HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Yadda *Ummi* take gabzar kuka mai tsuma zuciya gami da sauke ajiyar zuciya ne yasa ya juyo da sauri don ganin abinda ya sa ta wannan ajiyar zuciyar, ganin fuskar ta luluɓe da niƙab yasa yayi saurin furta, “astagafirullah!” Tare da kau da kansa don a tunanin sa matar aure ce.

Muryarsa ce ta daki dodon kunnuwansu da furucinsa cikin nutsuwa yana mai cewa,”ku yi haƙuri ku yafe masa bisa kuskuren da yayi muku, amma babu dole sai dai lura da fadin Allah madaukakin sarki cewa, yana son mutane masu hakuri. Zan so a ce hakurin aka yi tare da jin cewa komai ya wuce, sannan ku ma sai ku kiyaye zuwa akan lokaci don duk shi ne mafari na samun ita wannan baraka….”

“…sannan kai Malam Yunusa a matsayinka na masani mai ilimi bai kamata a ce ka kasa yakar shaidan wajen ingiza ga aikata abu makamancin wannan ba domin hakan ya nuna raunin da zuciyarka ke da shi wajen kiyaye amanar ‘ya’yan mutane da aka damka mana domin kowace daya daga cikinsu amanarka ce, don tseratar da kai daga fadawa halin cin wannan amana, ina ga sallamarka kawai ya kamata mu yi”.

Kallon inda su *UMMI* Malam Yunusa yayi yace, “ku min aikin gafara don Allah”. Komawa yayi ga sashen da *MUSADDAM* din yake zaune, “Wallàhi sharrin shaiɗan ne, ranka ya dade kuma insha Allahu hakan ba zai ƙara faruwa ba nayi muku alƙawari”.

Kuka yake sosai har sai dukkaninsu dake wajen jikinsu yayi sanyi, maimuna kuwa cikin karfin hali tace, “wallàhi malam idan ma kana da laifin mun yafe maka, amma mu da ma ba mu dauki hakan a matsayin wani abu ba saboda mun san hani da kuma tsawatarku na daga hakkin tarbiyyantar da mu da ya rataya a wuyanku. Mu ma muna rokonka tare da hukumar makaranta akan ku yafe mana”.

Shiru office ɗin yayi ana jiran jin ta bakin *Ummi* ganin ba ta da niyyar magana yasa shugaba yace, ” *Ummi* nasan halin ki tun kina karama kin kasance yarinya saliha mai hakuri duk faɗin unguwar na babu wanda bai san wannan ba, don ALLAH maganar ta mutu anan, kiyi masa aikin gafara kin ji?”

Buɗe baki *Ummi* ta yi za tayi magana kirjinta na bugun uku-uku sai wayar *MUSADDAM* ya fara ringing wanda hakan ya sa ta yin gum ta tsuke baki daga yin ta ta maganar don ta ba shi damar amsa wayar.
Ganin number mummy yasa ya tashi ya fita daga cikin office ɗin wanda hakan ya ba ta damar bude baki da cewa, “wallàhi komai ya wuce malam kuma ni ma kamin aikin gafara idan akwai abinda nayi maka, tabbasa na san idan ba don nayi maka laifi ba, ba zaka tsane ni ba…” rusunawa ta sake yi a gaban malam Yunusa tace, ” ..wallàhi Malam ko shakka ba na yi cewa idan ka samin albarka rayuwata za ta inganta, fushin ka a gare ni kuwa babbar asara ce. Domin yadda kake malami a gare ni na dauke ka tamkar uba, domin ba iyaye ne kawai ake koyi da kyawawan halayen su ba har da malamai”.

Gabaki ɗaya jikin su ya dada yin sanyi har shi kansa shugaban makarantar. Malam Yunusa kuwa takaici ne ya tukare masa maƙoshi, a can kasan zuciyarta yana sake jin tsanar yarinyar da take neman tona masa asiri na rasa dan aikin da rayuwarsa kwacokwam ta dogara akai.

Jinjina kai yayi cike da yabawa ilimi da zurfin hankalin yarinyar kafin yace, “Allah yayi muku albarka kuma Allah ya zaɓa muku mazaje na gari”.

Miƙewa suka yi da niyyar fita kasancewar shugaban makarantar ya sallame su, a daidai nan ne kuma *MUSADDAM* ya shigo yana gyara zaman agogon hannun sa.

Jin addu’ar da shugaba yayi musu yasa ya *MUSADDAM* sauke ajiyar zuciya wanda shi kansa ɓaisan dalili ba………

????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

 

1️⃣1️⃣

*Almighty. Keep hope alive in our hearts. We may not see a way out of our predicament but we know that You have a way. You always do in Your own time. Fill our hearts with deep rooted trust in You. Despite the setbacks we have to deal with, You will never disappoint! Aameen.*

 

________Samun guri yayi ya zauna yana fuskantar shugaban makarantar. Yayin da shi kuma yayi gyaran murya yace, “to alhamdullah *MUSADDAM* sun yafe masa sai dai kawai addu’a na fatan ALLAH ya tsare gaba”.

“Hakan yayi kyau ai da ma haka ake son musulmin ƙwarai ya kasance”.

“Za ku iya tafiya” shugaban yace da su . *Ummi* jiki a sanyaye suka bar cikin office ɗin, kallon ta Maimuna tayi tace, “yau dai kin samu cikar burinki ko Friend”.

Sa hannu *Ummi* tayi cikin niƙaɓinta tana share hawayen da sua gangaro mata tace, “tabbas kasancewa da *MUSADDAM* shi ne addu’a ta a kullum sai dai kuma yau ganin shi babu a abinda ya haifar min face ruɗani fargaba da ƙaryewar zuciya, tabbas na ji kunya kuma nayi bakin cikin yadda nake so na kai kaina inda ALLAH bai kai ni ba friend, wallàhi *MUSADDAM* ba ajina ba ne. Ni fa…..kukan da ya ci ƙarfinta ne yasa ta kasa ƙarisa zancen na ta. Dafa ta Maimuna tayi tace, “kar kice haka saboda idan kika ce haka kamar kina ƙalubalantar ALLAH ne kar ki mance shi ne ya sanya miki sonsa a zuciya, ina mai tabbatar miki ALLAH yasan dalilinsa na yin hakan” kawai ki ƙara hakuri insha ALLAH komai zai daidaita kin ji ƙawata. Amma fa gaskiya *MUSADDAM* ya haɗu sosai da sosai” tana magana tana ɗaga gira.

Dundu *UMMI* ta kai mata a baya tace, “ke dai kin shiga uku idanuwanki ba sa ganin komai sai mazan mutane”.

Dariya Maimuna take har tana riƙe ciki tace, “su waye mazan mutanen da na kalla?”.

*MUSADDAM* mana”.

“Tab, a yaushe *MUSADDAM* ɗin yayi aure?”

“Jiya mana”.

Dukkansu dariya suka yi suka shige cikin ajin nasu, da ma Maimuna tayi haka ne saboda ta kawar da bakin ciki a zuciyar *Ummi*.

*MUSADDAM* kuwa su *Ummi* suna fita ya juyo da hankalinsa kan Malam Yunusa yace, “ka san abinda yasa ban yi maka magana a gaban su ba?”

Girgiza kai Malam Yunusa yayi yace,” a’a yallaɓai”.

“Suna na *MUSADDAM* kamar yadda ka sani bar batun wani yallaɓai. Dalili na shi ne saboda ka kasance Malami mai koyar da ɗalibai sam ba ka cancanci tozarci ko kuma cin fuska ba, amma kai ma ka sani ba wai iyawarka ba ne ko kuma zabinka ba ne yasa kake a wannan matsayin ba Allah ne ya nufe ka ya kuma zabe ka da zama jakadan karantar da addininsa ga su wadannan yara don su san addininsa su kuma samu ikon bauta masa ta hanya mafi dacewa. Idan ba ka manta ba jiya kai ma zaune kake a gaban malami yana koyar da kai kamar yadda kake koyar da su a yanzu, shin da haka shi malamin naka yayi maka da ka kawo abinda ka zama a yanzu?”
“…Idan ma haka yayi maka wace riba ka ga ya samu sakamakon wannan mummunar ɗabi’ar? Duk wata ɗabi’a wacce ba ta da amfani babu amfanin ɗaukarta a matsayin abin koyi, ALLAH ne ya ba ka wannan ilimin kuma ka sani ilimin da aka ba ka wallàhi sai ya zama abin tambaya a gare ka ranar gobe kiyama, saboda haka mu yi hattara don ganin mun kaucewa duk wata hanya wadda ba za ta ɓulle damu ba. Ina fatan abu makamancin ba zai sake faruwa a gaba ba. Za ka iya tafiya abinka”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button