MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Murmushi ita ma Umma ta yi tace, “eh to…zuwa yanzu dai aƙalla mun kai shekara goma sha biyar a cikin wannan unguwan”.
“Abin mamaki amma ban taɓa ganin ki ba” in ji Mommy.
Caraf *Ummi* tace, “Mummy ai Umma ba ta zuwa ko’ina daga barka sai ALLAH ya tsare na gaba”.
Dariya duk suka yi jin abinda *Ummi* ta faɗa, Umma kuwa duka ta kai mata a baya tana cewa, “baki abin magana”.
Hararar wasa Mummy tayi wa Umma tana cewa, “aikuwa yau da mun kai ki gurin hukuma”.
Sosai suka taɓa hira cike da ƙaunar juna, nan da nan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su kamar sun daɗe da sanin juna. A takaice sai da mummy tayi Sallar Magrib a gidan su *Ummi* ganin haka yasa mummy ta shiga kitchen ta soya Masar da dama jira take yamma tayi ta soya musu, aíkuwa sosai mummy ta ji daɗin wainar musamman ƙamshin manshanun dake tashi a ciki.
Gabaki ɗaya Mummy mancewa tayi cewa tare suke da masu motar abinci a waje don kuwa ta ji dadin haduwar da tayi da su *Ummi* sosai.
Tashi tayi ta fara kakkaɓe kayan ta, sosai jikin *Ummi* yayi sanyi don kuwa lokaci ɗaya ta ji tana masifar son matar, ba ta ankara ba sai jin hannun mummy tayi saman ƙuncinta tana share mata hawaye tace, “mene ne kuma yasa ‘yar Mummy kuka?”
Rungume Mummy tayi tace, “za ki tafi kuma ni ba na so”.
Kuka take sosai harda sheshsheƙa, Umma kam sake baki tayi tana ganin abin mamaki.
Mummy kuwa janyota jikinta tayi tace, “ki daina kuka kin ji ba na so kanki yayi ciwo. Shin yaushe ma za ki zo?”
Ɗago kai tayi ta dubi Mummy tace, “mummy ina?”
“Gida na mana ko ba za ki zo ba?”
Baki na rawa tace, “duk abinda kika ce ba ni da abin cewa mummy na”.
Tsabar jin daɗin maganar *Ummi* sai da Mummy ta shafi gefen fuskarta tace, “ina maraba dake a kodayaushe ‘yata”.
Da haka mummy ta fita ƙofar gidan sosai tayi mamakin ganin yadda gari yayi duhu alamar dare yayi, umartar masu motar tayi da su ba wa su *Ummi* na su”.
Aikuwa Umma tsabar farinciki har ƙwalla sai da tayi.
Da haka suka yi sallama zuciyoyin su kuwa cike da kewar juna.
***********
Ko da *MUSADDAM* ya dawo gida sosai yayi mamakin rashin dawowar mummy, hankalin shi a tashe ya fita daga gidan don zuwa dubo abinda ya tsayar da ita har wannan lokacin.
Yana fita harabar gidan motar su mummy na shigowa, ajiyar zuciya ya sauke yana hamdala a zuciyar sa. Mummy kuwa gabakiɗaya tsabar farinciki bakin ta yaƙi rufuwa sosai *MUSADDAM* ya hango tsantsar farinciki a fuskar mummyn irin wanda tun daddy na raye yake gani to fa irin sa ne yau a fuskar mummy, tana zuwa daf da shi ta riƙo hannunsa tana cewa, “buri na ya gama cika *MUSADDAM* “.
Da mamaki yake binta da kallo yace, “mene ne ya saka ki farinciki haka mummy? Idan zakkar da muka fitar ne ai ba yau ne farau ba, abu ne da tun fil azal muka doru akai Mommy. Idan kuma wani mutum din ne ya zamo silar wannan farinciki naki to fa zan yi masa kyauta mafi tsada a rayuwarsa”.
Kallon sa mummy tayi tace, “ba a yin alkawari fa yayi da ake tsananin farin ciki, haka ba a yanke hukunci yayin da zuciya ta ɗau zafi saboda kar ka furta abinda ba za ka iya cikawa ba. Kar ka damu zo mu shiga daga ciki zaka ji komai”.
Bin ta kawai yake da ido har suka ƙarasa cikin babban falon gidan wanda rabon da su zauna a ciki tun daddy yana raye.
*********
*Ummi* kuwa tun fitar mummy daga gidan take ta faman kuka, duk yadda Umma taso ta Rarrashe ta abu yaci tura, kallonta tayi tace, “yanzu kukan me kike?”
Ɗago jajayen idanuwanta tayi tace, “Umma farinciki ne yayi min yawa ta yadda sam ba na jin dariya kawai za ta wadatar da ni, dole sai nayi kuka, Umma mummy ce fa da kanta tace na zo gidan su a duk lokacin da nake da buƙatar hakan, abu na biyu kuma shi ne ganin *MUSADDAM* kullum a kusa da ni yana iya haifar min da damuwa tunda nasan har abada ba zai taɓa kallo na a matsayin budurwa ba balle kuma a kai ga matar aure, Umma wallàhi sosai nake son sa so irin wanda ni kaina ban san dalili ba, ina masa so irin wacce mahaukaciyar uwa take wa ɗanta, ina masa so irin wadda mayunwacin zaki yake wa namomin dawa, mene ne zan yi don ganin *MUSADDAM* ya dawo mallaki na?”
Sauke ajiyar zuciya Umma tayi tace, “Addu’a kawai ita ce mafita”.
…
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_
1️⃣3️⃣
*Don’t jump in to conclusions. Things aren’t always what they seem. Our conclusions may be logical but they may not be true. By refraining from making the wrong assumptions, we can avoid unnecessary pain & conflict. So don’t be too quick to judge & condemn. Instead, be discerning!*
__________Murmushi *Ummi* ta yi tace, “ALLAH ya amsa addu’ar mu Umma”.
“Amin amin”.
Ko da Abba ya dawo Umma ba ta ɓoye ma sa komai ba domin kuwa wannan yana daga cikin ɗabi’unta duk abinda ya faru bayan fitarsa da zarar ya huta take zayyana masa, wasu yayi mata godiya wasu kuma ya nuna mata kuskuren ta, sosai Umma ta ginu bisa wannan tafarki.
Abba shi ma ya ji daɗin faruwar wannan al’amari kwarai da gaske don kuwa yau yadda ya fita haka ya dawo cikin gidan ko abin Naira biyar bai sayar ba.
(“Uba! Uba!! Uba!!! ALLAH sarki mahaifi ginshiƙin gida, bango majinginar iyalan sa, rumfa mai samar da inuwa ga iyalan sa, zafi, rana, iska, sanyi, haka suke fita domin sama mana abincin da zamu ci, suna so su rintsa amma babu dama, suna su so zauna a gida domin hira da iyalan su, amma ba su isa ba. Mahaifi shi ke cire kuɗi ya saya mana tufafi masu kyau da sheƙi don mu yi kyau ya kasance babu kafar da za a raina mu a tsakanin sa’annin mu, shi kuwa ƙafarsa ko takalma masu kyau babu. ALLAH sarki cikin kuɗin da ya samu yake tura mu makaranta kawai don ganin rayuwar mu ta inganta. Shin wanda yayi maka wadannan abubuwa ya cancanci mantuwa daga gare ka don kawai kana ganin yanzu ka girma kana da abin hannu kuma kana da motar hawa?
Gare ku masu mancewa da iyayen su kawai don ganin kun samu abin duniya, to fa ku sani wallahi yardar ALLAH ba ta samuwa sai da yardar iyaye, kar ruɗin duniya ko kuma ganin kin yi ko kayi aure yasa ki mance da iyayen ki, wallàhi babu wanda zai yi miki/maka ƙwatankwacin soyayyar da suka mana, wallàhi yin biyayya ga iyaye abu ne mai matukar wahalar gaske, amma idan muka tuna da cewa shi kansa ALLAH ya kira biyayyar iyaye a matsayin ibada, hakan ne yasa yin biyayyar ya zamo wajibi gare mu. Saboda haka idan ba ku sani ba to fa wallahi ku sani duk abinda aka ambace shi matsayin ibada to fa ba ƙaramin aiki ba ne ba, don kuwa ba za ka/ki samu aljanna daga zaune ba…. ALLAH yasa mu dace, amin)
Hamdala yayi yana mai ƙara godiya ga ALLAH mahallicin sa, kallo ɗaya Umma tayi masa ta fahimci halin da yake ciki. Murmushi ta yi tace, “karka damu kuma kar ka yi mamaki, domin kuwa ALLAH baya saɓa alƙawarin sa, kuma yayi wa dukkannin bayin sa da suka yi imani da shi alkawarin cewa, “zai zama gatan su idan har suka sa yarda da yaƙini akan sa, saboda haka ka ƙwantar da hankalinka, godiya ya kamata mu yi ma sa”.