HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Fitowarsa daga ɗaki yayi daidai da fitowar mummy daga sashenta za ta zo wajensa don kuwa bayan sun yi magana da shi ta mance faɗa masa tafiyar da za tayi gobe kuma tsaf ta san shi da wuri yake barin gida, hakan yasa ta yanke shawarar faɗa masa a cikin daren nan.

Kallo ɗaya ta yi masa gabakiɗaya ta nemi natsuwarta ta rasa. Shi kuwa izuwa lokacin tuni ya fara ganin dishi-dishi. Ganin zai faɗi ne yasa mummy taro shi cikin sauri haɗe da ƙwalla kiran sunan *SAFNAH*.  Jin kamar kiran ba na lafiya ba ne yasa ta ƙaraso gurin da gudu. Baki na rawa mummy tace, “kira min mai gadi da driver, *MUSADDAM* babu lafiya”.

Jin haka yasa ta fice daga falon tana mai ƙwalla kiran sunan mai gadi.
*
Cikin mintunan ƙalilan aka iso da shi asibitin. Wani tsaftataccen ɗaki aka kwantar da shi, yayin da likitoci suka fara ba shi taimakon gaggawa. Ba su dauki tsawon lokaci ba suka samu nasarar shawo kan al’amarin.

Da fitowar Dr waje sai ya yiwa mummy bayani kamar haka, “wato Hajiya ba wani abu ke damun sa ba face rashin hutu da kuma sa wa rai damuwa….bayan wannan ban ga wani ciwo tattare da shi ba.”

Godiya kawai mummy tayi masa sannan ta nufi ɗakin tana ƙwafa.

Shigarta yayi daidai da buɗe idanuwansa yana wani yamutsa fuska, kallonsa mummy tayi tace, “yanzu *MUSADDAM* so kake ka ga ka kashe ni sannan za ka huta ko?”

Jin wannan kalaman ya sa *MUSADDAM* ɗago fuskarsa cikin sauri yace, “mummy ki daina faɗar wadannan kalaman wallahi babu abinda nafi so a duniya bayan ALLAH da manzonsa sama da ke mummy na…”
“Mummy kar ki manta ke ce sanyin idaniyata, ta ya kike tunanin zan so a ce bakya raye cikin duniyar nan? In dai kuma zancen aure ne wallàhi zan yi kamar yadda nake faɗa miki kullum, insha ALLAH zan yi idan lokaci ya yi”

Sauke ajiyar zuciya mummy ta yi tace, “ga shi saboda damuwa har kana neman saka lafaiyarka cikin hatsari ai”.

“Ƙwantar da hankali ki mummy na babu abinda zai faru.

Yana cikin magana Dr ya shigo. Umartar su ya yi da su fita waje su bar shi ya huta. Sosai hakan yayi wa *MUSADDAM* daɗi dan kuwa a duniya idan akwai abinda ya fi tsana to fa ɓacin ran mummy ne .

Lumshe idanuwansa ya yi yana mai dafe ƙirjinsa, daga can cikin maƙoshi kuwa yana cewa, “kina ina ne? Shin a ina kika shiga kika ɓoye kan ki? Kin min alƙawarin za ki nuna min kanki nan ba da jimawa ba ga shi har yanzu na kasa sanya ki a idanuwana….”

“….ki taimaka ki bayyana a gare ni, kar ki damu da kamanninki da kike yawan cewa, idan na gan ki ba zan so ki ba. Wallàhi ko da ke gurguwa ce, ko kuma makauniya, ko da kin kasance kurma, ina mai tabbatar miki zan yi miki sahihiyar soyayya wacce babu algus a cikin ta….”

“….ki taimakawa rai da gangar jiki na yake ma’abociyar hikima tabbas kalaman ki su ne suka dulmiyar da ni zuwa ga kogin so da kaunarki…”

Haka dai *MUSADDAM* ya ci gaba da sambatu har bacci barawo ya yi awun gaba da shi ba tare da ya sani ba.

************

*UMMI* kuwa sosai take wa Umma magiya akan lallai sai fa an kai ta gurin *MUSADDAM*. Duk yadda Umma ta kai da dauriya amma saida ta zubda hawaye ganin yadda ƴar ta ƙwalli ɗaya ta bi ta fige saboda fama da so da ƙaunar mutumin da ko kallonsa ba ta taba yi ba. Inda uwar ramar da ta yi yasa ko mai aikin gidan su tafi ta dadin gani.
“Wannan wace irin jarabawa ce? ALLAH ka taimake mu ALLAH kai ne kawai ka san abinda ka ɓoye cikin wannan lamari ALLAH ina riƙon ka daka kawo mana mafita cikin gaggawa.

Ganin abin yaƙi ci yaƙi cinyewa yasa Abba kiran Dr akan ya cire mata ruwan dake jikinta zasu tafi gida su dawo”.

Sosai abin ya bawa Dr mamaki wanda ya kasance ɗan abokin Abban ne. Kallon Abba yayi yace,”Abba amma ina ga alkwai matsala barin *UMMI* ta tafi gida cikin wannan yanayin gaskiya, to wai mene ne za ta dauka a gidan idan ta tafi?”

Kallon *UMMI* ya yi yace,”ƙanwata me zaki ɗauka a gida ki faɗa min ni sai na tafi na ɗauko miki kin ji?”

Murmushi gefen baki *UMMI* tayi tace, “yayana wallàhi da kana da halin zuwa ka ɗauko min da na fi kowace mace murna da farin ciki a yau, sai dai kash wannan abin duk tsananin so da ƙaunar da nake masa ba ni da damar ɗauka sai dai hange daga nesa. Yaya ka ga kenan ba ni da damar aiken ka don ka dauko min”.

Buɗe baki ya yi da niyyar sake yin magana cikin sigar rarrashi sai tace, “yaya kar ka damu, kuma kar kace za ka hana ni don ba zan hanu ba kuma sam ba zan so ka damu ba, saboda duk cuta biyun ba su da magani. Yaya ina an kawo ni nan saboda ka sama min lafiya ne ko? “To fa ka sani Dr ɗina yana cikin unguwar mu, Dr ɗina yana nan kwance cikin wani gida wanda kallo ɗaya za ka masa ka fahimci * UMMI* ko ƙofar gidan bata isa takawa ba bare kuma samun gurbin so da ƙauna a zuciyar mafi soyuwa a cikin wannan gida, saboda haka zan tafi na gan shi ina da tabbacin idan na kai ga samun hakan zan samu sauƙi”.

Gabakiɗayansu idan ka ɗauke Umma wacce dama ta saba jin kalaman da suka fi wannan indai a bakin *UMMI* ne, Dr Nasir da Abba suman tsaye suka yi a wajen ganin yadda soyayya ta sauya *UMMI* daga mai tsananin kunya zuwa marar ita.

Hawayen da Umma take rikewa ne suka samu damar zubuwa daidai lokacin da Dr yake ƙoƙarin cirewa *UMMI* ruwan cikin sauri tasa bakin hijabinta ta goge.

A haka aka cire mata ruwa sannan aka saka mata hijabinta. Riƙe mata hannu umma tayi har suka isa ɓangaran da ake ajiye manyan mutane wato masu hannu da shuni VIP.

A daidai wata ƙofa wacce daga ita sai harabar asibitin, *UMMI* ta ji wani irin bugun zuciya wanda sai da ya sanyata dafe ƙirjinta da sauri saboda tsananin ta. Kallonta Umma ta yi tace,”lafiya kike kuwa *UMMI*? kallon Umma ta yi daidai lokacin da ta ji wani irin sanyi da nutsuwa ya dirar mata lokaci ɗaya, wannan bugun zuciyar kuwa na cigaba da tsananta sosai ta shiga ruɗani don kuwa gani ko kuma kasancewar *MUSADDAM* a guri shi ne kawai yake sa ta ji irin wannan yanayin “to ina yake MUSADDAM* ɗin”?

Kamar daga sama ta jiyo Umma ta jefo mata wannan tambayar, “wayyo kenan a fili na yi magana?”

Sake jefo mata tambayar Umma tayi a karo na biyu, kallon dakin *UMMI* tayi tace,”Umma ni ma ban sa ni ba, amma tabbas ina jin numfashinsa a kurkusa da ni Umma”
Daidai nan wata mata wadda da alama dai malamar asibitin ce ita ma da gudu ta fito daga ɗakin da *UMMI* take kallo tana kiran Dr! Dr! da alamar ruɗewa a tare da ita.

A hankali*UMMI* Take takawa zuwa ga wannan ƙofar da take gani kuma take ƙara tabbatar wa kanta cewar babu shakka *MUSADDAM* ɗin ta yana ciki.
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

 

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

_Jama’a ku shaida na sadaukarwa da wannan littafin ga*Musaddam Idiriss Musa*_

 

*Reviewed by: Musaddam Idriss Musa*

*Worry about your own sins, your shortcomings & transgressions. If you do that faithfully, you’ll have no time to worry about what others are up to. Remember, the Almighty is going to ask you about you! He won’t ask you about anyone else. Focus on self. Be the best version of you!????*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button