MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Nan da nan Ni’ima ta yiwa babanta waya ta faɗa masa zancen Sale cikin awanni aka sake shi. Sosai Muhammad yayi mata godiya bisa ga wannan hidima ta take ma sa shi da ƴan uwansa.
Kallo ɗaya za ka yiwa Sale ka fahimci ba ƙaramar wahala ya sha cikin wannan magarƙamar ba.
Godiya sosai yayi wa ƙanin nasa lokacin da ya fahimci yadda aka yi ya fito daga magarkamar. Bayan likitoci sun shawo kan matsalar ciwon Suwaiba ta dawo hayyacinta sosai ne suka nufi gida bagaki ɗayan su. Nan fa Sale da Suwaiba suka shiga mamakin ganin gidan da ƙanin bayan su yake zaune, nan da nan kuwa ciwon ƙyashi wannan bakin kishi da hassadar tasu ta motsa. Sai dai fahimtar cewa yanzu yayi musu nisa yasa suka kwantar da kansu kamar babu wani abu a ƙasan ran su.
Koda mahaifin Ni’ima ya zo nasiha yayi musu sosai mai ratsa jiki, sannan yayi musu alkawarin ba wa Sale jari wanda idan ya koma gida zai rinka juyawa, ba tare da ya saka ido akan kayan jama’a ba, Suwaiba ma haka kuɗi ya ɗauka ya ba ta masu yawan gaske wanda za ta samu ta ɗan dogara da kanta kafin ALLAH ya zaɓar mata mijin aure.
Ko da Sale da Suwaiba suka koma gida suka ba wa mahaifiyar su labari, aikuwa nan Inna Salma ta buga kasa tare da rantsuwar cewa sai ta ga bayan Muhammad da ahalin sa. Amma fa ta kitsa musu cewa dole su yi taka tsantsan don kuwa yanzu duk wasu munanan halayensu dole su boye don kar ganin rashin sauyin na su yasa Muhammad yayi watsi da su a karshe, ma’ana dai suka shirya cewa za su yi tuban muzuru.
******
ALLAH cikin ikon sa Muhammad suna cika shekara ɗaya da aure Ni’ima ta haifo ɗanta lafiyayye kuma kyakkyawan gaske. Ranar sunan kuwa an sha buduri da shagalin suna sosai irin wanda ba a taba yin irinsa ba don kuwa ɗan majalisa wato mahaifin Ni’ima buɗe bakin aljihunsa yayi a kayi ta ɓarin kuɗi sai dai ba irin na albozarancin nan ba a ka sha shagalin komai a wadace yaro kuwa ya ci suna *MUSADDAM* wanda hakan kuma suna ne na marigayi Janar Musaddam Kambiya wato kakan Ni’ima, mahaifin dan majalisa. Sosai kuwa mutane suka yi ta mararin wannan suna don kuwa suna ne na gwarzon sadauki daga mazan jiya wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidima ga kasa. Baya ga haka suna ne mai matukar daɗi da tsayuwa a rai.
ALLAH cikin ikon sa tunda aka haifi *MUSADDAM* ƙofofin arzikin Muhammad wato Mahaifinsa suka bubbuɗe kan kace me tuni sunan sa ya shahara, a matsayin babban ɗan kasuwa. Hajjinsa na farko sai da ya biya wa wan mahaifiyar sa shi da matansa biyu. Abin mamaki duk yadda Muhammad yayi da inna Salma akan ya biya mata hajji saboda ta shirya su tafi tare tsohuwar nan ki tayi.
Don kuwa yana tunkararta da batun sai ta miƙe karaf tana kara gyara daurin zaninta gami da cewa, ” Ɗan nan bawai ban yi farinciki ba ne, a’a sam na yi farinciki kuma na yi burin a ce Halima tana raye yau ta ga ɗanta cikin wannan irin daula, kai nasan sai tayi farin ciki sosai da sosai…”
“…Amma sai nake ga gaskiya ba zan iya zuwa Hajjin bana ba, saboda ka ga ciwon ƙafa yana damuna, ga kuma rashin kuɗin kashewa gidan nan babu abinci…” za ta kare magana ya dakatar da ita yana cewa, “inna karki damu ALLAH yasa hakan shi ne mafi alkairi, zan ba ki kudi masu ɗan yawa wanda zaki rinƙa juyawa har mu je mu dawo, kayan abinci kuma yana bayan mota yanzu za’a shigo dashi in Sha ALLAH”.
Kukan ƙarya inna Salma tasa tana cewa, “ALLAH ya jiƙan ka malam”.
Inna Salma ba ta tsaya ko ina ba sai gurin bokan ta inda ta zayyana masa abinda yake tafe da ita.
Kusan mintuna goma ya dauka yana bincikensa na iska kafin yace, ” Salma na faɗa miki tun wannan yaron yana cikin cikin mahaifiyar sa cewa, “ba fa za ki taɓa samun nasarar raba shi da rayuwar sa ba, saboda haka ki koma gida ki zubda makaman yaƙin ki kawai shi ne mafita”.
Hararar sa tayi tace, “kawai kace min ba zaka iya ba, sai na kwana da sanin cewa yanzu lokaci ba ya tsaginka mtsssss aikin banza kawai”.
Murmushi bokan yayi yace, “ba ki tambaye ni dalili ba kin hau masifa Salma”.
Hararar sa tayi a karo na biyu tace, “faɗa min dalilan naka ina sauraro”.
Murmushin takaici bokan yayi yace, “saboda ya riƙe ALLAH da Manzon sa, mutumin nan yana cikin azkar ɗin safe da yamma ba sa wuce shi, sannan ba ya ga haka shi ne yake jiran lokaci sallah ba ita ke jiran sa ba domin yana yinta cikin lokaci. Shin wa ya faɗa miki cewa akwai wanda lokaci yake tsagin shi a rayuwar nan bayan shi kan shi rai da muke kuri da shi watarana zai bar gangar jikinmu m, ya koma ga mahaliccinsa. Ina mai sake gargaɗin ki da ki koma ki zubda makaman yaƙin ki don kuwa nima daga yau na bar harkar bokanci daga nan har zuwa ranar da ALLAH zai raba rai na da gangar jikina”.
Tashi yayi ya fara ciccire kayan jikinsa yana watsarwa sai dai kash, ya mance cewa lokaci baya jiran kowa wani irin giftawar farin haske ya gani ta gaban goshin sa, aikuwa nan da na ya zuɓe a ƙasa duk yadda boka yayi don ya samu yayi kalmar shahada ko kuma neman tuba ina abu yaci tura banda tattauna harshe babu abinda yake ,har rai yayi halin sa.
Ganin abinda ya faru da boka yasa Inna Salma fallawa a guje ta bar gurin jiki na rawa….
Koda inna Salma ta isa gida samun guri tayi ta zauna tana tunanin wannan al’amari.
ALLAH cikin ikon sa kuwa Muhammad da iyalan sa, suka lula ƙasa mai tsarki.
Tun daga wannan lokaci ALLAH ya buɗewa Muhammad hanyar arziki, kullum ƙofofin alhairai sake buɗe masa suke domin kuwa shi ma kullum cikin kyautatawa na ƙasa da shi yake ba tare da gajiyawa ba.
Kamar yadda Inna Salma ba ta huta da zuwa gun bokaye ba, haka shi ma Muhammad da iyalansa kullum cikin neman tsari suke gurin ALLAH mahaliccin kowa da komai.
Hakan yasa ko da sau ɗaya ba ta taɓa samun nasara akan su ba.
Sai da *MUSADDAM* ya kai shakara tara kafin suka sake samun wani cikin, sai dai kuma izuwa wannan lokacin kaf faɗin garin babu lungu da saƙo da sunan Alhaji Muhammad mai shinkafa bai kewaya ba.
ALLAH cikin ikon sa kuwa Ni’ima ta haifo ɗiyarta kyakkyawa mai kama da ita tsaf kamar an tsara kara, ranar suna yarinya ta ci suna *SAFNAH*.
Bayan wata ɗaya da haihuwar Safnah, Ni’ima ta matsa lalle fa tana son zuwa ƙauyen su Muhammad duk yadda Muhammad yaso fahimtar da ita tarin hidimar dake gaban sa amma sam Ni’ima taƙi saurara sosai abin ya ba wa Muhammad mamaki dan kuwa a tsayin rayuwar su a tare ba ta taɓa masa musu ko kuma jayya ba.
Hakan yasa ya aminci suka shirya. A ranar washegarin tafiyar ta su a can kasuwa ya rinƙa yiwa mutane kyauta da alherai iri-iri. Duk wanda Muhammad ya san akwai wata ƴar tsama a tsakanin su sai da ya ya roƙesu gafara duk kuwa da cewa da yawansu din ma shi ne yake da gaskiya.
Daga nan Alhaji Muhammad bai tsaya ko’ina ba sai gidan marayu kamar yadda ya saba zuwa. Nan ma sosai yayi musu abin arziki, a ranar sai da ya basu kyautar sama da miliyan ɗaya wanda adadi ne da a baya bai taba ba wa gidan kamar hakan ba.
Su kansu duk da ya saba musu kyauta,amma abin sai yake basu mamaki yanmdda yayi ta jan yara da wasa, wata yarinya daga cikin su wacce ba ta da ido, ma’ana makauniya ce har Alhaji Muhammad zai shiga motar sa cikin sauri ta laluɓa ta rike masa ƙafa da mamaki ya juya yake kallon ta tare da dafa kanta yace, “Nuriya kina lafiya?”