HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nan ya sauko yasa kanshi bisa cinyoyinta ,ya jawo hannayenta kansa.

MISBAH na meye ya dame ki ?

Ta kwantar da kanta akan nasa suna manne da juna ,ta ce.

(My dear nice house)”.

Ya yi murmushi ,yace. Na tabbatar u will be a good home maker?”

Nsha Allah”Ta amsa.

“Deeni ina sonka”

Ta fada tamkar meyin rada a kunnen sa,yana jin muryarta na ratsa shi,yana jin tsigar jikinsa na tashi ,tsantsar sha’awarta cike fal zuciyar sa.

“”Bahijja ki kasance dani har abada karki kyale ni,ki cika min gida da irinki da alnarkar ki,ki cika min gida da yaranki,zaki sani farin ciki sosan gaske””..

“” Komai kake so zan maka Deeni,,Allah ya bani yaran da zan cika masu. Nima ina addu’ar Allah ya bani irin Deeni,Allah ya bani ikon sanya ka farin ciki da kyautata maka,Allah ya bani juriya akan ka Deeni..

Ina maka wani so Deeni,gashi dai ka zama nawa amma zuciyata na cike da tsoro da fargaba.”

“” Kar kiyi fargaba Bahijja,ni naki ne “”

Bai ankara ba sai jin hawaye na zuba masa yayi Saurin dago ta hankalinsa a tashe..

My deae mene ne ??

Idonta jawur ta kalle shi,”ko zaka iya fassara min rudewar da kayi lokacin da kaga Farida ??? Na mene ne ??  Don kaji tsoro masoyiyarka ta gannu a manne da juna ko kuma ka rude ne saboda ka ga tsohuwar masoyiyarka ???

Tofaa!!!! Ango kaka-kara   kaka………

SUMY LUV????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Written by  SA’ADATU WAZIRI GOMBE

=================== GIDAN NOVELS ====================================

 

Assalamu Alaikum

Yan uwa a wannan page din nake tunanin zan kammala littafin nan part 2 wato kashi na biyu insha Allah…

Wanda kuma a nan nake tunanin dakatawa zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu…….

Idan da me korafi nasan dayawa sunada contact dina,,,so se yayi pinging dina…..tnks

 

49

Zura mata ido yayi cike da mamaki,”Haba Bahijja,ban zaci haka daga gareki ba,wannan halin na zace shi ne daga halin wata me kasa da shekarunki, (me matured)”

Ranta taji ya mummunan baci,ta ce.

I will not be ,me kake nufi? Me yasa kake avoiding tambayata ? Ka fada min wane irin rudewa kayi don kaga Farida. ??

Ranshi yaji ya baci,amma sai ya daure ya ce.

Ke kinga ya dace mu zauna muna bata lokacinmu a irin wannan lokacin akan wannan maganar marabtushe ko kan gado ? Me ya kawo maganar Farida tsakanin mu a yanzu ?

“Akwai abinda ya kawo,ka ban amsa,me yasa mijina zai rude don yaga tsohiwar budurwarsa ?

For God sake!!Farida matar wani ce,uwar wasu ce,saboda mene ne zaki ta da min rigima yanzu ? Har sau nawa zan fada miki cewa bana son farida,na manta da farida. In ada baya can na so farida laifina ne da za ki dinga daga min hankali akan farida? Haba Bajijja ,a yau zamu fara sabuwar rayuwa,ya zaki bari wani dalili mara tushe ya nemi kawo mana matsala ?

To naji ya ishe ni haka, kiji kiyi tunanin duk yadda ki ka ga dama ,na ganta na rude sai yaya ?””

Cikin zafin rai da bacin rai yake maganar wanda ya kara tunzura Bahijja,ya kona mata zuciya. Ta fashe da kuka ta nufi daki ta rufe ….

Bai yi yunkurin binta ba don shima yana cikin zafi,ya zurawa abubuwan da ya shigo musu dashi na ci da sha  ,duk ta daga musu hankali har ya ji bashi da sauran sha’awar cin wani abu.

Kukanta yaji yana matukar daga masa hankali,ga sonta dake kara ruruwa a cikin zuciyarsa,amma zafin zuciya ya hana ya bita dakin balle yayi lallashi. Haka  ya dinga kaiwa da kawowa cikin dare,ya rasa me ke masa dadi,haka suka kwana baran-baran a darwnnsu na farki..

 

Ankira sallar asuba yayi alwala ya murda kofar dakinta,ga mamakinsa bata sa key ba ya sameta zaune kan sallaya. Bai ce mata komai ba ya fice zuwa masallaci,ya dawo ya nufi nasa dakin ,duk da ya kwanta ba bacci kirki amma haka baccin ya gagare shi..

Karfe takwas na safe ya fito falo,anan suka yi kicibis sanye da hijabinta…

“”Ina kwana?”” Ta fafa tare da kau da kai

Bai amsa mata ba ya sha gabanta ,tayi saurin kaucewa ta kama hanyar fita..

“Ina zakije ? Ya fada cikin daga mirya.

Gidana zan tafi”.ta bashi amsa a takaice.

Da izinin wa ? Da yardar wa ? Karki manta baki da gidan da ya wuce wannan,sannan fita a gidan nan ba da izinina ba,kar ki sake wanann kuskuren….

Ya fada cikin tsare gida ,fuskar sa ba alamar wasa,ya juya..

Wani iein bacin rai da takaici taji ya turnike ta,ta juya ta nufi kicin ranta bace ta dinga kaiwa da kawowa ,gata ba gwana ba wurin girki,da kyar ta samu ta hada masa patatos da source tare da yanka fruit da fresh juice da kuma ruwan tea a flask tare da sauran kayan tea ta jera kan dining table..

Yayin da Deeni yake kaiwa da kawowa ,sam baiji dadin yadda ya mata ba,to amma yana da matukar muhimmanci tasan cewa shi mijinta ne,aure sukayi ,ba zata yi yadda take so ba. Haka nan zafin zuciya da jin kai ya hana shi zuwa ya lallasheta,don shi gani yake bai mata laifi ba..

Bahijja na shiga daki ta fashe da kuka,nan ta dauko diary din nan cikin jakarta ta rungume tana kuka…

Hankalinsa ya kasa kwanciya har sai da ya bita dakin ganunta rungume da diary din tana kuka sosai ya taba zuciyarsa. Abu biyu ne suka hadu masa,tsananun sonta da tausayinta da kuma wani zafin kishi,saboda yasan me ke cikin wannan diary din .

Nan ya daure ya isa gareta ya jawota jikinsa,nan ta hau kokawar kwace jikinta amma bata yi nasara ba. Ya rufeta ruf kan faffadan kirjinta,ga turarensa mai hade da kamshin sin sa da ke ratsa ta ,yana kashe mata jiki,kawai ta fashe masa da kuka..

( I’m sorry my dear)nayi laifi kiyi hakuri..

Ya fada cikin murya mai taushi da lallashi.

Bahijja hawayenki da kukan ki yana daga min hankali fiye da komai,kin san yadda nake matukar jinki a raina ,kin san yadda jiki da euhina tare da zuciyata suke tsananin sonki ,please Bahijja kar ki daga mana hankali daga ni har ke.

Ba mai samun farin ciki a kan wannan halayya taki na kishi (I’m sorry l hurt you).

Bahijja da ina da ikon share baya da na share,amma bani da wannan ikon,abinda zan iya shi ne yanzu-yanzu kuwa da nan gaba duk kece.

Bahijja ina so kamar yadda kika taimaka min na manta baya na cigaba da rayuwata ina so ki taimaka ki bani hadin kai ,mu shirya rayuwarmu mai cike dab tsabtatacciyar soyayya da fahimta tare da kula da farin cikin juna…

Ina so ki sani kina da matukar muhimmanci a rayuwata,please dont make me hurt you again..”

Ta fashe da kuka,”Deeni na gaza ban san mw yasa na kasa jurewa ba,ban san me yasa nake jin tsananin kishin Farida ba ,duk da na sani matar aure ce,matar dan uwanka ne,uwace. Deeni ka taimake ni,zan iya jure komai anma banda wannan..”

Ta dago dara-daran idanuwanta wanda sukenrine,suka dawo ja,hawaye na zuba wanda yanayinta ba karamin tsuma shi yayi ba,ta ce ,

“”Deeni kasan ina sonka ko? Ina sinka sosai “” Ya girgiza mata kai yana jun tamkar ya hadiyeta don so ,ya ce.

Nima ina sonki Bahijja kin san haka kuma. Ina sonki”

Ta kankameshi ,”Nasani Deeni ,”please ka kula dani..

“Zan kula da ke Bahijja na,bari ma in fara daga yanzu.”

Nan yasa baki yana lasar hawayenta tare da bin fuskarta,kan idanunta zuwa wuyanta yana sumbata. Haka ya dinga bin jikinta.

Wani irin abu taji yana zaga jikunta har zuwa tsakar kanta,yayin da ta dinga jin wannan kuncin yana barin zuciyarta,sai tsananin so da shaukinsa,taji zuciyarta ta wanke tas. Nan ta biye masa itama ta ramawa kura aniyarta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button