MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yadda deeni yake cikin tunani da fargaba haka farida ma ta kasance ,tana sauraron wayar deeni .
Bayan Ahj umar wato mahaifin deeni ya gama duk wani abu daya saba na al’adar sa in ya dawo,yana zaune a falonsa haj A’i ta same shi da maganar deeni .
“Alhaji magana zamuyi” ta fada tana kallon sa ,hakan yasa ya juyo ya maida kallonsa gare ta tare da tattaro hankalin sa akanta yace “”” wace irin magana kuwa “? Ta gyara zama tacw ,,nu kabata sanin soyayyar deeni da farida kuwa,,”??
Ya kalleta ban gane ba ,deeni da farida?
“”. Ta girgiza kai ” kwarai……
Nan ta bashi labarin soyayyarsu,da shakuwarsu, takara da cewa .
“Yanzu lokaci yayi da mahaifin farida yakeson ya aurar da ita tarw da yan uwanta,kamar yadda kasani shi mahaifinsu yaranshi na gama secondry sch yake aurar dasu ,farida kuwa bata da wani saurayain da yawuce deeni ,,dan haka tayi masa magana ya fito,ya tura iyayensa a san da maganar neman aurenta ,shi ne ya min magana ya ce in fada maka””
Alhaji ya kallwra cike da mamaki ,ya ce .
Haba hajia ,ya kikemun irin wannan maganar kamar wata karanar yarinya ? Insu yara ne kema sai ki zama yarinyae ki biye musu ? Yaron da karatu ma ba inda yaje ? Yaron da baisan ciwon kanshi ba shine zaa nemar masa aure? Dan uwansa ma yaushe akayi maganar airen sa wanda ya girme da komai balle shi ? Da maganar shamsu ma kika min sai na saurareki amma DEENI ?ai ko ina da yarinya bazan aurawa kamar deeni ba ,yaron da yaki karatu,ya kasa nai da hankali akan rayuwar sa, yasan me yakeyi,ahekarun deeni nawa wai kike maganar auren sa? Shekarunsa ishirin da daya,yaro ne dabai san ciwon kansa ba balle har a dora masa na wata .
” baba addini ya hana dan shekara ishirin da daya aure ????
Muryar deeni sukaji tsaya daga kofa……………….
Copied by sumy luv❤❤
????????????????????????MISBAH????????????????????????
Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
COPIED BY SUMAYYA SA’AD❤❤
10
Tunda sassafe farida ta bugawa deeni waya,daga jin muryarsa tasan ba lafia ba ,hankalinta yai mummunan tashi,kawai sai ta fashe mishi da kuka ,muryarta na rawa tace .
“”Deeni ya zamuyi ? Dama abinda nake tsoro kenn kullum ,kasan babanka ba zai yarda ba ,haka abbana ba mai canja masa ra’ayi,bazai taba bari na in zauna injiraka ba ,hada ni aure zaiyi da koma waye “”
” cikin muryar rauni da matujar tashin hanklai yace
“”Saurareni farida, baki da wani miji sai in Nsha Allah,Allah ne ya hadamu ba mai rabamu . Inma baba yaki nizanje in sami yayana babana,Bappah na zaj daura mana aure ,ba dai abbanki zai aura min ke ba ?
Abbanki zai aura min ke ,in har nabturo waliyyi na zai daura mana aure . Anjima kadan ,zan fita,zan wuce gombe ,zan je in sami bappah na ,kafin in wuce inason ganinki,ki fito kofar gida mu hadu”
Nan ra amsa masa da toh,ta ajiye wayar .
Bai bata lokaci ba yayi wanka ya kimtsa,ko breakfast bai tsaya yi ba ,ya cewa mama shi ya fita. Ko kallon mahaifinsa baiyi ba balle ya gaishe shi.
Tsawa ya daka masa tare da kiran sunansa.
Cak deenin ya tsaya ,sai dai ko juyowa bai yi ba balle ya yi niyyar zuwa inda yake.
Alhaji yace ,ban haifi dan da gari zai yawaye yana kallona ya wuce bai gaisheni ba,baka isa ba .”
Jin hakan yasa deeni ya juyo ya kalleshi fuska ba walwala ya ce .
” Ina kwana ? Da fatan ka wayi gari lafia “”?
Bai saurari amsar mahaifin nasa ba yasakai ya fita ,mahaifin nashi ya bishi da kallo. Baiyi mamakin hakan ba,sabida yasan halin deeni ,sai dai fa duk abinda zaiyi yi dan baazaiyi aure yanzu ba da bai san ciwon kansa ba ,yayi haukansa ya gama .
“”Ina kaunarka dana ,,shiyasa nake son yiwa rayuwarka gata kafin in kai ga maka aure,,sai na maidaka mutum sosai,,mace kowa zaka sani kowacce iri kakeso a rayuwa ”
Mahaifiyar deeni ce ta shigo tare da matsowa inda yake , ta tsake masa tunanin da fadin ”
Alhaji bazaka sake duva maganata ba kuwa ?
Ka auna irin soyayyar da rayan nan suke yiwa juna , karfa ka illata rayuwarsu sabida wani dalili naka na daban . Sannan yarinuar nan ya kakeso tayi ? Dukkna tsawon rayuwarta bata da wani wanda take saurara in ba deeni ba ,kanaso ace deeni ya yaudareta ya rabata dawasu mazan kuma shi be aure ta ba ?
Ya dago udo ya kalleta yace ,
In bazaki gaji da maganar nan ba ,to nima bazan gaji da fada miki a’a ba ,sabida bazan biye miki inbata rayuwar dana ba . Inshi bashi da hankali yakamata ace ke kina dashi .
” Alhaji a duba yarinyar nan,ita kuma meye laifinta a ciki don taso danmu,jininmu ,sai mu hukuntata akanshi ? So kake mahaifinta ya hadata da duk wanda ya samu ? Farida kamar diyarmu ce,bazamuso ta shiga gidan wani can da bata san halinsa ba ..””
” wannan ne damuwarki ?
,” duka”” ta amsa masa .
” Saboda deeni yanason yarinyar nan fiye da tunaninka ,haka ba jima da saka burin farida tazama surikata ,uwar jikoki na . Na tabbatar da zanyi alfahati da ita ,duk inda akeson mace ta gari ,yarinyar nan ta kai “”
“”. To shikenn naji ,karki damu indai wannan ne damuwarki “”
Ta kalleshi cukin murna sa doki tace ,,kana nufin ka amince ?
” ki saurara ,ki sa ido kiga hukuncin da zanyj ,,ba zan bata rayuwar kowa ba ”
Yana gama fadi ya mike ya nufi dining table ,ta bishi da kallo tana nazarin kalamansa.
Kawarai hakan ya mata dadi ,saboda akwai alamun nasara . Da murna ta mike ta bishi tana murmushi ba tare da takara ce mishi komai ba ,sai kokarin masa hidima .
Denni na fita kai tsaye ya wuce gidansu farida ,a kofar gida suka hadu dukkansu hankalinsu a tashe ,,farida idanunta jawur tana ta zabgar kuka tamkar wadda akace iyayenta syn rasu. Hakan ya mummunan daga hankalin deeni ,soyayyarta ya dinga ji yana ratsa shi,yaji tankar ya jawota jikinsa ya rumgumeta ,sai dai bashi da ikon yin hakan ,don hakan sai yayi abinda yasan zai iya ya hau lallashinta tare da bata karfin gwiwa cewa ba gudu ba ja da baya yana tare da ita ,alkawarin da ya mata na aure ba fashi ,yana tare da ita.
Ta kalleshi idanu jawur sun kimbura ,ta ce
“”Deeni ina zan saka raina in na rasa ka ?
” ya zanyi rayuwar da batare da Deeni ba ?yaya zan soma rayuwa da wanj namiji a rayuwa matsayin miji ba Deeni ba ??
Nan yayi saurin rufe mata baki ,idanunsa suka kada,ya dinga jin wani irin zafi da radadi a zuciyarsa.
” karki kara furta haka farida ,karki sake ambatun rayuwa da wani namiji a rayuwarki. Kinajin zan iya numfashi in ganki kina rayuwa da wani ? Farida duk runtsi,duk wuya ,duk dadi ,munabtare da junan mu. Ni ne mijinki abokin rayuwarki,in Allah ya yarda zan mutu in na budi ido naga kin auri wani namiji “””
Hawayene ya gangaro mishi na tausayin kansu duka .
Sumy luv❤❤
????????????????????????MISBAH????????????????????
Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE
COPIED BY SUMAYYA SA’AD❤❤
11
Deeni ,farida ,ku ne da sassafe haka? Lafia kike ta kuka inata magana tun dazu baku.ma san ina gurin ba ?
A tare suka mai da kallonsu kansa,shamsu ne yayan deeni. Tuni deeni ya fada jikinsa yana kuka.
” ya shamsu kaji abin da Abba ya mun ko? Wai bazan auri farida ba ,ya shamsu kasan irin son da nakewa farida,ta yaya zan iya rayuwa babu ita ?
Itama faridan tayashi tayi tana kukan tace .
” ya shamsu ka taimakemu ,bazan iya auren wani namiji ba sai deeni,ya shamsu zan mutu inba deeni ,”
Kawai ta durkushe har kasa ta rushe musu da wani irin kuka deeni na tayata . Gaba daya suka zamewa shamsu hoto,ya bude baki yana kallonsu,yana mamaki duk da yasan irin soyayyar datake tsakaninsu ganin su cikin wannan tashin hankalin ya bashi mamaki tare da tausaya musu.