HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana sallama gidanta kuwa wani sakon ya shigo.

“Allah ya hice gajiyarki my MISBAH “”

Yanzun abin ya fara taba mata rai ,wa ce ko wane dan rainin wayon ne ?

Tayi tsaki ,zata wuce ciki taji muryarsa.

“Haba madam Bahijja ,wucewa haka ba kya duba gabanki ? Tun dazu nazo ina jiranki,awa na guda na samu Baba Andi itama har ta gaji ta tashi,amma ni ban gaji da jiranki ba. Haba abokiyata.”

Bahijja ta harare shi,”Gama cin abincin ka sha ruwa maza kaje gida kayi wanka ka kwanta kayi bacci,kana da aiki gobe..””

Ya yi saurin mikewa ya sha gabanta ,”Wa kike cewa yaro ? Wai an fada miki shekara talatin wasa ne ?

” Matsa ni kaban wuri,talatin din  har wata kayan gabas ce ? Akai na dai talatin dinka na komai bane..”

Har ta soma tafiya ya sake shan gabanta ya harde hannu tare da shan mur ,ya kafa mata idanunsa.

‘ Waye yaro ?

Muryarsa da irin kallon da yake mata duk suka rikitata ,ta rasa me yasa take jin shakkar sa. Nan dai ta dake ,murya na rawa ta ce.

“”Way…  …waye kake zarewa ido ? Wa zaka bawa tsoro ? Ni da waye a wurin ?

cikin muryar rada mai kashe jiki yace,”Yayata Bahijja da abokiyata Bahijja ,ita nake bawa tsoro ,kuma naga ta tsorata…

Gaba daya ta rikice ,taji jikinta na bari,da kyar ta iya daga kafa tayi ciki da sauri . Ya bita da kallon kauna yana murmushi,can ya jiyo muryarta tana cewa..

” Ka fita ka kira baba Andi ta rufe mana kofa,kuma karka sake zuwa mana gida da dare””

“”  zan zo ko yaushe nakeso,kuma in kin isa ki fito ki fuskance ni ki hana ni.

nan ta leko da kai ta ce,”Na fuskance ka,sai me ?

” ki kalli cikin idona in kin isa” “Naki din “ta fada tare da rufe kofar da karfi tasa key.

“”Wannan yaro ya zame min damuwa gurin aiki da gida duk bai kyale ni ba,sai na hada shi da mama”.

Tana cikin wanann mitar wani sako ya sake shigowa ….

” Ki tabbatar kin ci abunci kafin ki kwanta,karki kwana da yunwa MISBAH NA.

SUMY LUV????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

Kuyi hakuri da  abinda kuka samu,wlh nayi typing me yawa da safe ban san ya akayi ba akamun deletn….wlh saura kadan nayi kuka ,sabida yafi na koyaushe yawa..

 

45

Tsaki Bahijja tayi ta kashe wayarta takwanta a wurin ko kayan jikinta bata cire ba ta kwanta a kasa zuciyarta cike da tunani kala kala musamman na wanann sakonni dake shigo mata.

Can ta kau da tunanin ta soma tunanin yadda Deeni ya saki jiki da ita sosai,tayi zaton in ya warke a yadda ta sanshi da attitude zai fita harkarta ne amma sai wani sabon shakuwa ma da kara kusanci da ita yayi,lokaci guda sun zame mata kamar ‘yan uwa shi da mahaifansa da ‘yan uwansa. Tabba da haka kowani mara lafiya yake mata da duk kusan rabin kasar nan sun zama yan uwanta. Shi dai Deeni daban yake,mutumin kirki ne,mutumin kwarai.

Dariya tayi da ta tuna halayyarsa da yadda yake yawan nasara akanta.

Deeni kanina ,ina son sweet nature dinsa.

Ta yiwa kanta murmushi ,sannan tasa hannu ta dakko hoton Doctor Mislihu da danta kana kallo tana jin tsananin kewarsu.

“Allah ya jikanka,ya maka rahama masoyina. Muhammad dana Allah ya maka albarka ,ya albarkaci rayuwarka. Allah ya kare min kai a duk inda kake..

Hawaye ne ta dinga gangaro mata,ta tsinci kanta cikin kewa kamar yadda ta saba kowani dare,da hakan bacci ya dauke ta.

 

Haka Deeni yasa Bahijja a gaba da tura sako,ya hanata sakat. Wani lokacin sai ya zo gabanta sai ya tura mata,nan da nan zai ga ta rikice tayi wurgi da wayar har ya zamana tana shakkar kunna wayar,a dole take amfani da layin saboda shi ne layin da aka santa dashi ,ana iya nemanta.

Haushi ya kamata ,ga matsalar me matsa mata da text da bata san waye ba ,ga Deeni kusan sati guda bata ganshi ba ,ta masa waya bai dauka ba ,kuma bai kirata ba. Ta kira mama ta tabbatar mata lafiyar sa lau,aiki ne ya masa yawa.

Tsaki tayi ta kasa kulla komai,can ta yanke hukuncin leka shi a ma’aikarsa ,tunda ta shiga ta hango shi yana aiki bai zauna ba yana ta faman kaiwa da kawowa da ma’aikatansa,ya leka wannan fannin ya leka wancan . Can ra ga ya hau tractor yana zaga cikin farm din nasa,ta sa masa ido tana kallonsa tana murmushi..

Nan take ta rsinci kanta cikin nishadi,tana jin dadin ganinsa haka tana matukar sha’awar halinsa,wasa da dariya da maaikatansa gami da mutunta su,haka tsakaninsa da dabbobi,kaji da sauran tsuntsaye tamkar abokan sa.

Harde hannu tayi tana kallonsa kamar t.v. can ta ga wata yarinya matashiya ta zo tana kiran sa,ganinta yasa ya sauko daga kan tractor din ya zo yana kallonta yana daeiya suna magana,haka ya bata muhimmanci sosai. Haka kawai taji ranta ya baci,ta kasa ci gaba da jure kallonsu.

Har ta juya zata tafi sai taji muryarsa,”Har abokiyar tawa zata tafi bamu gaisa ba?

Ta kau da kai ,”Dole ne in gaisa da kai ?

Gaisuwa ba dole bace amma ganina dole ne ”

Ta harare shi ,”Ta yaya ya zama dole?

Tabbas nasan tunda har kika zo gidan gonata ba kinzo yawan shan iska bame”

” Kwarai “. Ta bashi amsa.

“kaji nazo gani da dabbobi.”

To ai baki gansu ba zaki tafi.

” Na fasa ”

Ta fada a hasale tana kallon yarinyar alamar tana tsaye tana jiransa ne.

” kaje kaji da bakuwarka ”

Ya yi murmushi ,kar ki damu da bakuwa ta,wannan special ce ba rabuwa za muyi yanzu ba,gara in gama da ke yanzu in koma.

“Yanzu ma ka gama dani,sai ka tafi.

“Bashi yiwuwa kizo ki tafi baki shiga office kinsha ruwa ba”

Ba shi nazo sha ba””ta bashi amsa.

“Na sani amma za kisha ”

Dura mun zaka yi ?

“A’a da hannunki””

” wai me kakeji da shi? Ta fada a hasale. “Ban ji ds komai sai gidan  gona ta da special bakuwata”

Hawaye ta ji ya ciko mata ido,jikinta yayisanyi tace,

Deeni sati guds ba waya ba ziyara? Na kira baka dauka ba ,ko special bakuwar ce ta hana ka ?

Yayi mata murmushin dake fadar mata da gaba ,yace

Ki yi hakuri aiki ne ya mun yawa da lokaci.

Deeni ba zaka iya samun lokaci komai kankantar sa ba mu gaisa?

Tana maganar saura kiris tayi kuka glhar ya lura da hakn yayi saurin kau da kai don ya bata damar zubar da hawayen.

Ya ce,MEYE DANGANTAKARMU? Bahijja kina naki duniyar ina tawa ,kina farin ciki da aikinki ina yi da nawa,idan halin haduwa ya zo sai mu hadu. Yanzu ba da bane,dukkan mu muna da abinyi,saboda me zamu dinga bata lokacin mu ?

” Haka me “.Ta fada murya kasa kasa .

Kayi hakuri,sai anjima.

Tajuya jiki ba kwari da kyar take iya daga kafarta .

“Bahijja”

Ya kirata amma bata juyo ba valle ta tsaya. Ya so ya bita amma sai ya fasa ,ya nemi wuri ya zauna ya fada wata duniyar tunaninta yana jin wani irin shauki mai karkin gaske game da ita yana ratsa shi,idonshi ya kada yayi ja yayin da gugiwar kaunarta ta dinga tashi a zuciyar sa…

Sumy luv ????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by  SUMAYYA SA’AD❤❤

46

Bahijja ta koma office amma ta kasa zaune da tsayee,gaba daya ta kasa samun nutsuwar yin aiki,dole haka ta tattara ta koma goda. Nan ma tayi kokarin yin rubuce rubucen ta amma hakan ya gagara…

Duniyar internet ta shiga ko zata samu abin bincikawa shima ta kasa,nan ta dauko liyyafi amma karatun ya gagara,ranta yayi mummunan baci,ta rasa me ke mata fadi…

Wannan shi ne lokaci na farko da haka ya faru da ita a tarihin rayuwarta,damuwa da bacin rai komai yawan sa da karfinsa ba ya hanata sukuni har ta kasa yin komai,ta kasa jin dadin komai a rayuwarta. Haka ta kasance har yamma lis ita daya a gida,don baba andi ma bata nan taje gai da  yan uwanta zata yi kwana biyu..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button