HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Da haka har kowa ya hakura, babu abinda lokaci ya bari kama daga rai da tsufa, haka shi ma mahaifin Ni’ima wacce yanzu suke kira da mummy  ya rasu.

Sosai mummy take tsaye kan duk wani al’amari wanda ya shafi dangin daddy, duk wani abinda ya taso takan yi ƙoƙarin ganin ta taimaka musu da shi, abu ɗaya ne kawai shi ne har rana mai kamar ta yau mummy ba ta sake taka kafarta zuwa  wannan garin ba, haka ma kuma ƴaƴan ta.

Don ko a lokacin da Suwaiba za tayi aure kuɗi kawai ta aika musu da shi sai kuma dangin Halima su ma kowane wata tana aika musu da kuɗi don biyan buƙatar yau da kullum.

Ko da *MUSADDAM* ya fara zuwa jami’a karatu, sosai mummy ta nuna masa tana da sha’awar yayi kasuwanci kamar yadda mahaifinsa yake da buri.

Babu musu kuwa *MUSADDAM* ya ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya. Inda bayan ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin Computer Science sai ya dora da yin digirinsa na biyu a fannin kimiyyar kasuwanci wato karatun MBA inda ya fito da sakamako mai kyau.
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_

1️⃣7️⃣

*A delay is not a denial, it is only a sign that you need to have peace, patience & trust that in perfect timing what you want will come to you. Sometimes you are delayed where you are because Allah knows there’s a storm where you’re headed. Be grateful. Trust Him.*

 

_______ *MUSADDAM* ya kasance mutum mai yawan son kyauta da kuma kyautatawa na ƙasa da shi, *MUSADDAM* mutum ne wanda kallo ɗaya ba ka isa ka fassara halayen sa ba, a murɗe yake gudanar da al’amuran sa, sam ba shi da son hayani, haka kuma ba ya son yawan surutai, sosai ƴan mata da samari suke son sa samari da yawa sun shi kawo kan su gare shi da zummar yin abota, murmushi kawai yake yace, “babu damuwa ai, rashin kulawa da kuma basarwa da suke fuskanta daga gare shi yasa duk suka janye.

*MUSADDAM* mutum me mai sauƙin kai ga duk wanda ya fahimce shi.

Hakan yasa sam ba shi da wadanda ya shaku da su sama da mutum biyu a rayuwar sa, na farko abokinsa Faruq, sai kuma wacce take kiran sa da Yaya wato Fairuza. Dukkansu a tare suka yi makaranta, kasancewar *MUSADDAM* yana da kaifin basira hakan yasa bayan an tashi daga lakca yake gabatar musu da darasi.

Sosai *MUSADDAM* da Fairuza suka shaƙu ta yadda duk inda ka ga *MUSADDAM* to fa za ka a wajen za ka ga Fairuza. Wannan dalili yasa da yawa suke musu kallon masoya, inda mata da yawa suka shiga hassada da ita, tun ba ta ɗauki abin komai ba har fa abin ya fara tasiri a zuciyar ta.

Shi kam *MUSADDAM* harkar gabansa kawai yake don kuwa ba shi da wani buri da ya wuci ganin ya faranta ran mahaifiyar sa ta hanyar fitowa da sakamako mai kyau.

Ko da Fairuza ta samu Faruq da wannan zancen babu ɓata lokaci yace, “kin ga Fairuza kame warki da kuma shiga ta kamala da kike yi ne yasa *MUSADDAM* ya yarda kika raɓe mu har muka saba da juna ki yarda da abinda zan faɗa miki wallàhi sam babu ɗigon sonki a zuciyar *MUSADDAM* kuma karki yarda ya ji kin furta wannan zancen idan kuma ba so kike abotar mu ta katse daga nan ba,”.

Girgiza kai Fairuza tayi tace, “sam ba na son yin nisa da *MUSADDAM* ko da kuwa na daƙiƙa ɗaya ne Faruq, wallàhi ni kaina ban san lokacin da na faɗa son sa ba, wallàhi Faruq ba zan taɓa iya cire *MUSADDAM* a raina ba, soyayyar sa tuni tayi zurfi a cikin zuciya ta, kullum da tunanin sa nake kwana ta yaya kake tunanin zan iya rayuwa babu *MUSADDAM* ?….”

” …Wallàhi ba zan iya ba”.

Kuka take sosai ta yafda har ba ta san lokacin da *MUSADDAM* ya iso gurin ba, gyaran murya yayi yace, “ya dai ƙanwata”.

A firgice ta juya tana share hawayen ta, murmushi yayi yace,”Ƴan shagwaɓan sun motsa ko?…” “…ko dai yau ma Faruq ne ya taɓa mana ke?”

Juyawa yayi yana duban abokin nasa, “Wallàhi Faruq ka kiyaye ni ka ji na faɗa maka…”
“…kar ki wani damu da shi kin ji zo mu tafi gida wallàhi a gajiye nake sosai da sosai”.

Da haka suka shige motar sa har suka isa ƙofar gidan su Fairuza babu wanda ya kuma cewa da wani uffan acikin su dama shi *MUSADDAM* ba ma’abocin surutai ba ne. Tana shiga ciki Faruq ya kalli *MUSADDAM* yana cewa, “Wai kana nufin kace min duk abinda take faɗa ba ka ji ba ne?”

A daƙile yace, “ban fahimci zancamen ba. Kana nufin saboda na ji tace tana sona shikenan sai na rufeta da duka ko me?”

Da mamaki Faruq yake kallon sa yace, “to ko dai kai ma kana sonta ne?”

Murmushi kawai *MUSADDAM* yayi yace, “Kwantar da hankalin ka Faruq nasan cewa kana son Fairuza tun ba yanzu ba, bayan sanin haka kuma sai ni na faɗa soyayya da ita? Ina sam dukda cewa kuwa ba ka faɗa min ba, amma alamomin hakan sun bayyana a tattare da kai kuma shin ina laifin wanda ya nuna yana ƙaunar ka, babu abinda yafi dacewa nayi mata illa in nuna ban ji komai ba, ko hakan zai sa kai ma ka samu shiga ta ɗan raɓa ka” ya karisa maganar cikin sigar zolaya.

Dukan wasa Faruq ya kai masa, *MUSADDAM* kuwa murmushi yayi yace, “wannan zuciyar taki ce ke kaɗai sanyi ln idaniyata, tun ban san waye ni ba na fara mafarki dake shin sai yaushe za ki iso gare ni ne?”

Dafa shi da Faruq yayi ne yasa ya dawo daga tunanin da yake yace, “Yallaɓai ya dai, ka fa wuce unguwar mu”.

Waskewa *MUSADDAM* yayi yace,”Malam na sani gida zamu tafi kullum sai Mummy ta tambaye ka”.

Da haka suka isa gida.

Abu kamar wasa soyayyar *MUSADDAM* ta samu guri ya zauna a zuciyar Fairuza, kullum da tunanin sa take kwanciya bacci kuma take tashi?

Ganin yadda kullum take ƙoƙarin shishshige masa yasa ya fara ja baya da ita ta hanyar ɗaure mata fuska, tsakanin shi da ita kawai sai dai zancen karatu. Suna gamawa kuma yake tafiya gida abin shi, Faruq kuwa tun yana danne wa har ya kai ga ya furta mata kalmar da ta daɗe a cikin ransa game da ita.

Rai a ɓace ta kalle shi tace, “shi *MUSADDAM* ne ya turo ka ka zo ka faɗa min haka ko kuma saƙonka ne?”

Da mamaki Faruq yake kallon ta dan kuwa yasan babu shakka yakai namijin da kowace mace za ta so, sai dai kawai da aka ce ra’ayi riga.

“Wannan saƙon daga zuciya ta ya fito kuma ina fatan za ki karɓe shi hannu bibbiyu”

Murmushin takaici Fairuza tayi tace, “wallàhi Faruq ko da kai ɗaya ne a cikin duniyar nan babu abinda zan yi da kai kalle ka fa babu wani tsari a tattare dakai na burge……”
Wani irin mari ta ji a ƙuncinta wanda yasa sai da ta daina ji na wucin gadi, ɗago kanta ta yi tana kallon sa, gabaki ɗaya kamannin sa sun sauya, banda hucin fusatar da yayi babu abinda yake, hannun sa kuwa rawa suke kamar an jona su da wayan lantarki, kallon Faruq yayi yace, “sshe kai sakarai ne? Mace za ka tsaya tana faɗan maka irin wadannan munanan kalaman kawai saboda ka furta mata kalmar so?”

“…Wallàhi ka ba ni kunya Faruq, ALLAH wadaran naka ya lalace”.

Kallon ta yayi a fusace yace, “kin ce Faruq ba kalanki ba ne ko? To ki sani haka nima ba kalanki ba ne ba, ko da kuwa matan duniya za su ƙare wallàhi ba zan taɓa sonki ba shashasha kawai mtssss”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button