MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kaunarta yaji yana dada tsuma shi,yana ratsa shi..
**Ke din daban ce special ce tunda har kika iya min dabara ,ni kika mayar marar wayo ? Ni kika fooling,wato dama wannan labarin kirkirankika yi a lokacin shi yada na nemi lityafin nan sama da kasa na rasa,ashe dama yana boye ne a cikin kwakwalwarki. (I love ur smartness)ina sonki Bahijja ‘yar Baiwa,MISBAH na . Sai yanzu na fahimci labarin rayuwata da kikela yi kokarin hada min naji yana shiga ta,naji labarin ya tsaya mun a rai . Na so inji karshen sa ko zan samu in warware nawa matsalat..””
Ya yi murmushi yana kallon hotonta ,””labarin da kika fara ni zan karasa miki,ba ni kika fooling ba ? Jiya kiga yadda zan fooling dinki…””
Nan ya yi ta ganin takardunta a wurin daban-daban da irin article din da tayi ta rubutawa.
MISBAH na ‘yar baiwa ce ,Nsha Allah zan zama ABOKIN RAYUWAR ki da MUTUWARKI kamar yadda kika fada,zaki ga yadda zan kawo farin ciki da canji a rayuwarki”
Ya yi murmushi ya ce,””Yayata Bahijja,Abokiyata,masoyiyata MISBAH .””
Nan yasa hannu ya dauki littattafan da yake so,sannan ya dawo gun su mama ya samu Baba Andi ta gabatar musu da abin motsa baki,yasa hannu ya dauki apple yana ci yana lumshe ido ,yana jin kamshin Bahijja ko ta ina a gidan .
Baba Andi tace,”kuyi hakuri na samu ta fara sallah ne .””
Mama tayi murmushi ,””Bakomai”
bata rufe baki ba kuwa Bahijja ta fito da fara’arta lullube da hijab,tunda ta shigo falon idonsa ke binta,ya zurawa fuskarta ido me cike da kamala da annuri ,murmushin dake kan fuskarta ya kara haska fuskarta ,yaga ta masa wani irin kyau da kwarjini……
Wani irin SO me karfi yaji yana shigar sa,Son da bai taba tsammanin akwai irinsa ba ,ashe da wasa yake ba so ba,MISBAH ita ce so,ita ce SHAUKI. kallonta na kara masa son rayuwa,yana kara masa tsammani ,yana sa shi wani irin farin ciki da nishadi…………
he’s inlove again ????????????????????????????????????????????????????????????????
????????????????amma anya kuwa Deeni baya zurfafawa dayawa a soyayya ??
Shin Bahijja zata karbi Deeni kaninta a matsayin masoyi ???
wani hali Deeni zai kasance idan Bahijja taki amincewa a karo na biyu???
sai munji ra’ayoyinku…
taku har kullum……
SUMY LUV????????????
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
=================== GIDAN NOVELS ====================================
44
Yadda Deeni yaga tana gaisawa da su Mama da Baba suna ta hira cikin kaunar juna da kulawa ya kara masa jin dadi da nutsuwa,haka yake burin ganin matarsa da iyayen..
Bahijja ta mai (a kallonta kansa,ta lura ya tafi wata duniya. Biron dake hannunta ta jefa masa tana dariya ,ta ce.
‘”Abokina Deeni,wacce duniyar aka tafi??
Yayi mata murmushi,ya ce,”Duniyar abokiyata Bahijja,gidanki ya mun kyau ,ya birgeni ,musamman (libry)dinki,cike yake da irin littattafan da nake so””
Ta zaro ido tana kallon sa,”Kaji min yaro ,daga zuwa gidan mutane har kasan hanyar (libry)dinsu ??
Ya yi mata muryar tsokana ,yace,”Ba gidan mutane bane ,gidan Abokiyata fa Bahijja ne. Sannan kin manta lokacin da kike zuwa nawa dakin kina mun yadda kike so ? Yanzu lokaci na ne.”””
Tace,”” Gidanku gidanmu ne ,ko mama?
Mama ta girgiza kai,”kwarai “””.
Ta kalli Deeni tana masa gwalo,ta ce.
“Gidana kuwa gidana ne ni daya,Baba Andi daga yau in yazo kar ki bude masa kofa ..””Baba Andi tayi dariya tace,”Ni na isa in shiga tsakanin yaya da kaninta ?? Deeeni yayi dariya,ya ce ,”Yawwa Baba Andi, daga yau kin zama babbar abokiyata,zan shigo inyi yadda nake so gidan yayata..””
Bahijja tace,”In kuwa kayiwa yayarka barna zaka sha bulala.”
Dariya sukayi duka har da Alhaji,Mama ta kalleta tace.
” Allah ya miki albarka ‘yar nan ”
Ameen Maama.”ta fada kanta sunkuye.
Tace,”kuyi ta mna addu’a mama,kuna sa mana albarka,insha Allahu Allah zai taimake mu..
Deeni ya kalleta yana dariyar tsokana,zuciyarsa cike da sonta ,yace.
“Allah ya miki Albarka ‘yar nan ……
Ta hararebshi ,”Mama kinga yaron nan ya raina ni.”
Alhaji ya kalleta yana murmushi ,ya ce .
Zan baki bulala ki dinga zane shi.”
Suka yi dariya duka,tace,’Yauwa Baba,gara in fara zane shi don naga girman jikinsa na yaudararsa…
Deeni yace,”To wata ma tayi girman jijin mana
Mama tace,”Deeni naga alama nima zan fara maka bulalar..”
Nan suka yi ta dariya suna hira har wurin karfe tara sukayi niyyar tafiya,Bahijja ta raka su har mota. Ta lura da wani irin mayataccen kallo da Deeni yake mata,haka ta ganshi cikin tsananin farin ciki. Sai dai bata zurfafa tunani ba ta kau da abin a ranta amma ta rasa me yasa kallon yake yawan fado mata rai(????????????????????????)…
***** ***** ****
Deeni da iyayensa suka ziyarci su Shamsu tare da sauran dangi,Shamsu da Farida kam sunsha mamakin ganin yadda Deeni ya ware har abinci ya zauna suka ci tare da shi da Faridan da yaransu ana wasa da dariya..
Tun Farida najin wani iri ,tana takura har ta ware tana kallonsa tana mamakin ganinsa haka. Ya kuma nuna mata shi dan duniya ne ,ya dinga janta da hira,”Aunty Farida kaza ,Aunty kaza akayi.” Tun bata da niyyar sakewa har ta sake..
Deeni kuwa har cikin ransa ya gama da farida da tunaninta ko soyayyarta,a halin yanzu duniyarsa,farin cikinsa da shaukinsa yana ga Bahijja.
‘yan uwa da abokan arziki kowa ya yi murna da sabon canjin da aka samu daga Deeni. Farida ta masa murna sosai ,amma sai ta tsinci kanta a cikin wani bakon yanayi na rasa soyayyar Deeni da tayi,sai a lokacin ta kara fahimtar abinda yayi,addu’a tai tayi har ta samu saukin abin. Saboda ita har yanzu cikin kasan zuciyarta akwaii Deeni a binne ,sai dai zata ci gaba da jurewa da kuma rungumar rayuwarta da mijinta da ‘ya’yanta ,ba zata taba tono shi ba.
A cikun wannan lokacin Deeni da mahaifinsa suka yi ta shiga da fita da buge bugen neman makeken fili a kusa da asibitin Bahijja don ann ya cewa mahaifinsa yake so ya yi gidan gonarshi. Shi dai bai tambayeshi dalili ba,ya biye masa don yanzu duk abinda Deeni ke so shi ake masa,da sauri ma kuwa. Shakuwa da soyayya ta musamman ta shiga tsakaninsa da mahaifinsa,gaba daya Deeni ya dawo sabon mutum..
Abinka da masu gidan rana ,lokaci kankani aka gama ginawa Deeni gidan gonar sa,aka daukar masa ma’aikata masu taimaka masa da komai. Duk wani abinda yake bukata an sa masa ciki,a hankali wurin ya dinga habaka yana yiwa Deeni yadda yake so..
Irin farin ciki da jin dadin da ya tsinci kansa a wannan lokaci ba a magana ,yayin da ya sako Bahijja gaba da nasa salon tsokanar wanda ya samo. Wata number ya samu yana tura mata text message.
Tana zaune office dinta tana karance karance taji wayarta tayi kara alamar shigowar sako,ta dauka ta bude. Gabanta ne ya ba da rass!!
“MISBAH””
Shine abinda taga an rubuta.
Tayi bala’in rudewa saboda duk duniya mutum daya ne yasan ita ce MISBAH ,wanda yanzu baya duniyar.
Kafin ta gama fita daga wannan rikicin ta sake ganin an turo mata wani.
(I knw u re my MISBAH).
Mikewa tayi tana sake maimaita sakon a ranta,mamaki ya bayyana karara a duskarta,nan tayi saurin mai da amsa.
“Waye kai?(wrong number)
ya bata amsa da ,”In wrong number ne me yasa kika tambayeni ?
Nan tayi saurin kiran layin,amma sai taji a kashe ,tayi shuru tana tunanin duk wanda yayi abin nan yasan yadda take tunani,yasan zata kira ,to waye ne ? Ko da wasa bata taba kawo Deeni a zuciyarta ba,asali na ta kasa kawo kowa a ranta. Haka tayi aikin wurin da abin a ranta.