HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Godiya malam Yunusa yayi ya fice daga office ɗin yana mai jin wani tuƙuƙin bakinciki a kasan ran sa.

******

Ko da *MUSADDAM* ya koma gida bayan yayi wanka, yayi Sallah sannan yaci abinci. Sai ya dauki waya ya bugawa shugaban ma’aikata wato MD na kamfanin su don ya ji yadda ayyukan kamfanin suke tafiya a ranar kasancewar yau bai samu damar bi ta can ba. Bayan ya kammala wayar ne yabi lafiyar gado ya kwanta don ya ɗan samu ya huta.

Abin mamaki duk inda ya juya surar wannan yarinyar yake gani cikin idanuwan sa, sosai ya ji irin wannan bugun zuciyar da yake ji lokaci zuwa lokaci, kamewa kawai yayi saboda kar ya bada maza a gaban shugaban makaranta.
“To me yasa ne ma ba ta yi magana ba?” Ya tambayi zuciyarsa. Tsaki yayi tare da cewa, “wai ina ma ruwa na da jin muryarta ne?” Sake wani juyin yayi a karo na ba adadi tare da rungumo yana mai lumshe idanuwansa da nufin ko zai samu ya rintsa amma ina abu ya ci tura! Ganin haka yasa shi mikewa ya tashi kawai ya nufi ɓangaren Mummy”.

 

Shigar sa din kuwa ta yi daidai da lokacin da take idar da Sallah. Kallon ta yayi fuskarsa dauke da murmushi yace, “sanyin idaniya ta, mahaifiyata abar alfaharina”.

Murmushi mai ƙayatarwa Mummy tayi cike da jin dadi kafin tace, “a yanzu kenan ko, kafin matarka ta zo ta kwace ragamar sarautar ba”

Karɓar sallayar dake hannunta yayi yana nadewa yace, “mummy na kenan, ke ma ai kin san babu wacce za ta maye gurbin ki a waje na”.

“Haka dai kace yawwa zauna ina son yin magana da kai kuwa dama”.

Sosai *MUSADDAM* ya tsinci kansa da faɗuwar gaba amma sam ba za ka taɓa gane hakan ba saboda kwarjinin fuskar sa duk ya shanye komai.

Zama yayi yace, “mummy na, ina jin ki. Hala kin samo min wani labari ne mai dadi”.

Murmushi ta sake a karo na biyu, kana cikin sakin fuska tace, “da ma ba wani abu ba ne. Tuni ne zan yi maka kamar yadda muka saba kowace shekara muna fitar da Zakka daga cikin abinda ALLAH ya fuwace mana domin fidda hakkin Allah kamar yadda yake a hukunce, ina fatan ba ka mance ba?”

Murmushi yayi yace, “tabbas Mummay, idan zan mance da wannan to fa babu shakka zan iya mancewa da ku kenan, tunda da irin wannan ayyuka kuka raine ni, tun bana iya bayarwa da hannun na, ke da daddy kuke riƙe min hannun ku bayar da hannun na, wannan ɗabi’a ce da tun kan na san kaina nake yin ta, ina sa ne kuma da ma gobe na so nayi miki tuni ni ma sai ga shi kin riga ni”.

Sauke ajiyar zuciya Mummy ta yi tace, “to madalla. Idan akwai sabon akan hakan da ma bai wuce ganin cewa kullum kiran mutane muke domin mu ba su ba. To, a wannan karon ni da kaina nake so na bi gida-gida na rabawa kowa suna zaune daga gidajen su. Ko ya gani?”

“Wallahi yayi sosai Mummy yaushe kike ganin za muyi hakan?”

“Na riga da na shirya komai saboda ɗazu Baba Liman ya zo mun tattauna duk yadda abin zai kasance, saboda haka gobe da safe insha ALLAH za mu raba”.

“Hakan yayi kwarai Mummy, ALLAH ya ƙara girma”.

“Amin, amin”.

****

Washe gari tun da sanyin safiya motar abinci ta iso kofar gidan su *MUSADDAM* ɗauke da kayan abinci iri daban daban, kama daga buhunan shinkafa, taliya da dai sauran su.

Cikin shiga ta kamala mummy ta fito ta rinƙa raba abinci ga mabuƙata fuskarta ɗauke da tsantsar farin ciki ta yadda duk yadda kaso misaltawa sam ba zaka iya ba, hakan yasa ma buƙata suka rinka fitowa lungu da saƙo, abu tun sanyin safiya har kusan yammaci duk inda lokacin sallah ya rinski Mummy sai ta roki masu gidan da su ba ta ruwa ta yi abinta ba tare da duba da yanayin bambancin dake tsakanin ta da masu gidan ba. Sosai jama’a suka rinƙa sanya mata albarka da fatan gamawa da duniya lafiya.

Da haka har rabo ya kai ta ƙofar gidan su *Ummi*….

????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

 

1️⃣2️⃣

_Jinjina da godiya zuwa ga besty na Haupha ƙaunar da kike min baki ba zai iya furtata ba ,fatana a gare ki shine gamawa da duniya lafiya ALLAH ya haskaka rayuwar ki da haske mafi haskakawa._

_Son so Fisabililah_ ????❤️❤️❤️

 

*Allah never said the road would be easy. But He said, “I will be with those who have patience.” Ask Allah to assist you in obtaining whatever you seek, and never lose hope in his mercy. When you are tempted to lose patience with someone, think how patient Allah has been with you.*

 

 

______Sam Umma bata san abinda ke tafiya a cikin anguwan ba saboda ita mace ce mai kamun kai,sam bata ɗaya daga cikin mata masu bin gidajan maƙota ace wannan ace wannan,hakan yasa da yawa suke bata girma dan kuwa idan ka ganta gidan maƙota tofa jaje ta tafi ko kuma barka, hakan yasa ko yau babu abinda suka ji daga batun raba kayan abinci.

 

Zaune suke Umma tana tsafewa *Ummi* kai, jin sallamar ta yasa duk suka amsa a lokaci guda tare da duban kofar shigowa gidan don ganin waye bakon da suka yi din a daidai wannan lokacin. Shigowa gidan na ta yayi daidai da lokacin da Umma ta ja wa *Ummi* suma tana cewa,”ai gashi nan lalaci yasa duk gashinki ya zube saboda rashin kitso”.

Wani irin farinciki ne ya luluɓe mummy bisa ganin yarinyar da kullum sai ta jajanta a cikin ranta cewa a ina ne za ta sake ganinta. *Ummi* kuwa dake zaune sai faman tura baki take jin abinda Ummanta take cewa da ita akan rashin son kitso. Kamar daga dama sai ta tsinkayi muryar da ko shakka babu na matar da tayi musu sallamar ce tana cewa, “a karo na biyu yau ma dai ga shi a na cikin rigima da yarinyar Mummy?” Ta karisa maganar tana dariya kasancewar dama cikin raha ta yi.

Ai *Ummi* ba ta san lokacin da ta isa gurin mummy ba, tsalle tayi ta ɗane jikinta tana murna duk kan su murna suke kamar dama sun saba da juna ne.

 

Umma kuwa tsabar mamaki bakinta kasa rufuwa yayi ganin wannan abin al’ajabin “maman *MUSADDAM* a gidan mu?”

Da gudu *Ummi* ta shiga ɗaki ta ɗauko mata tabarma tare da shimfiɗa mata jiki na rawa ta ɗibo mata ruwa cikin ƙofi mai kyau da tsafta. Yayin da Umma kuma ta kawo mata fura da nonon da ta damawa Abba *Ummi* ta ɗauko ta ajiye gaban mummy ganin za ta ƙara miƙewa yasa Mummy janyo hannun ta share ƙwallar daya gangaro mata tayi don kuwa sosai *Ummi* ta tafi da zuciyar ta tabbas ALLAH shi ne ma ji roƙon bawa, cikin ƙankanin lokaci ga shi ya sake haɗa mu.

 

Ganin yadda mummy tayi shiru kuma ba ta saki hannun *Ummi* ba yasa Umma yin gyarar murya tace, “Hajiya ki yi hakuri wannan yarinyar rawar kai gare ta ba ta ma bari mun gaisa ba”.

Murmushi mummy tayi tace, “ai babu laifi don yarinya tayi rawar jiki don ta ga mummyn ta ko”.

Sosai Umma ta ji daɗin wannan magana da Mummy ta yi wanda hakan ya sanya jin wata matsanciyar kunya gami da dadi sun lullubeta a lokaci sai kawai ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zaren bakin tabarmar kamar mai zane.

Sai da mummy ta sha nonon sannan ta gyara zama tace, “wai dama a unguwan nan kuke ko kuma zuwa kuka yi, ma’ana baku daɗe da zuwa ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button