HAUSA NOVEL

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

” yi hakuri farida ” ya fada cikin muryar lallashi.

“” ba mai rabaki da deeni insha Allah ,zan taimaka muku , dake da deeni duk kanne na ne ,share hawayenki,mike muyi magaana.”

Haya ya dunga sharewa deeni hawayenshi ,yana lallashinsu duka har suka dab fara samun nutsuwa ,anan ya tambayi deeni ya bashi labarin yadda sukayi da mahaifinsu,farida ma ta fada mishi yadda tayi da nata mahaifin ,ta kare zancen da kuka tana cewa ”

Ya shamsu in deeni bai fito ba wlh Abba auramun duk wanda yakeso zaiyi,ni kuma ya shamsu deeni nake so ” ta fashe da kuka .

” ya isa farida,naji ”

Ya fada cikin muryar lallashi da tausayawa , a ransa yace ,”soyayya me zafi ta kama zuciyar yan  yara.”

Ya tausaya musu kwarai,musamman a wannan shekarun irin na su da dukkansu ba mai tunani dai dai,,haka nan duk yadda zaa musu bazasu taba fahimta ba ,sabida sun haifi soyayyarsu tun suna yara suka tashi da ita ,sukayi ta rainonta ,don haka ravasu da juna ba karamin tashin hankali bane a gare su. Don haka ya kudiri aniyar taimaka musu,sabida a halin yanzu bazasu taba fahimta ba ,abu daya zasu fahimta a aura musu juna,kafin haka ya faru kuwa sai iyayensu sun canja ra’ayinsu ,ko dai baba ya hakura yayiwa deeni aure yanzu,ko kuwa Abban farida ya hakura tabar farida har deeni ya gama karatunshi. Sai dai fa wannan abin yafi komai wahala,don kuwa in duk duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su canjawa iyayensu ra’ayi ba.

A nan ya shamsudden suka yanke shawara da deeni da farida. Cewa zasuje can Gombe su sami Bappan su suyi mishi bayani ,haka zai nemi wani yayanta ya rakashi katsina itama su sami wani yayan mahaifinta wanda in abbanta yaki amincewa shi sai ya daura mata aure da deeni,shima deeni se kanin mahaifinshi ya masa waliyyi, in yaso wurin zama gida da komai zai dauki nauyinsu akansa.

Nan take murna ta cika zuciyar deeni da farida,har ma suka haskowa juna murmushi,suna yiwa shamsuddenen godiya .

Kwarai yaji dadin ganinsu cikun farin ciki ,saboda shi dai daga deeni har farida kannen sa ne .

Bayan sun sami butsuwar ne ya tambayeta ko Abbanra ya tashi ? Don dana baba ne ya aikeshi ya  ce ya fada masa yau da yamma inbaya komai yana so su hadu,akwai maganar da zasuyi .

Nab deeni da farida suka kalli juna jikinsu yayi sanyi,deeni ya ce ” maganar rabamu zasuyi ko ?

Shamsu yace kwantar da hankalinka ,in ma magnar zasuyi ai mun samo mafita ko ? Kasan ko baba beji maganar bappa ba amma dai bappah zai saurare mu ,kuma ya daura maka aure ko ?

Farida ma tace ,Abban mu dai najin maganar Bappan mu,amma fa zai yi wuya ya canja masa ra’ayi , sai dai nima zai iya daura min aure ”

Shamsu yace to kun gani ,karku damu,kuyi murmushi”

Nan suka masa murmushi duka,shima ya musu sannan ya shige ciki ya barsu a gurin a tsaye.

Deeni ya kalli farida yace, ” Nsha Allah sai na mallake ki masoyiyata ,matsayin matata ta sunnah”.

Allah ya tabbatar mana deeni,tafada tana kallon sa.

Yace , farida in yaya shamsu ya fito zamu wuce,inaso ki tuna ki sani ,duk wuya duk rintsi muna tare,farida ke tawa ce kimun alkawari.””

“” ni taka ce har abada ,ni amanarka ce””

“”Farida nima naki ne har abada “”

” Mu tafi ” muryar shamsu sukaji ya fito.

Nan ya dinga zolayar farida yana cewa.

” mata zankadediyar zan masa a Gombe ,sai ku zama ku biyu ;”

Ai kuwa bai ankara ba ya ga tasa masa kuka ,ba shiri ya hau lallashi har ya samu tayi shuru. Yana jinjina soyayyar da suke yiwa juna . Nan ya shige ciki ya fadawa baba sakonsa ,sannan ya ciro motar sa suka kama hanyar Gombe ,farida na tsaye tana kallon su har suka bace .

Sumy luv????????????????

????????‍????????????‍????MISBAH????????‍????????????‍????

Writting by SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA’AD❤❤

12

Dab da magriba Alh.Umar ,wato mahaifin deeni ya dawo daga office dinsa,kai tsaye ya wuce gudansu farida,ya samu mahaifinta a falon sa ,suka gaisa ,suka hau tattaunawa akan kasuwanci sannan matsalolin kasarmu da muke ciki na yau da kullum har aka kira magriba,sukayi alwala suka nufi masallaci tare.

Abinci da komai tare sukaci a gidan Alh. Ahmad,wato mahaifin farida. Suna nan tare har bayan isha’i,sukayi sallah suna hira har Alh. Umar ya yi masa maganar da ainihin ta kawoshi. Sun jima suna tattaunawa akan maganar wanda ya dauke su tsawon lokaci,har kusan karfe goma na dare ,sannan suka kai ga matsaya ,suka yanke hukunci, da alama kuwa dukkan su sun amnince da hukuncin da suka yanke.

Goma da rabj sukayi sallama ya nufi gida wanda ya yi dai dai da lokacin da su deeni suka dawo daga gombe.

Alhji yayi mamakin ganinsu a wannan lokacin.

” shamsu ,deeni, daga ina haka “?

Deeni bai saurareshi ba ya kama hanyar shiga cikin gida,ya daka masa tsaqa.

” Wai bada ku nake magana bane zaka kama hanya ka shiga ciki?

Bai saurare shi ba ya cigaba da tafiya,hakan yasa Alhaji shan gabansa ya ce,,,,

“” kai saurara ,gidana kake ,magana nake maka,wa zaka gwadawa danyen kai ? Me kake ji dashi ne ? Kana tsaye a gidan nawa………….””

Deeni ya katse shi ,ya ce, ” ina tsaye a gidan mahaifina ne ,bandmga kuma wanda ya isa ya hanani shuga gidan nahaifina ba ,randa na shiga gidan mahaifinka sai ka kore ni ;;””

“” Deeni !!! Shamsu ya daka masa tsawa .

“” Bakada hankaki ne ? Baban kake yiwa wannan maganar? Ban fa sanka da rashin da’ a da kadabi ba , meye ya haifae da wannan rashin da’ar ?

Mahaifin nasu ya kalle shi ,”dakata shamsu,kyale ni dashi ,” ya kalle deeni ya yi murmushi tare da shafa kansa ya ce ,

“” kayi gaskia dana ,nan gudan mahaifinka ne ,ba wanda ya isa ya hanaka shiga ko da kuwa mahaifin ne da kansa. Ina alfahari da hakan,da fatan kai ma zaka yi kokarin tsayawa kan kafafuwanka ka samu naka gidan na kanka ka ajiyeqa naka yaran yadda watarana zasuyi alfahari da cewa nan gidan ubansu ne ,don kuwa kai zan iya kyale k saboda kace nan gidan ubanka ne,kuma ba yadda na iya da kai tunda ni nakawo ka duniya. Amma kasani bazan bar dan ko yarka a gidana ba ,sabida kai ka kawosu duniya ,dan haka kayi kokarin nema musu muhalli kafin suzo,in ba haka ba karkayi kuka dani duj randa ba kori naka yaran a gidana na bar nawa dan,tunda gidan ubansa ne ..?

Nan deeni ya dinga jin zuciyarshi kamar wuta ,ransa bace ya shige ciki ba tare da ya sake tankawa ba . Ya fahimci sarai me mahaifin nasu ke nufi.

Alhajin ya bishi da ido yana masa daria ,zuciyarsa cike da tsananin kaunar sa. Sannan ya mai da hankalinsa kan shamsu,ya kalleshi yace .

” In shi yaro ne kai babba ne a kansa,ka dunga kula dashi kana bashi shawara me kyau,ka dai na biye masa. Karku manta ku ya’ya na ne ,ni mahaifinku ne ”

Yana gama fadi ya juya ya yafi batare da ya saurari me zai ce ba ,nan shamsu ya wuce daki yana nazarin maganganun mahaifinsa tare da juya su a kwakwalwarsa.

Bayan fitar Alh. Umar daga daga gidansu farida bai jira sai da safe ba ya nufi bangaren su farida don yana da bukatar yin magana da ita a wannan daren. Ga mamakin sa kuwa ,da ya buga kofar bangarensu ita tazo ta bude masa kofa,ya lura tana cikin damuwa wanda shi ya hanata baccin ma.

Hannunta ya ja har zuwa falonshi ya zaunar da ita suna fuskantar juna ,idonta jawur ,fuskarta cike da tashin hankali. Tausayin ‘yarsa da kaunarta ya shige shi,tana cikin rudani a lokacin da take da shekaru masu rauni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button