HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sun jima manne da juna sannan ta zame jikinta a hankali ta nufi bayi don shirya masa ruwan wanka,yayin da Deeni ke kwance idonsa jawur,hankalinsa tashe.. (Deeni dai ba wanka yakeda bukata ba????????????????????????sry anty zee karkice banda kunya)..

Kwarai ya so kasancewa tare da ita yau,sai dai kasancewar Bahijja na farko ya zamana a wuri na daban lokaci na daban…….

Karfe goma mama ta turo musu da break fast kala-kala,sannan tayi waya suka gaisa ta kara da cewa su shirya jirgin su zuwa kasa mai tsarki,wato saudia. Karfe sha biyu ne wanda ta biya musu suje suyi Umra su kara yiwa Allah godia tare da yin addu’o’i,sannan daga nan in suna so su wuce duk kasar da suke so su zaga duniya har na wata guda ,sannan su dawo.

*****     *****     *****

A kasa mai tsarki Deeni da Bahijja suka san sirrin juna,suka zama abu guda,,suka barji gumin juna. Kwarai sun more rayuwar su yadda ya kamata ….

Bayan sun gabatar da idabar su ta Umrah tare da yin addu’o’in su,nan suka ci gaba da gudanar da ibadar su na aure ,sun manta duk wani damuwa da bacin rai da tashin hankali da suka taba fuskanta a rayuwa ,suka bude sabon rayuwa mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali tare da yiwa juna alkawarin kula da juna farin cikin juna da kuma kasancewa da juna har abada Nsha Allah…

 

Bahijja na da kyau na daukar hankali,kyau mai sa nutsuwa da kwanciyar hankali ga wanda ya mallake ta,yasan sirrin ta,ya dandani zumar ta. Don haka Deeni ya tabbar shi din mai sa’a ne da ya mallaki mace kamar ta…

Duk inda ake son mace Bahijja ta kai ta kawo,sai dai abinda yake kara jan hankalin sa gareta da kara masa sonta shi ne halayyar ta,hikimar ta da baiwarta. Yadda take kula da shi,take sarrafa shi da rayuwar sa,irin soyayyar da take masa,take kuma nuna masa,ga wata girmamawa ta musamman . Duk da kasancewar ta girme masa amma bata taba nuna masa raini ba,asali ma in ba an fadi ba babu mai cewa ta girme masa,saboda bala’in dacewa da sukayi da juna …

Halayyar su ta zo daya,tunaninsu yazo daya,duk abinda daya keji dabshi daya naji da shi. Don haka suke yawan hakuri da juna ,in data ya hau daya na dannewa,sun zauna sun tsara yadda za su gabatar da rayuwarsu cikin soyayya da saukin rayuwa..

 

Bayan sunyi sati biyu suka bar saudia zuwa Dubai,sun zaga kasashe uku zuwa hudu suna yawon shakatawa da more rayuwar su. Sunyi wani irin sabo da kara shakuwa da juna sosai sosai..

Sun kasance cikin farin ciki marar misaltuwa ,watansu guda suka tattaro suka dawo gida Nigeria..

A nan suka tarar da mummunan labari da kuma mummunan tashin hankali na rasuwar Shamsuddeen tare da mahaifin Farida…

Satin su biyu da tafiya hatsarin ya faru da su a cikin garin kaduna,mahaifin Farida ya je duba Shamsu a ma’aikatar su don ganin ya yake da yadda ayyukan suke tafiya,dama ya saba kai masa irin wannan ziyarar . Anan Shamsu ya bar motarsa a office ya biyo Alhaji Ahmad don dawowa gida tare ,a hamyar su ta dawowa tsautsayi da karar kwana suka hadu da doguwa ta taho ba birki ta hade motoci da yawa tayi barna wasu sunji rauni wasu sun rasa rayukansu ciki har da Shamsuddeen da Alhaji Ahmad wato mahaifin Farida.

Cikin tashin hankali da damuwa Deeni da Bahijja suka nufi kaduna inda ake zaman makoki….

Muje ga littafi na uku…

DANDANO DAGA LITTAFI NAGABA

 

kanta sunkuye gaban su ya ce,”Mama ina jinki “”

Hajia ta kalli Bahijja ta ce,””Bahijja kin tabbar kin amince ina sonki kamar yadda nake son Deeni ko ? Kin dauke ni mahaifiyarki ?

Bahijja ta girgiza kai,ta ce,”Kwarai Mama,tsakanina da ku sai addu’a ,bani da iyaye amma kun maye gurbin su,tsakanina da ku sai addu’a”

Mama tayi murmushi ta ce,Alhmadulillah,kamar yadda na rike ki ‘yata haka ba riki farida,ina neman alfarmarki bamu hadin kai mu hada auren Deeni da Farida…….????????‍♀????????‍♀????????‍♀

SHIN WANNAN MUTUWAR TA SHAMSU FARIDA AKAYIWA KO BAHIJJA ???????

SAI NA JIKU

TAKU HAR KULLUM

=================== GIDAN NOVELS ====================================

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button