HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bahijja da can na yi hakuri amma yanzu ban san ta yaya zan fara wanann hakuri ba ,saboda abinda nakeji yanzu da can ban ji rabinsa ba .

Bahijja ni masoyinki me,me yasa zaki hana ruhinki abinda yake bege? Me yasa za ki cutar da mu ki kuntatawa zuciuar mu?

Muryarta na rawa tana kuka ,ta ce.

” Deeni saboda ina tsoro. Ina fargaba da tsoron son da nake maka,so ne mai yawan gaske ,son da yafi karfina,son da ya tilasta mini mika wuya ga soyayyarka,so mai radadi da ciwon gaske. Ina tsoro Deeni idan duniya ta raba ni da kai fa ? Ba zan iya wata rayuwar jin dadi ko sukuni ba tare da kai ba . Ina tsoron idan na bata makafa na ki aurenka saboda wasu dalilai da nake ganin zasu iya hana mu kasancewa tare ? Deeni shekaru uku na baka kai saurayi ne,ni bazawara ce,iyauenka ma ba zasu amince ba,nima in nayi haka ban maka adalci ba . Budurwa ya kamata ka nema ka aura ku more rayuwarku tare “”

“”Bana son budurwar,ke nake so. Bahijja ke nake so ,ko shekara nawa kika bani ke nake so ki zama abokiyar rayuwata. Iyayena ba ruwansu da aurena,wacce nake so ita zan aura,kuma zanyi alfahari da auren mace irinki.”

” Deeni ina tsoro”

Ta fada cikin murya dishasshiya.

Ina tsoro Deeni,so na kake ko kuma ina cire maka keawar Farida ne ? Ina tsoron wataran kaji kana bukatar auren budurwa i dont want to rubish myself wato bam son wulakanta kaina,bana so ka aureni saboda ka rasa Farida ne “..

“Ba haka bane Bahijja ,ke kika ja hannuna kika sa ni mancewa da Farida da soyayyarta”

“Wanann gaskia ne,amma soyayyar da nake miki na faara ta ne lokacun da soyayyar Farida ta kare a zuciyata,ki yarda dani ba Farisa a zuciyata ko kadan..

Farida matar wani ce,uwar wasu ce,na shafeta a babin rayuwata,SHAUKI NA YA SAUYA tun tuni,idan kika rabu dani akan haka ba ki min adalci ba,kuma zaki kuntata rayuwata,kyautar da kika mun na farin ciki a rayuwata za ki kwace shi. In kika yi haka za ki kuntata mana duka..

Ki tuna kece me fadakar da mutane akan wanann matsalar,yanzu kuma da yazo kanki sai ki nemi kauce masa ? Bahijja ina sonki,kina sona?

Girgiza masa kai tayi alamar eh hawaye na zuba,ta kwantar da kai tana kallonsa tana jin sonshi kamar zai hallaka ta,wani so da bata taba sanin akwai irinsa ba. ..

Ra ce,”Ina sonka Deeni so na sosai,ina kishinka,ba zan jure ba nan gaba in ka auro wata,saboda wani na kasu ko gazawa a tare da ni,Deeni bakin ciki zai kasheni a wannan ranar..”

Durkusawa yayi a gabanta yace …

“”zan miki alkawari yau,ina kin yarda dani?

Ta girgiza masa kai.

“Na baki kyautar kaina ke kadai,ba zan taba auren wata wai don saboda una bukatar budurwa ko don kina bazawara ba,idan na same ki MISBAH bana bukatar wata mace..””

Ya jawo diary din,”Gashi a rubuce ,ni Deeni mallakin Bahijja ne ita daya kawai????????????????????????????????????????????????………………

Gaskia yau na rubutu,,sai bayan sati daya nida kuma yin posting????????????ina jin wata ce tamun baki ,na dingi rubutu kamar an aiko ni wlh….

SUMY LUV????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by  SUMAYYA SA’AD❤❤

47

Kallon shi take tana jin wani nutsuwa a ranta,yadda dai Deeni ta amince masa tasan mutum ne da yake yin abinda yace,haka soyayyar sa ba karya ba yaudara,mutum ne mai gaskia da nagarta.

Tayi masa murmushi ,”Deeni ,ba sai ka rubuta ba,na yarda da kai,nima wanann halayyar taka ita taja hankalina gareka har na saki jiki da kai muka shaku. Sai dai nima zan rubuta maka na amince maka Deeni ka auri ko wacce irin mace a duniya in kana so,amma banda mutum daya FARIDA wacce nasan ka daina sonta,kuma matar aire ce. Amma ita ce mave daya da nake kishi a duniya,nake jin zafin kishinta a raina ,saboda nasan irin soyayyar da ka mata ba na wasa bane. Idan kuwa kaddara yasa ka aureta to duk hukuncin da na yanke zaka amince da shi..”

Ya yi murmushi,”Bahijja na haramtawa kai farida tun lokacin da ta zama matar wani,ba ciwon sonta na yiwa jinya ba sai ciwon Cin amanar da suka min. Amma duk da haka don ki samu kwanciyar hankali na amince.

Tayi masa murmushi me cike da kauna tana masa kallon so ,ta ce,

Deeni komai kake so matarka ta maka zan maka shi a rayuwa duk dadinsa ko wuyar sa “”

” Ina da yakini akan haka Bahijja,kuma nima zan miki duk wani abu da mijin kwarai ,uba na gari ga ‘ya’yanki MISBAHna,Abokiyata,matata.”

Dariya sukayi duka,sun jima suna hira sannan sukai sallama da kyar kamar ba zasu rabu ba.

 

Soyayya mai tsafta da tsananin shakuwa ya kullu tsakanin Deeni da MISBAH,dukkan su suna son juna sosai so mai ban mamaki,dukkunsu kowa na aikin sa,sai dai wanann bai hana su bawa juna lokaci daga gidan gonar Deeni zuwa asibitin Misbah ba,nisan sa bai wuce tafiyar kafa ba.

Haka wata rana Deeni zai bat abinda yake ya je wurin Misbah yana kallonta daga nesa ko da bata sani ba baya gajiya da kallon ta,haka kullum sonta karuwa yake a ransa. Tana masa wani irin kwarjini,ya dinga jin sonta yana tsuma shi,yana godewa Allah da ya hada shi da MISBAH ,yana godiya da wannan shauki nata da yaje ji,fatansa da burinsa Allah ya bashi ‘ya kamar MISBAH……

Ta bangaren Bahijja lokaci gida Deeni ya canja rayuwarta,ba ta taba zato ko tsammanizata tsinci kanta a wannan sabuwar rayuwar ba. Wani lokaci inta tuna irin soyayyar da take yiwa Deeni hankalinta na tashi saboda nata tsoron kar wani ya shiga tsakaninta da Deeni,don kuwa tasan tabbas bazata iya rayuwa ba Deeni ba. Don haka kullum tasa goshinta a kasa tayi sujjada sai ta roki Allah da ya mallaka mata Deeni matsayin abokin rayuwa ,ya mallaka mata deeni da zuciyar sa.

Zaune take a office dinta idonta rufe ta tafi wani duniya tana hango rayuwar da za suyi da Deeni,tana jin son shi na tsuma ta. A lokacin ya shigo ya harde hannu a kirji yana kallonta yana murmushi,yana jin wani irin dadi a ransa.

Kamshin turaren sa mai karfi da dadin gaske ya dawo da ita hayyacinta,ta bude ido ta ci karo da fuskar sa yana mata wannan murmushin nasa da take so fiye da komai a rayuwa…

Itama murmushin ta masa ta zuba masa nata many manyan idanun ,ta ce…

“Har sakon zuciyar nawa ya isa gare ka ?

Ya fadada murmushinsa,yace ,”Wannan idanu suna kasheni da yawa ,suna tsumani ,suna gigita ni.”

Nan ta sake lumshe masa su ta kuma bude su,sai da wani abu yaji ya tsirke shi har tsakar kanshi,yaji wani irin tsananin kaunarta da sha’awarta mai karfi yana shigarsa. Zai yi magana yaji muryarsa na shakewa,da kyar ya iya furta maganar…

Bahijja lokaci yayi da zamuci moriyar soyayyarmu,Bahijja ina bukatarki kusa dani,ba zan iya jure yin nesa da ke ba. Ina zaune yanzu fitinar sonki ya hana ni sakat ,na rasa sukuni ,na rasa inda zan sa kaina ..

Mayiwa baba. Waya nace masa Baba zan yi aure ,ya ce in kawo duk mayar da nakr so a duniya zai aura min ita,na ce masa na samu mata,na samu uwar ‘ya’yana ,Doctor Bahijja,Abokiyata kuma likita ta. Ya taya ni murna ,ya min alkwarin mallaka myn abinda nake so ko menene shi indai bai fi karfinsa ba.

Na ce masa bana son komai sai Bahijja ‘yarsa ce,shi babanta ne,’yarsa nake so ya aura min. Na masa alkawarin rike masa ita da amana,don haka yau mamanki da babanki zasu tambayeki wa kikeso? Ina fata zaki fito musu da gwaninki..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button