HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Malam Yunusa kuwa jin muryar *MUSADDAM* kawai ya isa shaida masa cewar shi ne don kuwa duk yawan malaman makarantar nan babu wanda bai san muryar *MUSADDAM* ba.

Jiki na rawa yace, “ku tashi ku tafi.

Miƙewa *Ummi* tayi tana waige-waige don kuwa tabbas wannan muryar *MUSADDAM* ce, “to me kuma ya zo yi cikin makarantar mu?”

Duk wannan tambayar cikin ranta take yinta, ɗaya daga cikin ƴan matan ajin ne ta matso kusa da su tace, “Kai amma wallàhi kun yi aa’a don kuwa sanin kanku ne malam Yunusa ba shi da mutunci”.

Kallon ta *Ummi* tayi tace, “wanene wancan wanda yayi masa magana, kuma menene halaƙar sa da wannan makarantar…Me ya zo yi?”

Murmushi wacce ake kira Shamsiya tayi tace, “Tab ba ki san *MUSADDAM* ba? Ai shi ne ya gina mana wannan makarantar kuma duk ƙarshen wata sai ya zo ya duba abinda ake da buƙata sannan ya biya malamai kuɗin wata, ai shiyasa ba’a karɓar ko sisi a gurin iyayen mu, saboda shi ne yake biyan su”.

Gabaki ɗaya*Ummi* ji tayi jikinta yayi sanyi, “tabbas*MUSADDAM* ya yi min nisa, nisa irin wacce ke tsakanin sama da ƙasa”.

Tafiya yake cike da ƙasaita har zuwa office ɗin Shugaban makarantar sallama yayi fuskarsa a daure wanda ganinsa cikin wannan yanayin ba ƙaramin mamaki ya bawa shugaban makarantar ba, don kuwa yanayi ne wanda bai taɓa ganin sa a ciki ba, miƙa masa hannu ya yi suka yi musabaha, kujerar dake fuskantar shugaban makarantar ya samu ya zauna, sai da yayi a ƙalla mintuna biyar ba tare da ya furta ko da kalma ɗaya ba.

Shi kuwa shugaban bin sa da kallo kawai yake don kuwa ya san akwai matsala babba kenan.

Murya a dake yace, “shin kana sane da abinda yake faruwa cikin wannan makarantar ko kuma a bayan idanuwan ka hakan ke faruwa da ƴaƴan jama’a?”

Cike da ruɗani yace, “dukda ban fahimci inda zancan ka ya dosa ba ranka ya dade…” dakatar dashi yayi yace, “kullum ina faɗa maka ka kira ni da suna na kawai hakan sai ya fi min daɗi, akan duk wani kame-kame”.

Haɗiye maganar sa yayi a tsorace yace, ” *MUSADDAM* wallàhi ban san abinda kake magana akai ba kuma babu hannu na a ciki”.

Kallon yaron da ya shigo cikin office ɗin *MUSADDAM* yayi yace, “kai je ka kira min malam Yunusa da kuma yaran da yake son ganawa azaba, kuma kace masa na ba shi nan da minti biyu”.

Da guda yaron ya nufi ajin su *Ummi* don isar da sakon *MUSADDAM*……………
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_

 

1️⃣0️⃣

*Life is a question that no one can answer, death is an answer that no one can question. No matter how great you are, your earthly journey will come to an end one day. Let us live everyday like it’s our last day, by doing good and by forgiving one another.*
*May the Almighty continue to bless you & your family and forgive all your sin JUMMA’AT MUBARAK*

 

_______________Ko da yaron ya isa cikin ajin babu malam Yunusa babu labarin sa ga shi kuma bai san yaran da aka ce ya kira ba. Fita kawai ya yi daga ajin da nufin komawa ya fadi yadda ya tarar da ajin, a can ya hango Malam Yunusa hanunsa riƙe da buta da alama zagayawa yayi. Da gudu yaron ya nufi wajen shi, bayan ya gaishe shi sannan yace, “Malam shugaban makaranta yace na kira ka, wai ka zo kai da yaran da ka daka”.

Wata irin murdawa cikin malam Yunusa yayi da gudu ya koma cikin makewayar yana cewa, “kace masa ina zuwa wallahi gudawa nake”.

Yaron kuwa sai da ya tuntsire da dariya sannan ya tafi don isar masa da sakon.

Ya bar Malam Yunusa a halin rudani da danasanin abinda ya aikata saboda a zahiri ya san cewa ko da tana da laifin yin latti hanyar da ya bi don hukuntata din ba daidai ba ce don haka babu ta yadda zai fidda kan shi da cewa ba shi da laifi. Yace, “innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Yau fa na gamu da bacin rana, ALLAH ka kawo min mafita”.

Tsarkake jikinsa yayi sannan ya fito. Ajin su *Ummi* ya nufa yana zuwa ya kira su duk kan su biyun, tashi suka yi jiki a sanyaye musamman ma *Ummi* wacce tun ganin *MUSADDAM* gabakiɗaya ta ji wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe ta, gyara zaman niƙabin fuskarta *UMMI* ta yi suka bi bayan Malam Yunusa ba tare da sanin inda suka nufa ba.

Ganin inda Malam Yunusa ya shiga ne yasa duk suka sauke ajiyar zuciya don kuwa kowa ya shaida cewa shugaban makarantar ba azzalumi ba ne, mutum ne mai nutsuwa da saurarar koken dalibai gami da kwakwanta adalci a tsakanin su da malaman makarantar a duk sanda takadda ta taso.

Sai dai me? Jin yadda komai ya kwace mata jikinta sai rawa yake, gabaki ɗaya taji ta rasa natsuwar ta yasa Ummi take tunanin lalle akwai wani abin. Ganin halin da ta shiga ne yasa Maimuna rike hanunta har suka shiga cikin ofis din, ganin *MUSADDAM* a zaune kuwa *Ummi* ji tayi kamar za ta zame ta faɗi.

Cikin sauri Maimuna ta rike mata hanu da haka suka ƙarasa cikin office ɗin, gaishe su suka yi amma shugaban makarantar ne kawai ya samu damar amsawa *Ummi* kuwa tsabar tsoro ko jin muryar ta ba a yi.

Kallon Malam Yunusa shugaba yayi yace, “Malam me ke faruwa ne tsakaninka da daliban naka a safiyar yau?”

Baki na rawa yace, “Alagafarta malam, an dan samu kuskure ne amma….”

Wata irin tsawa da *MUSADDAM* ya daka masa sai da *Ummi* ta kusa sakin fitsari a zaune daga inda suke tsugunne sun rakube a jikin bango saboda tsoratar da tayi, shi kuwa Malam Yunusa sunne kansa kansa yayi yana mai karato duk wata addu’a da ta zo bakinsa, “ka ga malam kar ka tsaya kana mana wani kame-kame, kawai ka faɗi abinda aka tambaye ka, period!”.

Hadiye yawun fargaba yayi tare da gyara murya kafin ya shiga zayyano bayanan daki-daki wanda tsabar tsoro har ma musayar maganganun da suka yi sai da ya fada ba tare da yayi aune da katobarar da hakan za ta haifar ba.

Tuni wasu irin jijiyoyi suka mimmiƙe a saman goshin *MUSADDAM* ga wani irin ja da idanuwan sa suka yi, leɓensa kuwa sun bushe sunyi fari fat, gabaki ɗaya banda zufa babu abinda ke fitowa daga jikin sa, ganin yadda hanun sa ke rawa saboda fusatar da yayi ne ya sanya shugaban makarantar yayi farat ya shiga zazzagawa Malam Yunusa masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.

Ganin haka yasa *Ummi* ta fashe da kuka saboda tun tana ƙarama lokacin da su kayi rayuwar zaman gidan haya na gidan yawa kafin dawowar su gidan da suke ciki na yanzu sam ba ta ƙaunar ganin ana wa wani faɗa kuma wai saboda ita balle kuma malamin da yake koyar da ita tabbas ta san bai kyauta ba amma ai koma me yayi mata ba za ta iya biyansa abinda ya koyar da ita ba.

(Tabbas Malaman mu abin girmamawa ne da kuma mutuntawa, saboda a dalilin su muka fahimci wane ne mu, a dalilin su muku san ALLAH, a ta dalilin su muka san yadda za mu bauta wa ALLAH domin kuwa ALLAH da kansa yace, “ku san ni kafin ku bauta min” idan kuwa haka ne malamai sun cancanci fiye da tunanin mu, su kan yi awanni a zaune ko tsaye kawai don ganin sun nuna mana hanyar tsira. Ina mai jinjina da kuma roƙon ALLAH da ya azurta duk wani malami walau na addini ne ko na ilimin zamani da aljannarsa maɗaukakiya. ALLAH ka karɓi uzurin malamai wadanda suka koyar domin ka kuma suka wa’azantar domin ka. Ya ALLAH ka yi musu rahama daga cikin rahamarka, amin. Don ALLAH mu rinka tunawa da Malaman mu wanda a yanzu suke halin tsufa ko kuma hali na rashin abin kashewa na yau da kullum ko kuma suturar sa wa da duk dai abinda ALLAH ya ba mu iko da mu taimaka musu da shi, domin kuwa malami shi ne mafarin komai na rayuwa, tunatarwa ce kawai ƴan uwa).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button