HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Janye hannun Faruq yayi suka bar gurin, tsabar takaici har ya sauke Faruq ko kallon inda yake bai ba.

Fairuza kuwa sosai ta shiga damuwa ganin yadda gabaki ɗayan su suke gudanar da sha’anin rayuwar su ba tare da sun sake shiga sabgarta ba da haka har suka gama makaranta kowa ya kama gaban shi, lokaci zuwa lokaci Faruq da *MUSADDAM* suke haduwa don kuwa tuni har yayi auren shi ma *MUSADDAM* ya bari a baya.

A gurin Fairuza kuwa sam abin ba haka yake ba, don kuwa ta lashi takobin sai ta auri *MUSADDAM* ko a na ha maza ha mata.

Wannan shi ne taƙaitaccen labarin *MUSADDAM*
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_

1️⃣8️⃣

 

*Stop telling people more than they need to know. It only provides them with fodder for more gossip. Over sharing is not healthy. It can lead to unnecessary complications in life especially if you shared with the wrong people!*

_______ Ranar kuwa tsabar farin ciki Mummy kasa bacci tayi duk inda ta juya ganin *MUSADDAM* take a tare da *UMMI* murmushi tayi mai ƙaryatarwa tace “In sha ALLAH farincikin gidana zai dawo kamar yadda yake a baya”.

Miƙewa tayi ta ɗauro alwala, nafila ta shiga gabatarwa tana mai mikawa Ubangijin taliƙai zaɓi.

Cikin wannan daren kuwa rayuka uku ne basu rintsa ba, domin kuwa a ɓangaren *Ummi* ita ma kasa baccin ta yi ganin haka yasa ita ma tayi alwala ta fara gabatar da nafila. Shi kan sa *MUSADDAM* hakan ce ta kasance da shi cikin wannan dare mai tarin al’ajabi.

Sai da duk suka yi sallar Asuba sannan suka kwanta, sosai umma tayi mamakin rashin tashin *Ummi* da wuri kamar yadda ta saba da sallama umma ta shiga ɗakin ganin ta kwance saman sallaya yasa umma ta fahimci *UMMI* ba ta samu ta yi bacci cikin dare ba.

Gyara mata kwanciya kawai tayi ta fice daga ɗakin.

*UMMI* ba ta tashi farkawa ba sai kusan 11:00am.

Da gudu ta faɗa dakin umma tana cewa “Umma shi ne ba ki tayar da ni ba?”

Shafa gefan fuskantarta tayi tace “ai gani nayi kina bacci shi yasa”.

“Aiyya Umma wallàhi da kin tashe ai, ga shi kuma yanzu ya wuce “.

Haɗe fuska Umma tayi tace “au da ma zancen rashin ganin *MUSADDAM* kike?” na ɗauka magana kike akan ba ki tashi kin taya ni aiki ba”.

Tafukan hannun ta *Ummi* tasa ta rufe fuskarta da shi tana murmushi, kallon ta Umma tayi tana mai jin tsantsar ƙaunarta yana ratsa jini da jijiyar ta.

Tace, “wai ke rashin kunya ko?”

Juya bayanta tayi tace “a’a Umma wallàhi ba haka bane kiyi sorry kin ji Umma na?”

Maficin dake hannun ta umma ta daga za ta buga mata tana cewa “Gogonki ladidi ita ce kike cewa sorro ba ni ba”.

Da gudu *Ummi* ta fita daga ɗakin tana dariya har da riƙe ciki, sosai Umma take kallon ta ganin yadda ƴar ta ƙwalli ɗaya take cikin farin ciki wanda rabon da su ga irin hakan an dauki lokaci mai tsawo sosai.

Lura da yanayin kallon da Umma take mata yasa ta tsagaita da dariyar tace “Umma kawo omo nayi miki wanke-wanke “.

Miƙa mata Umma tayi tana mai jero mata addu’ar dauwama cikin farin ciki a rayuwar ta.

Wanke-wanke *Ummi* take tana rero karatun ta cikin muryarta mai daɗin sauraro. Faɗowa gidan Maimuna ta yi kamar an jeho ta. Jikin *Ummi* ta fada nauyinta ya rufu akanta ALLAH yasa akwai turmi kusa da ita wanda hakan yada tayi saurin dafawa tace “haba maimuna mene ne haka wai? Yanzu da na faɗi fa?”

Murguɗa baki Maimuna tayi tace “damuwata da ke kenan yasin, duk lokacin da mutum ya kawo miki labari mai daɗi sai kin nemi ɓata masa rai, shikenan ma na tafi abu na”.

Cikin sauri *Ummi* ta sha gaban ta tace “Ni ba haka nake nufi ba, amma dai kin san abinda kika yi ba ki kyauta ba dai ko?”

Rausayar da kai maimuna tayi tace “to shikenan ki yi haƙuri”

“Ke ma kiyi haƙuri, mene ne da ma kike son faɗa min?”

Faɗaɗa murmushin ta Maimuna tayi tace “Yanzu Asiya take faɗamin cewa, sakamakon jarrabawar mu ya fito”.

Tsalle *Ummi* tayi tace “Alhamdullah gobe sai mu je mu duba namu, shikenan   sai jami’a, wai wa ya ga *Ummi* a jami’a, tab za’a ga rigima, dukkan su dariya suke lokacin da suke gwada irin tafiyar da zasu rinƙa yi a jami’a.

**********
Ko da *MUSADDAM* ya farka sosai ya ji wani irin farin ciki yana shigar sa ta ko’ina, banda nishaɗi babu abinda yake ji, hamdala yayi dan kuwa yafi danganta samuwan wannan farin  ciki da sallolin da yayi jiya, tabbas babu abinda yafi sauƙin samar da farin ciki kamar ka kusanci mahalicci ka a lokacin da kake cikin wata damuwa.

Ji yayi yana da muradin fita shaƙatawa hakan ne yasa ya shiga wanka tare da sako kayansa masu matukar kyau da ɗaukar hankali. Kai tsaye zan iya kiran *MUSADDAM* da cewa yana daga cikin jerin mazaje masu cikar zati da haiba, don kuwa idan a tsaye yake ka dube shi, yana da tsawo sannan launin fatarsa baki ne sai dai ba irin baƙi wuluƙ ɗin nan ba, yana da wadatacciyar baƙar suma akai, haka yana da kwantaccen saje da kullum yake cikin shan gyara banda aikin fitar da wani irin ƙamshi da sheƙi ba abinda yake.

Yana da dara-daran idanuwa, hancinsa kuwa har baka, fuskarsa tana ɗauke da madaidaiciyar baki wanda kullum yake cikin kyalli kamar ana shafa masa mai.

*MUSADDAM* yana da faffaɗan ƙirji salon tafiyar sa na matukar burgewa da kuma ɗaukar hankalin ma’abocin kallonsa.

Saukowarsa ta yi daidai da fitowar Mummy daga sashinta, kallon sa take tana mai jin so da ƙaunar ɗanta yana  daɗa nunkuwa a ranta.

Har gabanta ya rusuna yace “Good morning Mummy na, abar alfahari na”.

Murmushi mai saukar da natsuwa tayi tace “Morning Son ya kake? Fatan ka tashi lafiya”.

“Lafiya ƙalau Mummy na, ina Lil Sis take ne?”

“Tana ciki”.

Suna cikin maganar sai ga Safnah ta fito tana cewa, “gaskiya an fara nuna wariyar launin jinsi a nan gidan”.

Dukkansu murmushi suka yi Mummy tace “wanda yasa kika makara dai shi ne ya nuna wariyar”

Cikin shagwaɓa tace “Yaya kana ji na da Mummy ko?”

Janyo hannun ta yayi yace “Ni dai ina matukar son ƙanwa ta”.

Tsalle tayi yace “Yawwa Mummy kin ji abinda Yaya *MUSADDAM* yace ko?”

Dariya *MUSADDAM* yayi yace “Kin ga rabu da mummy kawai bari ki ji wani abin mamaki”.

“Yawwa Yaya *MUSADDAM* ina jinka”.

“Shin kin san kuwa duk fadin duniyar nan babu wacce ta iya kiran suna na kamar ke?”

Ware idanuwa Safnah tayi tace “don ALLAH Yaya *MUSADDAM* da gaske kake?”

“Na taɓa miki karya ne kanwata?”

Tsalle Safnah tayi tace “Wowwwwww Nagode sosai “Yaya *MUSADDAM*.

Cike da ƙaunar juna suke cikin abinci har suka gama.

Tashi *MUSADDAM* yayi yace “Mummy bari na je na dawo”.

“Wai *MUSADDAM* ina kake zuwa ne kwanannan haka?”

Murmushi kawai yayi yace “Mummy ke ma kin san ɗanki ba ma’abocin yawon banza ba ne sai dai ya je wurare masu amfanarwa amma idan bakya so na fita sai na hakura na zauna”.

“To ai gani nayi yau Asabar ko?”

Dawowa *MUSADDAM* yayi ya zauna yana cewa “shikenan na ma fasa fita, Mummy ki ba ni labarin Daddy don ALLAH”.

Wata irin firgita Mummy tayi tace “Me kake faɗa haka ne wai, har sau nawa zan faɗa maka cewa rashin lafiya yayi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button