MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Kwantar masa da hankali yayi yace, “ka mance da batun muhalli, ni zan sama muku inda zaka zauna ai kai ma kamar ɗane a guri na, abinda nake da buƙata daga gunka kawai sadaki daga shi babu ƙari.
Sosai wannan abu ya faranta ran Muhammad, cikin ƙwanaki ƙalilan ya tafi ƙauye dan shaidawa danginsa, abinda ya fara cin karo da shi sai da ya ji inama bai dawo gida ba, ƴaƴan Suwaiba ya tarar da wani ƙaton garɗi kwance saman katifar mahaifinsu suna baɗala, rintse idanuwan sa yayi da karfi jin yadda kansa ya sara masa lokaci ɗaya.
Abin takaicin kuma inna Salma tana zaune tana ɓarar agushi, ko alamar damuwa babu a fuskar ta, “kenan abinda yanzu gidan mu ya koma kenan”.
Gashi Sale babu abinda yake a cikin garin sai yiwa mata fyade da sace-sace.
Ranar kuwa Muhammad yayi kuka sosai, kukan rasa mahaifa, tashi yayi ya shaidawa wan Halima halin da ake ciki, cike da murna suka nufi gidan su Muhammad da murna inna Salma ta karɓe shi sai dai jin raba gado yake so ayi a bawa Muhammad kason sa saboda yana so yayi aure yasa gabakiɗaya ta nemi farin cikinta ta rasa, aikuwa nan fa ta fara musu ruwan bala’ai da zage zage babu shiri suka bar gidan hakanan ita kuwa ta rako su tana zazzaga bala’i……
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_
*Sometimes even those with good intentions can lead you down the wrong path. Tread carefully. Watch where you’re heading. Learn to listen to the Almighty more than you listen to people. Trust Him more than you trust people. People are fallible. He isn’t!*
__________Yayan Halima shi yayi kudumbala ya ba shi kudin sadakin. Sosai Muhammad ya yi farinciki da samuwar kuɗin sadakin ba tare da bata lokaci ba kuwa ya kai gidan su Ni’ima inda aka sanya lokacin aure nan da wata ɗaya.
A nan ne kuma zuciyar Muhammad ta sake cika da jin kewar iyayensa. Rintse idanuwan sa yayi yace, “ina ma a ce kina tare da ni a yanzu Umma!? Na san ko ba komai zan samu sassaucin kuncin da nake ji a raina. Ina ma zan wai ga na ganka a tare da ni Abba na, wallàhi na san da duk wannan kuncin ba zan gan shi ba. Yaya Suwaiba ina miki fatan shiriya daga ALLAH mahaliccin kowa da komai, haka kai ma yaya Sale. Inna Salma ke ma ina miki fatan ki gane gaskiya tun kafin lokaci ya kure miki.
Haka dai Muhammad ya zauna yayi ta addu’ar shiriya ga ƴan uwan sa idanuwansa na ta zubar da hawaye.
Yau da gobe kayan ALLAH. Haka aka ɗaura auren Muhammad da Ni’ima cikin kwanciyar hankali aka kai ta makeken gidan su mai kyau da tsari, ganin wannan gida sai da Muhammad ya zubda hawaye saboda a cikin rayuwarsa ko da wasa bai taɓa kawowa a ransa cewa zai mallaki wannan gida a matsayin nasa ba.
Cikin tsafta da aminci suke gabatar da rayuwar auren su, wata rana Ni’ima ta buƙaci su tafi garin su don ta saba da ƴan uwan sa. Babu musu kuwa ya amince suka tafi don kuwa shi ma abin yana ransa da ma lokaci kawai yake jira.
Ko da suka tafi garin sosai abubuwa suka ba shi mamaki ganin yadda Inna Salma ta ƙara lalacewa da son kuɗi. Suwaiba kuwa ta ƙanjame ta rame saboda fama da take da matsananciyar jinya, ga shi Sale yana magarƙama sanadiyar satan da yayi duk dauriyar da Muhammad yake da shi sai da ya zubda hawaye ganin yadda uwa tayi burus da rayuwar ƴaƴan ta.
Ni’ima kuwa tsabar tausayi sai da ta yi kuka har idanuwanta suka kumbura, ranar suka juya suka koma tare da Suwaiba suna zuwa ba su tsaya a ko’ina ba sai asibiti taimakon gaggawa aka shiga ba ta.
Nan da nan Ni’ima ta yiwa babanta waya ta faɗa masa zancen Sale cikin awanni aka sake shi. Sosai Muhammad yayi mata godiya bisa ga wannan hidima ta take ma sa shi da ƴan uwansa.
Kallo ɗaya za ka yiwa Sale ka fahimci ba ƙaramar wahala ya sha cikin wannan magarƙamar ba.
Godiya sosai yayi wa ƙanin nasa lokacin da ya fahimci yadda aka yi ya fito daga magarkamar. Bayan likitoci sun shawo kan matsalar ciwon Suwaiba ta dawo hayyacinta sosai ne suka nufi gida bagaki ɗayan su. Nan fa Sale da Suwaiba suka shiga mamakin ganin gidan da ƙanin bayan su yake zaune, nan da nan kuwa ciwon ƙyashi wannan bakin kishi da hassadar tasu ta motsa. Sai dai fahimtar cewa yanzu yayi musu nisa yasa suka kwantar da kansu kamar babu wani abu a ƙasan ran su.
Koda mahaifin Ni’ima ya zo nasiha yayi musu sosai mai ratsa jiki, sannan yayi musu alkawarin ba wa Sale jari wanda idan ya koma gida zai rinka juyawa, ba tare da ya saka ido akan kayan jama’a ba, Suwaiba ma haka kuɗi ya ɗauka ya ba ta masu yawan gaske wanda za ta samu ta ɗan dogara da kanta kafin ALLAH ya zaɓar mata mijin aure.
Ko da Sale da Suwaiba suka koma gida suka ba wa mahaifiyar su labari, aikuwa nan Inna Salma ta buga kasa tare da rantsuwar cewa sai ta ga bayan Muhammad da ahalin sa. Amma fa ta kitsa musu cewa dole su yi taka tsantsan don kuwa yanzu duk wasu munanan halayensu dole su boye don kar ganin rashin sauyin na su yasa Muhammad yayi watsi da su a karshe, ma’ana dai suka shirya cewa za su yi tuban muzuru.
******
ALLAH cikin ikon sa Muhammad suna cika shekara ɗaya da aure Ni’ima ta haifo ɗanta lafiyayye kuma kyakkyawan gaske. Ranar sunan kuwa an sha buduri da shagalin suna sosai irin wanda ba a taba yin irinsa ba don kuwa ɗan majalisa wato mahaifin Ni’ima buɗe bakin aljihunsa yayi a kayi ta ɓarin kuɗi sai dai ba irin na albozarancin nan ba a ka sha shagalin komai a wadace yaro kuwa ya ci suna *MUSADDAM* wanda hakan kuma suna ne na marigayi Janar Musaddam Kambiya wato kakan Ni’ima, mahaifin dan majalisa. Sosai kuwa mutane suka yi ta mararin wannan suna don kuwa suna ne na gwarzon sadauki daga mazan jiya wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidima ga kasa. Baya ga haka suna ne mai matukar daɗi da tsayuwa a rai.
ALLAH cikin ikon sa tunda aka haifi *MUSADDAM* ƙofofin arzikin Muhammad wato Mahaifinsa suka bubbuɗe kan kace me tuni sunan sa ya shahara, a matsayin babban ɗan kasuwa. Hajjinsa na farko sai da ya biya wa wan mahaifiyar sa shi da matansa biyu. Abin mamaki duk yadda Muhammad yayi da inna Salma akan ya biya mata hajji saboda ta shirya su tafi tare tsohuwar nan ki tayi.
Don kuwa yana tunkararta da batun sai ta miƙe karaf tana kara gyara daurin zaninta gami da cewa, ” Ɗan nan bawai ban yi farinciki ba ne, a’a sam na yi farinciki kuma na yi burin a ce Halima tana raye yau ta ga ɗanta cikin wannan irin daula, kai nasan sai tayi farin ciki sosai da sosai…”
“…Amma sai nake ga gaskiya ba zan iya zuwa Hajjin bana ba, saboda ka ga ciwon ƙafa yana damuna, ga kuma rashin kuɗin kashewa gidan nan babu abinci…” za ta kare magana ya dakatar da ita yana cewa, “inna karki damu ALLAH yasa hakan shi ne mafi alkairi, zan ba ki kudi masu ɗan yawa wanda zaki rinƙa juyawa har mu je mu dawo, kayan abinci kuma yana bayan mota yanzu za’a shigo dashi in Sha ALLAH”.
Kukan ƙarya inna Salma tasa tana cewa, “ALLAH ya jiƙan ka malam”.