MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“Lafiya kalau Baba,”
Alhaji Muhammad gabakiɗaya jin sunan da ta kira shi da shi yasa ya ji tsigar jikin sa duk sun mimmiƙe, fashewa da kuka yarinyar tayi tana ƙara ja masa ƙafa, kwantar da muryar sa Alhaji Muhammad yayi yace, “kina buƙatar wani abu ne?”
Girgiza kai wacce ake kira Nuriya tayi tace, “a’a Baba ai ka gama bani komai tunda ka ba ni abincin da zan ci, kuma ka gina min gurin da zan kwana, sannan ka gina min makarantar da zan yi karatu duk da kuwa bana gani. Baba kar kayi tafiyar nan dan ALLAH”.
Cikin sauri Alhaji Muhammad ya kalle ta fuskar sa cike da tsantsar mamaki yace, “wa ya faɗa miki cewa zan yi tafiya?”
Murmushi Nuriya tayi tace, “baba duk da ba na gani amma ina iya ganin abinda ku masu idanuwa sam ba za ku taɓa gani ba, don ALLAH Baba karka tafi”.
Wani irin kuka Nuriya take wanda kallo ɗaya zaka mata ka fahimci daga zuciya kukan yake fita…..
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_
1️⃣6️⃣
*The best plan is the one who knows what’s ahead & what would happen. & there’s only one who knows the unseen. That’s Almighty. He’s the best of the planners. Trust him & his plans. You don’t know what’s coming but he does. Have patience & you’ll ace through all.*
______ Sosai jikin Alhaji Muhammad yayi sanyi, ganin abinda Nuriya take yasa shugabannin gurin suka ɗauke ta daga gaban shi, murmushi kawai yayi yace, “za mu tafi a yi mana aikin gafara.
Duk wanda ke cikin wannan gidan marayun jikinsa yayi sanyi ganin yanda har Alhaji Muhammad ya tafi Nuriya ba ta daina kuka da birgima ba, bayan kuma duk faɗin gidan Nuriya tana ɗaya daga cikin yaran da ake tunanin suna da matsalar rashin son magana, amma yau ga shi har tana wasu bayanan wanda kowa sai da yayi mamakin haka.
Cikin mota kuwa Alhaji Muhammad sai sharar ƙwalla yake, gabakiɗaya jikin sa yayi sanyi, kuma ko tambayarsa aka yi wallahi ba zai iya faɗar matsala ɗaya da yake ganin ita ce sanadiyyar sanya shi cikin wannan yanayi ba.
Ko da ya isa gida tuni Ni’ima ta gama harhaɗa duk abinda ta san za su buƙata, sosai wannan abu yayi matukar ba wa Alhaji Muhammad mamaki, amma saboda sanin hali irin na Ni’ima yasa yayi mata uzuri. Har ya fita daga gidan kuma sai ya dawo, ya yi hakan kusan sau uku a na ukun ne yayi kiran *MUSADDAM* yana cewa, “ya ka zo gurina sanyin idanuwa na,”.
Murmushi kawai *MUSADDAM* yayi yace, “Daddy na wallahi kayi kyau sosai kamar saurayi”
Kallon sa Daddy yayi yace, “me kake so na ba ka a matsayin tukuicin wannan yabon?”
Ɗaga kai sama *MUSADDAM* yayi alamar abinda zai faɗa yake tunawa, can kuma yace, “Daddy ka min nasiha kawai ya isa, domin Malamin mu yana cewa mafi girman kyautar da za ka yi wa bawa shi ne kayi masa nasiha”.
Shafa kan *MUSADDAM* yayi tare da bubbuga bayansa cike da jin dadi yace, “ina maka nasiha da ka ji tsoron ALLAH, sannan ka riƙe gaskiya da amana a cikin rayuwar ka, sam kar ka damu da munafiki kuma kai ma ma kada ka zama mai munafurci, sannan ka rike zumunci domin kuwa ALLAH da Manzon sa ne suka umarce mu da muyi ta, saboda haka ina mai neman da ka min alƙawarin cewa za ka yi riko da wadannan abubuwa”.
Murmushi *MUSADDAM* ya yi yace, “nayi maka alƙawarin hakan daddy na”.
Kallon sa Ni’ima ta yi tace, “Wai me ke faruwa ne duk na ganka wani iri?”
Murmushi kawai yayi mata yace, “babu komai me kike gani?”
“Na ga kana ta ba wa wannan ƙaramin yaro amana ne da sunan ya riƙe maka ne wanda nake ga kamar tayi masa nauyi a wannan shekarun nasa”.
Janyo hannunta yayi ya ɗaura na *MUSADDAM* akai yace,”Na ba ka har amanar kula min da Mummyn ka da kuma ƙanwarka Safnah ka ji ko”. Gyada kai kawai *MUSADDAM* yayi. Ita kuwa Mummy jikinta ne yayi sanyi kalau ta kasa sake cewa komai.
Har suka isa garin kallon mamaki take bin sa da shi don kuwa ta lura duk jikinsa a mace yake.
Da murna Inna Salma ta tare su tana musu barka da zuwa. Sai da aka gaggaisa sannan Inna Salma ta miƙe ta shiga ɗakin ta, cikin ƙanƙanin lokaci kuma ta fito hannun ta ɗauke da ƙwaryar nono tana cewa, “yauwa ɗana aikuwa kamar na san kana hanya na aika aka siyo min nono da fura, yanzu na gama damawa ma”. Miƙa masa tayi, shi kuwa ba tare da tunanin komai ba ya karba fuska a sake ya kurɓe nonon yana mai ƙara jaddada mata yadda ya ji daɗin shan nonon.
Inna Salma kuwa daga ganin ya sha nonon nan habawa, tuni farinciki ya gama mamaye mata jini da tsokar jiki.
Kallon ta Muhammad yayi yace, “Inna wannan farin cikin duk na mutuwar Muhammad ne?”
Saboda tsabar ruɗani sai da Inna Salma ta nemi faɗuwa tace, “ban….ban fa..ban fahimci abinda kake nufi ba ɗan nan…”
Murmushi kawai Muhammad yayi ya kalli Ni’ima yace, “don ALLAH kiyi min alƙawarin za ki ba wa ƴaƴana tarbiyya wacce zasu yi alfahari da ita ko da kuwa bayan ran mu ne, ki min alƙawarin kulawa da ƴaƴana, ki tabbatar sun yi karatu mai zurfi, kar ki bari *MUSADDAM* ya aure sangartacciyar mace, domin kuwa haka na iya jefa shi cikin mawuyacin hali. Ki tabbatar *MUSADDAM* ya auri yarinya ma’abociyar addini, saboda rashin samun haka yana iya jefa shi cikin halaka mafi girma, ki kuma kula min da ƴaƴana da dangina, har duniya ta naɗe ban yarda ki faɗawa kowa sanadiyyar mutuwa ta ba, don kuwa ita mutuwa rigar kowa ce, kallon Inna Salma yayi yace, “tabbas na san cewa kin saka guba cikin wannan furar saboda sam dandanon furar ya bambanta da yadda na saba ji amma haka na dage na shanye tas, saboda yau ita ce ranar da ALLAH yayi alƙawarin mayar da ni inda na fito”.
Kuka sosai mummy take kamar ranta zai fita, sake rike hannun ta yayi yace, “ki riƙe min alƙawarin za ki rufe wannan sirrin, kada ki faɗa wa kowa abinda ya faru, ko da na mutu yanzu ko anjima, Ni’ima ki min alƙawarin rike wannan sirrin, ba na fata a rinƙa kallon yara na ana cewa, ga yaran da Innar su tayi sanadiyar raba rai da gangar jikin mahaifin su”.
Miƙa mata hannu yayi idanuwansa sunyi ja sosai ga wani irin gumi dake feso masa ganin ba ta da niyyar miƙa masa hannun yasa yayi ƙarfin hali saka na shi cikin na ta kallon ta yayi yana murmushi yace, “shin a haka zamu rabu?”
Cike da jarumta, “Ni’ima tace, “na yi maka alkwari insha ALLAH babu wanda zai ji wannan kuma ai cuta ba mutuwa ba ce,kawai ka tashi mu tafi asibiti tun kafin wannan gubar ta yi maka illah sosai don ALLAH”.
Tashi mummy tayi ta fita neman wadanda zasu taimaka mata don su dauke shi su kai shi asibiti.
Inna Salma kuwa gabaki ɗaya ji tayi jikinta yayi sanyi, nadama take son yi sai dai kuma son duniya da abinda yake cikin ta tuni sun rufe mata ido.
Koda aka kai Alhaji Muhammad asibiti tuni rai yayi halinsa.
Sosai da yawa suka kaɗu da jin rasuwar wannan bawan ALLAH.
Can gidan Marayu kuwa sosai suka sake yarda da lamarin Ubangiji, kenan duk abinda Nuriya take faɗa wancan ranar gaskiya ne.
Tun daga wannan lokaci Ni’ima ta ɗora daga inda mijinta ya tsaya wajen ayyukan kyautatawa mutane duk inda danginta suka yi da ita akan tayi aure amma ina kullum zancenta ɗaya ne, “mijina guda ɗaya ne cikin duniyar nan kuma yanzu baya nan”.