayata kuma mai guiding dina…””

Tayi murmushi ,”Insha Allah ,Allah ya yi mana jagora duka”.

Ameen “Ya amsa tare da fadin .

“”Sannan zaki bani littafin nan na MISBAH ,kuma zaki zama ABOKIYAR RAYUWATA…””””

Ta dalla masa harara ,”Abokiyar rayuwarka kadai? Ka manta har ABOKIYAR MUTUWARKA ma zan zama ..”

Ya yi dariya ,”yauwa my Bahijja’”..

Wucewa tayi ta fita ta wuce mota ,har ta saba da halinsa na zolaya. Ya bita har ya shiga suka tafi yana zolayarta.

Har gida ta kaishi ta ajiyeshi,ba yadda bai yi ba ta shiga ta ki,ta ce ya gaida hajiya. Anan ya karbi numbern wayarta sukayi sallama.

Kai tsaya ya wuce falon mahaifinsa,anan ya same su duka har lukman kaninsa,yana dariya ya gaishe su. Kallo daya zaka masa kasan yana cike da tsantsar farin ciki.

Ya zauna kusa da mahaifinsa tare da kwantar da kansa a cinyarsa.

“Baba ka yafe mun”

Alhaji Umar ya dinga ji da ganin Deeni kamar a mafarki,sai da hawayen farin ciki ya zubo masa bayan shekara takwas zuwa tara Deeni ya fito daga kejin da ya shiga…

Mahaifinsa ya kalleshi,Deeni Alhamdulillah ,tsantsar farin cikin da nake ciki bnsan iyakarsa ba. Nima ka yafe mun.

Mama dai ta kasa jurewa sai da tayi kuka,farin ciki da jin dadin da suka tsinci kansu a ciki,sai godiyar Allah. A nan Deeni ya tabbatar musu da ba zai taba sake daga musu hankali ba.

“Zan yi biyayya a gare ku insha Allah””.

Alhaji ya kalleshi,ya ce,”Allah ya maka albarka Deeni,nima na muku alkawari dukkan ku ‘ya’yana ba zan sake shiga rayuwarku ba,kowa yayi abinda yakeso duk da nasan nayi latti duk kun gama karatu..

“”Baiyi latti ba Baba .”Deeni ya katsae shi.

Ko a yanzu zaka iya yin abinda nake so,ina fatan zaka taimake ni kasa mun albarka.”

Insha Allah Deeni sai inda karfina ya kare..””

Yace,”Wannan yarinya likita Bahijja Allah ya mata albarka ..

Mama ta kalli  Deeni ,”Zaka kaini jar gida insa mata albarka.

Yayi dariya ,”To mama ko yanzu ma in kin shirya”.

Tayi dariya ,*ba yanzu ba sai gobe ”

Alhaji yace,”Nma ba za a barni a baya ba””

Washegari bayan sallar isha Deeni ya tuka su zuwa asibiti wanda anan gidan Bahijja yake,suka yi tambaya don kuwa Deeni bai taba zuwa gidanta ba.

Sun samu baba andi ta ce bari ta shiga ciki ta mata magana,anan Deeni ya mike yana zagaye falon nata dabyadda ta tsara shi yana murmushi yana jin sonta na kara tasiri a zuciyarsa,soyayyar Bahijja na shigarsa yare da saka masa wani irin tsananin farin ciki da jin dadi.

Yana tafiya yana zagaye wurin har ya hango gurin da ta kebe mai kama da (libry)anan ya hango hotunanta da mijinta da danta suna rumgume da juna,ya zurawa hoton ido yana tuno Dr. Mislihu . Sai a lokacin ya fahimci mijinta ne.

Wani dan madaidaicin (diary)ya gani da biro a hade alamar bata jima da yin rubutu ciki ba,haka zuciyarsa ta dinga azalzalarsa ya bude ,yana kwadayin sanin komai game da Bahijja. Nan ya yi karfin halin budewa duk da yasan hakan ba dai dai bane.

Abu na farko da ya fara gani yaji zuciyarsa tayi mummunan tsinkewa shi ne,(To my dearest wife MISBAH).

“”MISBAH ? Ya maimaita a ransa ..

Bai bata lokaci ba yaci gana da karantawa,sai lokacin ya lura da diary din da marigayi mijunta ya rubuta mata ne,yana fada mata irin muhimmancinta da soyayyar da yake mata gami da yabonta na ayyukan kwarai da take,yana mata addu’a gami da sa mata albarka.

Nan ya rufe ido yana kokarin tuno inda yake ganinta da diary din nan mai kama da littafi,da lokacin da take zuwa gidansu wurinsa,da kuma asibiti,in tana zaune bata da komai takan dauko littafin tana karantawa …

Sannan wannan shine littafin da ta rike da sunan tana karanta masa sabon littafin MISBAH.

“Wato Bahijja ita ce MISBAH””. Ya maimata.

‘Author din da nake so tun ba yau ba ,Author din da na hada (special bond ) da ita tun lokacin da na fara karatun littafin ta a rayuwata,Bahijja abokiyata wacce take yanzu masoyiyata ita ce MISBAH na da na jima ina so ina kauna?  Wow ! Bahijja na ita ce MISBAH na ..””

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button