MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Da farin ciki malam Ali ya fita daga ɗakin yana fita Halima ta fara kwararo aman jini kan a ɗauki wani lokaci mai tsawo tuni rai yayi halin sa.
Sosai malam Ali ya kaɗu da jin cewar Halima tana dauke da ciwon zuciya kuma ta kai a ƙalla shekara ɗaya da fara zuwa amsar magani sai dai kuma rashin samuwar kwanciyar hankalin yasa wannan ciwo ya zama ajalin ta.
Cikin ƙanƙani lokaci gari ya ƙaraɗe da zancen mutuwar Halima da kuma faɗin ta sanadiyar haihuwa ne ta mutu….
Tun kan malam Ali ya shigo gida Salma ta samu labarin mutuwar Halima sosai tayi farin ciki da jin wannan batu, sai dai kuma ganin malam Ali ɗauke da jariri yasa ta ji babu daɗi.
Tun a gaban jama’a ta fara sayar da hali.
Sai da komai ya lafa sannan ya samu Salma da zancan rike yaron nan wanda yaci suna Muhammad a matsayin ɗan da ta haifa a cikin cikin ta.
Nan kuwa Salma ta daka tsalle tace, “ba dai ita ba”.
Duk yadda ran malam Ali ya kai ga sanyi ranar sai da ya ɓaci kawai ya danne ne.
Ganin jariri yana neman mutuwa yasa inna maƙwabciyar su ta kaɗa madara na yara ta kaiwa malam Ali haɗe da yi masa bayanin yadda ake ba wa yaro.
Sosai malam Ali ya yi mata godiya, haka rayuwa taci gaba da garawa yau daɗi gobe akasin sa, idan nace zan tsaya baku labarin irin rayuwar da Muhammad yayi na kunci da mairaici ina mai tabbatar muku sai kunyi kuka saboda tsabar wahalar da ya sha, kuma zuwa yanzu kowa yasan irin wahalar da ake sha hannun gurɓatacciyar kishiyar uwa…
Zaune na hango wani kyakkyawan yaro dukda kuwa shekarun sa ba za su gaza tara ba, amma duk wani cikar kyau da ƙwarjini da cikar kamala sun fito raɗau-raɗau a jikin wannan yaron. Zaune yake duk kayan jikinsa sun jeme, sunyi kaca kaca da datti. Sumat kansa kuwa har wani harhaɗewa suka yi da juna suka cure guri ɗaya saboda rashin kula da kuma aski.
Hawaye yake zubarwa musu tsananin ciwo. Sa hanu malam Ali yayi ya share masa hawayen dake zuba a saman kuncin sa. Babu ma’anar ɗagowa dan ganin wanene don kuwa duk duniya babu mai son sa sama da Mahaifinsa.
Kallon sa malam Ali yayi yace, “Muhammad mene ne ya saka ka kuka?”
Kamar kullum yau ma dai amsar sa ɗaya ce, “babu kowa kawai kewar inna ta nake”.
Share masa hawaye yayi dukda kuwa yasan cewa ba gaskiya Muhammad ya faɗa masa ba, riƙe hannu juna suka yi har cikin gida, ganin shigowar su yasa Salma ta miƙe jiki na rawa don kuwa duk a tunanin ta Muhammad ya faɗawa malam Ali abinda tasa ‘ya’yan ta suka masa ne.
Ganin yanayin da ta shiga kawai ya sake tabbatarwa malam Ali abinda suka yi wa Muhammad ba ƙaramin abu ba ne.
Jinjina al”amarin yayi yana mai yanke hukunci da shi kansa kawai ya san me ya hakaito akan al’amarin.
Kamar yadda duk kuka sani malam Ali yara uku gare shi Sale, Suwaiba, sai Muhammad wanda ya kansance ɗa ga Halima.
Tun daga wannan haihuwar Salma ba ta sake samun haihuwa ba. Yaran Salma sun taso cikin wani irin rayuwa na rashin kwaɓa, babu mai saka su haka babu mai hana su, ta kai ta kawo ko maganar mahaifin su ba sa saurara.
Hakan yasa ko da ya sa su a makarantar kin zuwa suka yi, babu yadda Malam Ali bai yi ba don ganin rayuwar su ta inganta, amma ina.
Washe garin ranar da asuba ya ɗauki Muhammad da ɗan jakar kayansa wanda a yanzu ba ta da maraba da buhun shara.
Makarantar kwana malam Ali ya saka Muhammad, cike da kwazo da Nasara Muhammad yayi karatun sa har zuwa matakin secondary, a can ƙauye kuwa duk wanda ya tambayi malam Ali lamarin Muhammad amsa ɗaya yake basu, “Muhammad yayi tafiya”.
Tun jama’a suna yarda har abu yaci tura, Salma gida gida ta rinƙa bi da zancan mijinta ya sayar da ɗan sa na gurin matar sa ta farko.
Duk da malam Ali ya san abinda take sam hakan bai sa ya damu ba, saboda shi ya san inda ɗansa yake kuma duk ƙarshen watan duniya sai ya tafi birni ya duba Muhammad wanda zuwa yanzu ya zama saurayi abinsa.
Ganin yadda dangin Halima suka fara ɗaukar jita jitar mutanen gari ne ya sa malam Ali ya ɗauki babban wan su Halima ya kai shi inda Muhammad yake karatu, a ranar sun yi kuka sosai don kuwa a kamanin Halima babu inda Muhammad ya rage, sai dai kasancewar sa namiji hakan yasa kai tsaye ba zance kamar ƴan biyu ba.
Muhammad yana kammala karatun sa na secondary cikin nasara ya samu gurbin karatu a jami’a.
Lokaci wawan abu ne yakan zo ya tafi mana da abubuwa da muke so, haka mutuwa ba ta jiran kowa, wata rana a hanyar malam Ali na zuwa duba Muhammad kamar yadda ya saba a kowane ƙarshen wata motar su tayi hatsari ba tare da bata lokaci ba kuna motar ta kama da wuta kaf cikin motar babu wanda ya rayu.
Tabbas wannan mutuwa ta girgiza jama’ar garin don kuwa malam Ali mutumin kirki ne ba shi da abokin faɗa sam.
Muhammad kuwa ganin kwana biyu babu malam Ali babu labarin sa yasa ya kira wan Halima inda ya faɗa ma sa dalilin rashin ganin mahaifin na sa, sosai Muhammad yayi kuka jin rasuwar mahaifin sa.
Babu shiri ya baro makaranta ya dawo gida, ranar kuwa ina wuta Salma ta jefa Muhammad, a farko ma cewa tayi, “sam wannan mai kama da Muhammad ne ai Muhammad ya daɗe da mutuwa.
Ganin yadda mutanen gari suka yi caaa akanta yasa ta sauko kuma ta amince cewa Muhammad ne.
Ko da aka yi zancen raba gado, Salma cewa tayi baza’a raba ba sai Muhammad ya gama karatu.
Masifar ta yasa babu wanda ya ja da ita daga nan rayuwa ta sake sauyawa sosai Muhammad yake shan wahala a makaranta dan wani lokacin ma da yunwa yake kwana.
Kasancewar Muhammad mai ilimi da hazaƙa yasa mata da yawa suke son sa, kamun kan sa da dattakun sa yasa hatta malamai suke son sa.
Kamar yadda soyayar Muhammad yayi wa mata tsaye a zuciya tofa hakance ta kasance a zuciyar ɗiyar ɗan majalisan dake ci a lokacin, mai suna Ni’ima.
Ni’ima ta kasance yarinya natsatsiya wacce kowa ke yabo da kuma jin sha’awar halin ta duk da kuwa yadda mahaifin ta yake da kuɗi sam hakan bai saka ta ɗorawa kanta girman kai ko kuma wani ɗagawa ba.
Sosai take jin son Muhammad ga shi kuma ita sam ba za ta taɓa iya furta masa ba, abu kamar wasa har ciwo sai da Ni’ima tayi ganin yadda duk hankalin iyayenta ya tashi yasa ta faɗa musu abinda ke damunta.
Cikin yardar ALLAH kuwa mahaifinta yayi bincike sosai akan Muhammad, ya ji daɗin jin halayen sa nagartattu ne, sai dai shi ba ɗan kowa ba ne.
Jin labarin halin da Muhammad yake ciki yasa mahaifin NI’IMA cikin dabara yayi magana da ɗaya daga cikin malaman makarantar wanda aka faɗa masa cewa shi da Muhammad akwai shaƙuwa sosai a tsakanin su da farko ya so ya ɓoye masa amma jin furucin da malamin yayi na cewa, “ya san duk abinda ke faruwa kuma kamar yadda Ni’ima take mutuwar son Muhammad ,to fa haka shi ma kansa Muhammad ɗin yana mutuwar son ta.
Sosai mahaifin NI’IMA yaji daɗin wannan al’amari,cikin ƙanƙanin lokaci soyayya mai ƙarfi ya shiga tsakanin Muhammad da Ni’ima.
Tun kafin su gama makarantar Kasancewar Muhammad kasuwanci ya karanta yasa mahaifin Ni’ima ya fara ɗaurashi akan harkar kasuwancin sa,gaskiya da riƙon amanar da Muhammad ya nuna, yasa aka sakar masa ragamar abubuwa da dama yana juyawa.
Koda mahaifin Ni’ima ya buƙaci suyi aure Muhammad ɓai boye masa duk wasu abubuwa daya kamata ace ya sani dangane dashi ba,kama daga rashin muhalli.
Sosai mahaifin Ni’ima ya jinjina zancen da kuma ya ƙara tabbatar wa da kansa cewa Ni’ima tayi zabe na gari.