MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kicin ya shiga amma ta rasa abinyi,ta fitofalon. Tana nn tsaye ta hango kanta tsaye a gaban tafkeken madubin dake manne a bangon falon.
A hankali ta matsa tana kallon kanta da yanayin ta,gaba daya ta canja,ta birkice,ba nutsiwa ko kadan a tare da ita.
” Meye haka Bahijja ?
Ta tambayi kanta.
“Me ke damunki ? Me ya hanaki sukuni?
Can karkashin zuciyarta tasan amsar ,amma sai ta ki amincewa wanda ita kanta tasan kin amincewa abinda kasan ba gaskia bane yana matukar wahalar da zuciya tare da ruhi da jikin mutum gaba daya.
Idanunta suka kada sukayi ja,tausayin kanta ya kamata. A hankali ta sa hannu ta zame gyalen da ta daure kanta dashi,ta baza gashin kanta tana shafa fuskarta da gashin ta,idanunta suka kada sukayi jajawur,ta tsinci kanta cikintsananin kewa . Sai a wannan lokacin ta tuna cewa eh ita mace ce fa mai rauni,abinda ta manta da shi duka yau ta tuna,tana bukatar a kula da ita ,tana bukatar soyayya ,tana bukatar wani ya sota,ya kuta da ita,ya kawo karshen wannan emptiness din a rayuwarta.
Bata ankara ba sai hawaye taji yana zubo mata da karfin gaske,har bakinta na bari. Ta sa hannu duka biyu ta rufe fuska tana kuka .
Ya sake kallon kanta ,”Bahijja ya kike ? Ya kamanninki kaye ? Ke kyakkyawa ce ko mummuna ?
“Ya kamannina yake ban taba sani ba,kullum dai mijina ya kan kalle ni ya yabani da kyauna,amma ni ban taba tsayawa na kula ba””
Shin me yasa nake son kula da kamannina na yau? Shin wa zai fada min ya nake? Ya kamannina suke?
“”Bahijja u re a beautiful woman,””””
Taji muryar Deeni tsaye a bayanta.
Ras !!!Gabanta ya fadi,tuni tayi wani mugun rudewa,tayi saurin jan gyalen ta lullubu,ta kasa ce masa komai.
“”Gidanki ne amma zan miki tayin gurin zama””
Ta rasa me yasa yake iya controlling dinta,bata iya musa mishi ko tayi niyya duk kuwa zafinta da jin ta isa.
Wuri ta nema a kujersr falon ta zauna,ta kau da kai.
Ya matsa gabanta ya kafa mata ido,”Bahijja meye damuwarki?
“”Me yasa zan fada maka damuwata?
“Hakan na nufin cewa akwai damuwar kenan ? Ina son sani…””
Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai.
“Bahijja “”ya sake kiran sunanta.
A duk lokacin da ya kira sunanta tana jin wani abu me sanyi da dadi yana ratsa ta har cikin zuciyarta da kwakwalwarta,yana kashe mata jiki.
Lumshe ido tayi tana jin wani abu me karfi game dashi..
Ya cigaba ,”Bahijja ninda ke duk muna cikin kuncin zuciya da shauki,bambanci shi ne kawai naki ya fito nawa kuma na boye shi a zuciyata,saboda bana son bayyana shi har sai na fahimci meye a zuciyarki.
Kuncin da kika shiga yanzu ni na shige shi na tsawon lokaci,ni kadai nasan ta yaya na rayu da wannan shaukin ..””
Wayar sa ya ciro ya daddanna a gabanta ,yayin da tana ji nata wayar yayi kara. Shi ya dauka ya mika mata,gaba daya jikinta ba kwari maganganunsa kawai ke mata yawo a jiki dabjijiyarta,da kyar ta iya karba ta bude sakon tana karantawa,ya sa mata ido yana karanta mata abinda sakon yace.
” I love you MISBAH”
Bugun zuciyarta taji ya tsananta ,ya sake maimaitawa yana kallon cikin idonta.
“Ina son ki MISBAH ”
Nan tayi saurin sunkuyar da kai ,gaba daya taji ta rufe ,ta susuce,bakinta na bari,ta rasa abin fadi,ta kasa zaune da tsaye ,gashi ya tsareta da ido.
“” Na san abokiyata itace MISBAHna tun randa na fara zuwa gidan nan , na miki abinda kika koya mun ne na kirkirar sabon labarin MISBAH a lokacin,tunda kin kasa karasawa ni zan ci gaba ,sauran sai mu karasa tare. Ina fatan za ki bani hadin kai mu karasa tare .
Bahijja ina matukar sonki,so na hakika,zan kawo farin ciki ratuwarki,zan kula da ke,zan shagwabaki ,dukkan damuwarki zai zama nawa,zan dauki nauyin sa ki farin ciki a rayuwa…
Nasan nayi soyayya mai zafi a baya ,sai dai ina so ki sani dangantaka ta da kaunata da ke ya jima sosai,tun kafin in san ke wace . Na jima da kaunarki tun kafin in san ke mace ce ko namiji,ta hanyar rubutunki.
Bayan haduwa ta dake,kin taimake ni na manta da abin da ya faru a baya,wanda soyayyarki ce ta mantar dani. Yanayin rayuwarki abar so ce,abar koyi ne,sannan kin fahimtar dani abubuwa da yawa da baiwarki,wanda karo na biyu na sake fadawa sonki ba don komai ba sai wannan halayyar taki wanda ita na jima ina mafarki da burin gani a wurin mata ta (how u cope ur loneliness)ya birgeni ,ta kara min ganin ganin girmanki ,sannan lokaci guda na zo na fahimci MISBAH na ita ce Bahijja na ,sai abin ya min bibbiyu.
Halayyyar Misbah da Bahijja shi ya haukata zuciyata da sonta har na manta da na taba wata soyayya a rayuwata,duk abinda Misbah tayi yana burge ni,yana min dadi,musamman zuciyarta da boye kanta da tayi wa duniyata watsa iliminta da baiwarta ga alumma suna amfana.
Bayan nan Misbah kina da kyan da ya shiga zuciyata ya zauna,murmushinki,muryarki mai dadin sauraro,wannan bakin dake min mita da surutu kullum,wannan idanun masu kashe min jiki ko kirarki ,iya takunki ko nutsuwarki me hanani sukuni.
Bahijja ina sonki ,kina sona ??
Gaba data ya gama tsuma da kalaman sa,ya kashe mata dukkan gabban jikinta ,sonshi ne mai tsananin gaske take jin yana huda dukkan ilahirin jikinta. Da kyar ta iya bude baki murya kasa kasa tace.
” Kasan me kake fadi kuwa ? Ni na ce maka ina sonka?
Ya karya kai yana kokarin su hada ido amma taki ,yace.
“Ba ke kika ce ba,ni naga haka,ni naji a jikina ,lokacin da hankalinki ya tashi da na daina zuwa wurinki na daina daukar wayarki,lokacin da hankalinki ya tashi da kika ganni da ma’aikaciyata. Wannan abin shi ne so Bahijja ,wannan feelings din da muke ji shi je so. Ko ki so ko ki qi mun riga da mun shirya duniyarmu nida ke tun tuni,mun tsara rayuwar mu ba tare da mun fahimci haka ba sai yanzu. Ina fada miki gaskiyar da kin kini sani ne …””
Ta mike da sauri,”karka manta kai kanina ne,har yanzu ni yayarka ce,wacce na taba aure har ma na haifi yaro. Kai saurayi ne,dan gata ne,dan asali ne. Kar ka manta ni marainiya ce da bani da asali.
“” Martabarki da darajarki ya wuce haka,ke abar so ce Bahijja,ina son sani wanne ne daya kike magana akai,sona ne bakya yi ko kuma wannan bayanan zai hana ki aure na ? Uwa ta gari nake nemawa ‘ya’yana na gani a tare da ke,mace saliha nake nema na gani a tare da ke ,don haks ki bar wannan zancen..
Ni ne me aurenki ba mutanen duniya ba,ni zan zauna da ke na miki alkawarin soyayyarki ba zata canja ba,haka zan cigaba da daraja ki da mutunta ki. Ke abu ce mai matukar muhimmanci da daraja a wuri na,kin wuce wasa””
Bata furta komai ba duk da alamar maganganunsansun ratsa ta,wucewa tayi library dinta hankalinta a tashe ta rasa inda zata sa kanta da soyayyar Deeni da ke azalzalar zuciya da ruhinta. Ta dauko wannan diary din da kullum ta rsinci kanta cikin kewa da rudani yake bata kwanciyar hankali in ta bide ta karanta,twyi ta kokarin budewa page by page amma ta kasa karanta komai,sai hawaye da ya cika mata idanu . Bata ganin komai haka ta dinga bide shi da sauri da sauri.
Ya biyota ya sa hannu ya karbi diary din.
“”Duk da abu ne mai muhimmanci a gareki Bahijja ni yana kona min zuciya ,ina kishi da shi,kishin gaske da ba na wasa ba nake yi da diary dinki.
Kiyi hakuri ina jin wani tashin hankali,Bahijja ina tare da tsoron rasa ki,duk da una da tabbacin kina sona,ina tsoran kar wannan diary din da dalilan da kika kirkiro dazu marasa tushe su sa na rasa ki..