HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kalamansa sun ratsata,kuma sun mata dadin gaske,wanda bata san yaishe ta fara hawaye ba. Tun tana ‘yar karama take buri da sha’awar ta ga soyayyar uwa da uba,ta ga kauna da gata daga iyaye kamar kwacce yarinya ,amma ta san wannan burin nata ba zai taba cika ba. Muslihu ya so ya cika mata wannan burin ,sai dai hakan bai samu ba…

Bata san yaushe ta kifa kanta bisa hannayensa ba tana kuka..

“” Deeni ka gama min komai a rayuwa”””

“”Burina kenan Bahijja in faranta miki,inga na cika kowanne irin buri naki karami ko babba,duk da ke din ba mai buri bace.”

“”Burina guda in mallaki Deeni da zuciyarsa ”

Yayi mata murmushi,”Burinki ya cika my dear,ina jin dadin yadda kike sona Bahijja ,yadda kike nuna damuwarki da kulawarki a gareni.. Ina bukatar wannan har karshen rayuwarta..””

” kasamu Deeni,soyayyata da kulawata naka ne”

Yayi murmushi ,”Nagode ,anjima Mama zata zo ta tafi da diyarta gida don mata shirye-shiryen aure,saura kadan Abokiyata ta zama amaryata..””

Murmushi tayi tare da boye fuska saboda kinya ,musamman da ta ga irin kallon da yake mata…….

****        ****      ****

Da yamma Mama ta zo ta tafi da Bahijja tare da Baba Andi can gidansu Deeni,duk da tana jin wani iri da nauyin Mama amma ta daure sabodaDeeni..

Mama ta lura da haka,don haka tayi kokarin kawar mata da nauyin da take ji,ta ce.

“Bahijja ke diyata ce,soyayyar da kike wa Deeni shima yake miki ya sani sonki da kaunarki kamar ‘yata. Ina godiya ga Allah da ya kawo ki rayuwar Deeni,don haka saki jikinki nan gidanku ne,zan miki duk wani abinda uwa zata yiwa diyarta ko shakar haka kar kiyi..””

Alhaji ya shigo yana jinsu ,shima ya matso ya ce.

Haka zan miki duk abinda amahifi zai yiwa ‘yarsa Nsha Allah””

“” Na gode Baba ”

Ta fada kai sunkuye yayin da taji hawaye na kokarin ciko idonta,wani feelings ne da bata taba jin irinsa ba,wani irin farin ciki na daban taji yana ratsa ta..

Allah abin godiya ,Allah mai kyauta da kari,ya bata miji da iyaye lokacin da bata zata ba balle tsammami….

Alhaji ya zauna gefen Mama ,ya ce,”Bahijja wane lokaci kika ga ya dace mu tsaida ranar aurenku?

Kanta sunkuye tace,”Baba ai ku iyayena ne,duk ranar da kuka ga ya dace ku ka tsayar dai dai ne..” Alhaji yace ,”To Allah ya miki albarka,ina so zan hada airen ku tare da lukman ,shima ya samu matar sa,sai mu hada muyi nan da sati biyu masu zuwa. In mun hada ku mun hutar da ‘yan uwa masu zuwa daga nesa sau biyu,tunda mun shirya sai mu hada””

To Baba ,tafada kai sunkuye.

“To Allah ya miki albarka.”

Nan ya mike ya fice,mama ta kalleta ta ce,

“To diyata zata zama amarya sai an bawa asibiti hutu ko saboda a bawa jiki hutu da nutsuwa””

Tsananin kunya yasa Bahijja kife kai,Mama na dariya ta ce.

“Na fada miki ni mahaifiyarki ce..”

Deeni dake tsaye yana kallon su ya tsinci kansa cikin wani irin tsananin farin ciki da jin dadi ,son mahaifan sa da kaunatsu yaji yana kara kardi a zuciyarsa.

“”Zan mallaki Misbah na nan da sati biyu Nsha Allah.”

A sati biyun nan mama tayi hayar masu gyaran amarya na musamman suka sa Bahijja gaba da gyara baji ba gani..

Mama ta fahimci nauyinta da Bahijja ke ji,wanann yasa ta damkata a hannun masu gyara da kuma aminiyarta Haj. Amina da tazo bikin da kanwarta…

Ya zame mata dole tayiwa matar Deeni gyara,Deeni gudan zuciyarta ne,zata iya komai don farin vikinsa,tunda Bahijja ce farin cikin Deeni ba zata yi wasa da ita ba…

Lokaci guda Bahijja ta canja,rayi wani irin kyau da haske me ban mamaki ,ta dawo tamkar wata Balarabita,duk inda ta wulga sai kaga tamkar anyi walkiya saboda tsabar haske da kyau da daukar ido da take …

Deeni ya kasa daga ido akanta duk inda tabi yana binta da idanunsa,yana jin alfahari da samun mace irinta. Tabbas Bahijja ta ishe shi har iya karshen rayuwarsa,bashi da bukatar wata mace ……

Ana saira kwana uku biki ‘yan uwa da abokan arziki suka cika gidan wanda musamman Alhaji ya tura ticket na jirgi wa mutanen gombe da kaduna don zuwa bikin dan gatansa.

Daya bangaren na gidan aka warewa baki,yayin da bangaren su Hajiya sai aminiyarta da kanwarta tare da su farida da mahaifiuarta.

Dakin Deeni shi ua koma dakin Bahijja shi kuma ya koma gidansa na farm house sai dai kullum yana makale tsakanin idonsa kan Bahijja ,bai iya jure rashinta ko na kankanin lokaci…

Bahijja ta kasa gasgatawa kanta sabuwar duniyar da ta tsinci kanta,gata da kauna da take gani gun mahaifiyar Deeni da ‘yan uwansa kadai ya isheta farin ciki,ballantaan kuma uwa uba Deeni..

 

Bayan sallar juma’a jama’a  da dama suka shaida daurin aurwn Deeni da Bahijja ,aure yayi albarka,dumbin jama’a ne suka cika a daurin auren. Bayan nasu aka daura na lukman da Amaryarsa Abida,duk a masallacin juma’ar unguwarsu aka daura…

Bayan daurin aure Mama ta shirya walima ta musamman ,abinci ba irin kalar da babu tun daga gargajiya har turawa. Wajen ya tsaru soaai,an gayyaci malamai mata masana da kuma ‘yan uwa da kowa in ya ci abinci ya tofa albarkacin bakinsa…..

Ina kuke FANS din Dr Deeni Da Dr Bahijja ????????????????ranar da kuketa jira yau gata ta zo…….

SUMY LUV????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by  SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by  SUMAYYA SA’AD❤❤

48

Haka a wajen Alhaji ya shirya nasa da maza abokai da yan uwa a waje,kowa ya ga Deeni wannan rana yasan yana cikin tsananin farin ciki. Wannan ya kara kayatar da kyan fuskar sa.

 

Cikin gida a daki Bahijja  ta sha kwalliya da gayu sosai,duk da shiga mai sauki tayi,doguwar riga mai tsadar gaske ta sa wanda Mama tayi mata order daga Dubai. Blue ce ammata kwalliya mai sauki da fararen duwatsu,ya matukar karbar fatarta mai haske ,haka ya dad fito da kwalliya fuskarta. Ta tufke gashinta baki mai tsayi da sheki tare da lulluba gyalen rigar ,ta sa cover shoe masu tsadar gaske da ya yis shige da irin dressing dinta,ta sa bracelet mai saukin kwalliya tare da zobuna guda biyu wanda suka yi matukar kayatar da dogayen yatsunta.

Bahijja macece doguwa mai kyakkyawar kira,shigar da tayi tai matukar kyau da bata taba ganin tayi ba ,sai kamshi take.

Mama ta shigo ta ganta ita kanta tayi bala’in mata kyau,ta dinga ganin duk yawan taron nan ba kamar surukarta Bahijja ,tabbas ta amsa sunanta matar Deeni.

Tayi murmushi,”Tabbas diyata tayi kyau”

Tace,”Bari inje zan turo wacce zata zo ku tafi tare wurin walimar,duk an gama taruwa””

Ita dai Bahijja kanta sunkuye har mama ta fita,shuru taji gidan yayi alamar duk an fits wurin walima. Tana nan zaune shiru zuciyarta cike da tunani kala kala taji motsin shogowa. Kamshin turarensa ya tabbatar mata da Deeni ne ya shigo dakin,nan tayi saurin daga kai suka yi ido biyu,yana mata wannan  murmushin..

Ya zuba mata idanu,itama ta kasa dauke idonta a kansa,yayi mata kyau sosai. Sanye yake da blue shadda kalar nata kayan ya sha aiki,shigar ta matukar masa kyau. Hular da ya kafa a kansa ta kara fiddo da kyan fuskarsa,gashin kansa kwance irin na fulani sak,ga sajen da ya karawa fuskarsa kwarjini da annuri…

Ji tayi tamkar ta je ta fada kirjinsa ta kwanta,amma sai ta kasa saboda kunya duk da yana mijinta. Shi yasa hannu ya jawo hannunta yana wasa da ‘yan yatsunta,tsigar jikinta taji tana tashi tana jin sonsa da shaukinsa yana ratsa jijiyoyinta,yana bin jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button