MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Sauke ajiyar zuciya Abba yayi yace, “samun ki babbar nasara ce a rayuwa ta. Alhamdulillahi ala kulli halin. Su kuma Allah ya saka musu da alheri, ke ma kuma Allah ya miki albarka”.
Sunkuyar da kai Umma tana mai cike da jin kunya, tace amin.
*********************
Kallon Mummy *MUSADDAM* yayi yace, “Mummy kin yi shiru kuma ba ki faɗa min komai ba”.
Har yanzu dai farin ciki ne cike da fuskar ta tace, “daina hanzari insha Allahu zuwa gobe zan yi maka bayani”.
Ba tare da gardama ba ya tashi ya nufi ɗakin sa bayan yayi mata sallama, dukda kuwa zuciyar sa cike take da tambayoyi da kuma burin son sanin abinda ya saka ta farin ciki haka.
Yana fita daga ɗakin Mummy ta ɗauko hoton daddy dake manne da bangwon ɗakin, ajiyar zuciya mai ƙarfi Mummy ta sauke haɗe da lumshe idanuwan ta. Wasu irin hawaye ne masu zafin gaske suka shiga zarya a ƙuncinta, sake kallon hoton tayi tace, “na yi kewarka mijina, annurin zuciyata. Tabbas rashinka abu ne da babu wani abin da zai iya taɓa maye gurbin sa a rayuwata har zuwa lokacin da ni ma za a dauki nawa ran na koma izuwa ga inda zan riskeka. Yau ga shi na cika maka alƙawarin da na daukar maka akan ɗan mu *MUSADDAM* hasken idaniyarka. Ka buƙaci na dau alkawarin aurawa *MUSADDAM* yarinyar da ta fito daga gidan mutunci kuma ka hore ni da kar na yarda na aurawa *MUSADDAM* mace sangartacciya, kai ne kace na tabbatar *MUSADDAM* ya auri yarinya ma’abociyar addini da sanin ya kamata kuma wacce zai so ta ita ma ta so shi fiye ma da yadda yake son na ta…”
“…ALLAH cikin ikon sa na samo ta, kuma ina da yaƙini akan *MUSADDAM* cewa zai yi na’am da wannan zabi na zai so ta fiye da tunanin mai tunani, sai dai kuma yuwuwar auren na su yana a hannun rabbi, haka Mummy tayi ta sambatu iri daban-daban tayi kuka sosai a wasu lokutan kuma tayi murmushi.
*WANE NE MUSADDAM?*
*MUSADDAM* ya kasance ɗa ga Alhaji Muhammad Ali mai shinkafa. Shi kuma Alhaji Muhammad ɗa ne daga cikin ahalin gidan Malam Ali Mai Dabino, Malam Ali Mai Dabino ya kasance yana da mata biyu Halima ita ce matar sa ta farko, ALLAH cikin ikonsa tunda Ali da Halima suka yi aure ko ɓatan wata Halima ba ta taɓa yi ba sosai hakan yasa ‘yan uwansa suka sako shi gaba ala dole sai ya ƙara aure, jin hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi wa Halima ba. Abin mamaki sai ga ta cikin hidimar bikin mijinta dumu-dumu.
Wannan lamari sosai ya taɓa zuciyar dangin nasa, tuni suka fara hasashen ko dai akwai wani kulli ne a ƙasa?
ALLAH cikin ikonsa kuwa aka yi biki cikin kwanciyar hankali ba tare da anyi hayaniya ba, Halima da kanta ta raka malam Ali har bakin ƙofar ɗakin amarya, sannan tayi masa addu’ar samun abinda suka daɗe suna nema cikin daran nan.
Allah mai kyauta da kari! Sai ga shi cikin kudurar Ubangiji, Salma ko wata biyu ba a rufa ba ta samu ciki, gane faruwar wannan al’amari kuwa a ranar sai da Halima ta bar gidan don tsabar cin fuska da nuna tsana da ake mata, sosai ran malam Ali ya ɓaci don haka yayi gargaɗi haɗe da jan kunne kan a fita harkar matan sa.
Wannan gargaɗi da yayi shi ne ya kara rura wutar ƙiyayya tsakanin dangin Ali da Halima.
ALLAH cikin ikon sa Salma tana kai wa wata goma da aure ta haifi ɗanta fari ƙyaƙyaywan gaske.
Sosai Halima ta nuna tsantsar farincikin ta game da wannan babbar kyauta da ALLAH ya yi musu.
Ranar suna yaro ya ci sunan ƙanin mahaifin Malam Ali wato Sale.
Tunda suka yi arba’in kullum Sale a hannun Halima yake, har sai idan ya buƙaci nono take miƙa shi ga mahaifiyar sa, dukda ran Salma ba ya so sam babu inda ta iya don kuwa Malam Ali yayi mata gargaɗi da cewa ko da wasa tayi wa Halima gorin haihuwa wallàhi a bakin auren ta, hakan yasa ta tsuke bakin ta ba don ba ta da abin faɗa ba.
Salma tana yaye Sale ALLAH ya ƙara azurtata da samun wani cikin daga nan komai na Sale ya koma hannun Halima, kashinsa, fitsari, wanki duk ita ce take kula da su.
Bayan an kuma shafe wata tara Salma ta haifo kyakkyawar ɗiyarta mai kama da ita kamar an tsaga kara.
Nan fa dangin miji aka samu abin faɗa, gori babu irin wanda Halima ba ta sha ba. Ganin hakan bai sa ta shiga damuwa ba sai suka shiga zuga Salma akan ta ƙarɓe ɗanta idan ba haka ba tana ji tana gani zai tashi yana mata kallon kishiyar uwa a maimakon uwa.
Jin wannan batu yasa Salma ta tayar da hayaniya ranar suna, ala dole sai an mayar mata da ɗan ta, Halima tana cikin rabawa jama’a abinci ta fara jiyo surutai da hayaniya yana tashi cikin ɗakin Salma….
Ajiye abincin tayi ta nufi ɗakin, sai dai tana zuwa bakin ƙofar kunnuwanta suka jiyo mata abinda sai da ta ji kamar za ta faɗi. Ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauko duk wani abinda ta san mallakin Sale ne ta damƙa musu, aíkuwa nan da nan jikin kowa yayi sanyi don kuwa ba haka suka so ba. Sun so ne su ga ƙarshen haƙurin na ta.
Ko da Malam Ali ya dawo nasiha Halima tayi masa akan hakuri da kuma ribar da mai haƙuri yake samu muddin domin ALLAH yayi ba saboda wata manufa ba.
Sosai jikinsa yayi sanyi.
Wasa wasa tun daga wannan rana Halima ta fara zazzaɓi tun tana ɗaukar abin matsayin damuwar da ta sawa kanta ne, har dai abin ya fara cin karfin ta, ko da suka tafi asibiti gwajin farko aka sanar musu da cewa ciki gare ta, zo ku ga murna gurin malam Ali a wannan rana, ji yake kamar wannan shi ne ciki na farko da aka taɓa yi a gidan sa, kulawa sosai Halima take samun gurin mijinta, saɓanin dangin miji wanda ko ALLAH ya raba lafiya ba su zo sun yi mata ba.
Watarana da daddare Halima ta farka da wani irin matsanancin ciwon mara, cikin hanzari aka nufi asibiti da ita da cikin gaggawa aka shigar da ita ciki ganin yadda jini yake zuba mata kuma da alamu kamar haihuwa ce….
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
*_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_*
1️⃣4️⃣
*Remind yourself that everything is temporary; nothing lasts. You’re on a journey. You’ve not reached your final destination yet. An eternal abode awaits. The Hereafter. So quit stressing over everything that happens. Let the Almighty take over after you’ve done your best!*
________Halima ta sha wahala sosai, ALLAH cikin ikon sa ta haifi ɗanta kyakkyawan gaske, kiran malam Ali ta sa aka yi, riƙe masa hannu tayi cikin sauri ya janye hannunwan sa jin yadda hannuwan ta suka ɗauki sanyi kamar an dora masa ƙanƙara.
Murmushi tayi tace, “zan tafi, amma ka sani zan damƙa maka amanar ɗana a hannun ka, don ALLAH ka kula min da addinin sa, ka tabbatar ka yi iya yinka wajen ganin ya samu tarbiyya, ka min alƙawarin za ka ba shi ilimi daga na islamiya har na boko, wannan shi ne kawai abinda nake buƙata daga gare ka….”
Share hawayen fuskar sa malam Ali yayi yace, “na yi miki alƙawari, amma ki sani cuta ba mutuwa ba ce, insha ALLAH za ki warke mu koma gida tare kin ji?”
Murmushi kawai tayi masa tace, “ka je ka kira Dr ya zo ya ba mu sallama gida nake son komawa”.