MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

” Haba MISBAH na ,ya zaki kawar min da fuska,amaryata ki tuna fa ke halal dina ce yanzu,baki san irin jin dadi da tsananin farin ciki da fuskarki ke sauke mini bane da baki kawar da kai gare ni ba . A yau sai naji soyayyarki ta zama sabuwa ,ta zama danya sharaf a zuciyata. Toho gareni,please Bahijja ko zan samu nutsuwa..”
A hankali cikin nutsuwa ta matso gare shi ya jawota jikinsa tare da bata kyakkyawar runguma,tuni ta bace a cikin jikinsa,suna manne da juna tare da jin irin son juna da sha’awar juna..
Cikin muryar rada yake mata wasu irin kalaman soyayya masu ta da hankali da tsuma zuciya da ruhinta.
Nagode Bahijja da soyayyarki,wannan shi ne (the most beatiful moment of my life)..
Rufe ido tayi jin kalaman sa na ratsa ruhinta,tana shakar kamshin sonta tare da fadin..”Deeni ina sonka ,kai nawa ne ni daya,mallakina ni daya..”
Haka ne Bahijja ni naki ne ke daya kamar yadda kike ke tawa ce ni daya,bana taba hada ki da kowacce mace a duniya,haka ba zan taba hada soyayyarki da kowa ba””
Sun jima a cikin wannan halin na tsananin shauku da son juna..
A hankali ta turo kofat tayi sallama amma shuru,hakan yasa ta kutsa kai,Farida kenn..
Gabanta yayi mummunan faduwa ,ya dinga bugawa da karfi ganin Deeni da Bahijja a hakan ya mummunan daga hankalinta.
Wani irin masifaffen kishi taji yana turniketa,masifaffen kyan da ta ga sunyi da Deeni da Bahijja ya razana ta tamkar dama an halicce su don juna ne. Tsohuwar soyayyar sa taji ta taso mata ta kasa gani da jure soyayyar da taga Deeni yana yiwa Bahijja wanda ita duk tsananin soyayyar da suka yi a baya ta dinga gani kamar wancan soyayyar wasa ce..
”Ya za’ayi Deeni yaso wata mace a duniya fiye da ita? Ya za ayi Deeni ya ci amanar kauna? (Readers kuji fa karfin ) Na zata Deeni zai yi aure ne ba don soyayya ba sai don raya sunnah kamar yadda nayi,ya za’ayi Deeni yaso wata fiye da ni ? Har yau ban taba son wani fiye da shi ba ,duk da nayi aure na zama uwa amma soyayyarsa bai taba barin zuciyata ba ko na second daya. Ya zanyi in rayu da wannan bakun ciki da bacin ran da na gani yanzu. ???(To jama’a farida na tambaya)….
Nan ta sake daga kai ta kalle su,har yanzu suna wata duniyar . Ta kalli kanta ta kalli Bahijja sai taga ta mata nisa,ta mata fintinkau nesa ba kusa ba…
“”Shin ni ya akayi na kasa hada Deeni da kowanne irin namiji a duniya ? Tabbas saboda Allah bai taba hadani da namijin da ya kaishi bane,yayin da Allah ya hada Deeni da macen da ta fini.”
Kau da kai tayi taji hawaye na zuba mata,tsananin kishi da son Deeni taji yana shigarta,ta macen da abinda ya kawota,ta mance da cewa ita matar wani ce,uwar wasu ce….
Karar wayarta ce ta dawo da su hayyacinsu duka,nan tayi saurin share hawayen yayin da Deeni da Bahijja suka ganta bazata a gabansu..
Ras !!! Bahijja taji gabanta ya fadi,ita ma din kishin farida taji ya shigeta,har yau in ta tuno irin soyayyar da Deeni da Farida sukayi sai taji hankalinta ya tashi…
Deeni ganin Farida a gabansa bazata tana kallonsa tamkar ta hadiyeshi yasa ya ji ya shiga dan rudani,musamman da ya san yadda Bahijja take da kishin Farida a zuciyarta,duk da ya sha nuna mata cewa Farida ba ta gabansa yanzu,amma ta kasa fahimta. Sam ko kadan babu ita a ransa,amma ya rasa dalilin da yasa yaji ya wani irin rudewa a wannan lokacin…
Bahijja na kallon irin rudewar da yayi yasa taji ranta ya mummunan baci,hankalinta ya tashi .
Dukkan su idon su ya rufe da wani irin kishi,musamman irin kallon da Bahijja ta ga Farida na yiwa Deeni. Yayin da Farida ta dinga jin kishin irin kallon da Deeni ke yiwa Bahijja…
Nan faridan ta daure,tayi dariyar yake ,ta ce….
“”Ango da Amarya ,ina tayaku murna,Allah ya bada zaman lafiya..”
Bahijja bata iya ta amsa ba,sai Deeni ne ya amsa a takaicw,yasa kai ya fita..
Farida ta kalli Bahijja tace,”Amarya,Mama tace in fito da kee ana jiranki wurin walima””
Girgiza kai tayi dakyar ta cije tayi dariyar yake,ta fito suka jera tare..
Tunda ta fito idon kowa ya koma kanta ta fito ta haska wajen gaba daya kowa sai albarkacin bakinsa yake fadi,Mama kanta ta kasa hakuri ,ta taso da fara’arta ta zo ta kama hannun Bahijja ta jata gun zamanta. Wannan ya kara bakanta ran Farida,har agun mama ma Bahijja ta ture gwamnatin ta …
Wani hawayen bakin ciki taji yana zubo mata ,wurin walimar da bata zauna ba kenan,ta juya ta koma ciki,har aka tashi daga walimae bata dawo ba….
Ranar lahadi jamaar biki kowa ya watse ,yayin da ranar lukman ya tare da amaryar sa a gidansa da mahaifin su ya bashi,yayin da Shamsuddeen ya koma saboda aikin da ya bari a kamfaninsu na kaduna. Farida kuwa da yake ana hutu da yaara za su zauna su yiwa mama hutu…
Mama ta shiryawa Bahijja da Deeni kayansu,siyayyar da ta musu na kayan sawa da sauran su ta sa a mota ta tura tare da baba andi taje ta shirya musu….
Gidan yayi tsit ba kowa daga Farida da yaranta,sai Deeni da Bahijja wanda suma suna shirin tafiya nasu gidan….
Alhaji ne ya kira Deeni da Bahijja falo suka same shi yana zaune shi da mama ,nan suka nemi wuri suka zauna.
Alhaji yayi musu nasiha da fada sosai tarw da musu fatan alkhairi haka mama ta kara damka musu amanar juna tare da musu nasiha da cewa siyi hakuri da juna,zo mu zauna zo mu saba..
Alhaji ya mika masa key na gida.
ya yi murmushi ,”Nagode Baba,mallaka min Bahijja da kayi matsayin nata ta kadai ya ishe ni babbar kyauta. Ka mata waliyyanci,ka zama mahaifinta,yayin da Bappah ya min waliyyanci. Na gode da amanar yarka da ka bani Baba,ina da gidana nallakina na godan gona wanda ka taimaka min na kafa shi,haka Bahijja tana da gida,zamu zauna a duk wanda muke so. A halin yanzu rayuwar mu soyayyarmu ,ayyukanmu,gidajen mu da dukiyoyinmu suna hake ne. Baba,Mama,mun gode ,kuyi ta mana addu’a,muma zamuyi ta muku..”
Dariya sukayi yayin da yace,”Allah ya muku albarka Deeni”
“”‘Ameen “””.
Suka amsa a tare ,sannan sukayi sallama da su mama ta raka su har bakin mota ita da Bahijja kamar ba zasu rabu ba.
Wannan soyayya da shakuwa na Bahijja da Mama ba karamin dagawa Farida hankali yake ba,sai tana ji kamar ta zama ita bata da mihimmanci..
Tabbas daga Farida har Bahijja suna fama da kishin juna da ke tsananin cin su a zuciya..
Kai tsaye suka wuce gidan Deeni ,wanda ya ra tsara musu shi sosai,kana shiga gidan zaka fahimci gida ne na masu ilimi daga bokin har addini…
Tun a mota Deeni ya lura da Bahijja bata magana,duk kokarin da yayi don ya takaleta amma bata kula shi ha,shima sai ya nuna mata halinsa,ya dage kai ya kyaleta..
Addu’a tayi sannan ta sa kafarta a gidan ,wani irin kamshi taji yana tashi mai kwantar da zuciya.. Ta lumshe ido tana shaka,nan take taji hankalinta na kwanciya ,fushin nan da take taji yana sauka. A hankali ta dinga bi tana zaga gidan ,Deeni ya bita danido zuciyarsa cike da sonta da sha’awar ta.
Ko ina ta gama zagawa yana biye da ita,ta dawo falo ta zauna,nan ya jawo kujera ya zauna a gabanta yana kokarin su hada ido amma taki. Ya yi murmushi ,yace..
Haka kawai Amarya taji bata son sakar min fuska a daren mu na farko a gidan mu ?
Zuba mata ido ya yi yaji kamar yanzu ma ya fara sonta..
Ina sonki Bahijja soyayyar da ban san irinta ba,komai kika yi a rayuwa sai inga ya miki kyau. Wannan kamshin da ake sha min ma sai naga ya miki kyau,kin kara burgeni””.