HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“Ƙwantar da hankali ki Mummy ni ba wai ban gamsu da bayanin ki ba ne, kawai dai akwai abinda nake tunawa ne game da wannan tafiyar tamu, Mummy. A lokacin Daddy lafiya kalau ya bar gidan nan”.

Daka masa tsawa mummy tayi tace “na yi maka karya kenan ko *MUSADDAM*?”

Sosai Safnah da *MUSADDAM* suka firgita da ganin yanayin Mummy daga sama suka ji wata murya tana cewa “ni ce kaɗai nake da wannan amsar da zan ba ka”.

Cike da firgici Mummy ta miƙe ganin …………….
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

1️⃣9️⃣

*_Dear Almighty. You have always been wonderful and merciful towards husband and I. Keep protecting my dear future husband and evil that men do which will surely leave after them. I believe in the oneness of the almighty and his judgement. You are the best of the judges . And let the enemies live long and see what the future holds for me._*

 

 

______________Suwaiba ce gabaki ɗaya tayi baƙi ta rame kamar wacce take ɗauke da cutar ƙanjamau, cike da mamaki Mummy take kallon ta tace, “meya kawo ki gida na?”

Murmushi Suwaiba tayi irin na tsofin riƙaƙƙun ‘yan bariki tace, “dama na san ba za ki taɓa farincikin zuwa na gidan ki ba Ni’ima, amma yau ALLAH cikin ikon sa ga shi na zo kuma ina mai tabbatar miki da cewa duk abinda kika shuka, to fa yau ne ranar da za ki girba. Yau ne ranar tonon asiri a gunki baƙar azzaluma kuma makira”.

Daka mata tsawa *MUSADDAM* yayi cikin wata irin fusatacciyar muryar da shi kan sa bai san yana da ita ba yace, “ke wace irin shashasha ce, kin shigo mana gida kina neman zagar mana uwa. Haka ake zuwa gidan mutane baƙuntar, shin wace ce ke ma tukunna da har za ki zo kina neman yi mana hauka”.

Dakatar da shi mummy ta yi tana cewa, “wannan ba maganar ka ba ce,ku shiga daga ciki ku bar ni da ita”

Dariya Suwaiba tayi tace,”dole kice su shiga ciki tunda kin san mugun abinda kika aikata ga mahaifin su”.

Gabaki ɗaya mamaki ne ya hana mummy furta ko da kalma guda bisa jin abinda Suwaiba take faɗa.

*MUSADDAM* kallon Mummy yayi tace, “Wai Mummy wace ce wannan don ALLAH, mahaukaciya ce ko me? Wai wa ma yace mai gadi ya bar mahaukata suna shigo mana gida…”

Haɗiye bakincikin da ya tokare mata wuya tayi tace, “yayar mahaifinka ce”.

A razane ya ɗago kai cike da mamaki yace, “Mummy…” cikin sauri Mummy tace,” *MUSADDAM* ba na son jin wata maganar daga bakin ka, kawai ja ƙanwar ka ku shige ciki zan yi muku bayanin komai zuwa dare”.

Har za su tafi suka tsinkayi muryar Suwaiba tana cewa, “ai dole kice musu haka, tunda kin kashe musu uba duk saboda son abin duniya, wallàhi Ni’ima kin ji kunya ta yadda sam ba na hango miki ƙarshe mai kyau…” Wata irin cakuma *MUSADDAM* yayi mata wanda sai da ta kusa faɗuwa ƙasa, gabaki ɗaya idanuwansa sun sauya kala saboda ɓacin rai. Ita kuwa Suwaiba numfashi ma neman gagararta shaƙa yake saboda tsabar matsar da ta sha, cikin sauri Mummy ta shiga tsakani ta hanyar janye shi gefe guda yana ta huci kamar fusataccen Zakara.

Sai da numfashin Suwaiba ya daidaita sannan tace, “dama na san ba za ka taɓa yarda da ni ba, amma ga wannan ka karanta, miƙa hannu Mummy tayi da zummar ta karɓi takardar amma cikin sauri Suwaiba ta miƙa takardar zuwa hannun *MUSADDAM*.

Buɗe takardar yayi zuciyar sa na wani irin bugu da karfin gaske, ganin rubutun kawai ya isa shaida maka cewa wannan daɗaɗɗen rubutu ne, a hankali *MUSADDAM* yake bin rubutun  takardar yana karantawa, wani irin gumi ne mai zafin gaske ke fita ta ko wacce ƙofa dake jikin *MUSADDAM* idanuwan sa kuwa kallo ɗaya zaka musu ka ji ba ka da marmarin sake kallon su saboda tsabar rinewan da suka yi, sun yi ja.

Mummy kuwa ganin halin da ya shiga yasa ta zo dabda shi da niyyar amsar takardar cikin sauri *MUSADDAM* yayi gutsu-gutsu da takardar ya yaga ta ya watsar a wajen. Wani irin ciwon kai ne mai tsanani yayi masa dirar miƙiya…ya na so ya furta ko da kalma ɗaya ce ko hakan zai sa ya samu sassauci daga abinda yake ji amma ina maimakon haka sai zubar hawayen masu zafin gaske. Janyo Safnah yayi jikinsa yana fitar da wani irin zazzafan hawaye. Tiririn zafin da ta ji irin mai yamutsa fatar mutum ɗin nan na fitowa daga jikin ɗan uwan nata ne yasa ta fahimci tashin hankalin da yake cikin ya kai ƙololuwa, cikin sauri ta janye jikinta tana cewa,”Mummy Yaya *MUSADDAM* ba shi da lafiya”.

Cikin sauri Mummy ta kai hannu jikinsa don tabbatar da abinda Safnah take faɗa,  cikin tsawa *MUSADDAM* ya dakatar da ita, tsawa irin wadda ke firgitar da hanjin ciki yace, “Har abada ba na ƙaunar hannunki ya sake taɓa jikina… kin cutar da mu, kin azabatar da mu, amma kar…..”

Jirin da ya ƙwashe shi ne ya hana shi ƙarasa zancen nasa da gudu Mummy ta rungume shi tana kiran sunan sa tare da girgiza shi take tana kuka mai tsuma zuciya. Kuka take wanda kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa kuka ne mai fitowa cike da zafi mai ƙona zuciya.

Cikin gaggawa aka nufi asibiti da shi, i zuwa lokacin kuwa Mummy har ta fita daga hayyacinta.

Suwaiba kuwa ganin cewa haƙonta ya cimma ruwa, ma’ana ta samu nasarar abinda ta zo ƙullawa, shewa ta saka tare da buga cinya a lokacin da ta ga maigadi na buɗe musu gate, “an gaisheka Boka Ɗan Kande, tabbas ban yi tafiyar banza ba har zuwa ƙasar da kake domin kuwa na samu biyan buƙata. Ƙaryar mutum ya ja da Suwaiba ya kwana lafiya wallahi ko da kuwa shi ne shaiɗan” sake bushewa da dariya tayi kamar wata tsohuwar mahakaukaciya.
“Yanzu saura aiki na gaba, farraƙu. Ke da ‘ya’yanki kam dai dai gani daga nesa Ni’ima. Uwar mu ta ga bayan mijinki ni kuma nace sai na ga bayanki da na ‘ya’yanki” da gama fadar haka sai ta kewaya zagayen bayan ginin gidan ta cikin haraba inda aka yi dashen wasu fulawoyi ta sinto baƙar layar da bokan ya ba ta ta toni ƙasar wajen ta binne tare da ɗauko wani guntun ragowar dutsen interlock ɗin da aka yi aikin gidan ta ɗora a saitin wajen don kar a gane tayi tono. Tana gama hakan tayi saurin ficewa daga gidan tana zazzare idanu a maigadin.

********

*UMMI* kuwa washe gari tunda sanyin safe suka nufi Cafe duba sakamakon jarabar su, ALLAH cikin ikon sa kuwa duk kansu sun fito da sakamako mai kyau.

Da murna suka nufi gida, ko da *UMMI* ta nunawa Umma sosai tayi farin cikin samuwar wannan nasarar da ta yi.

Daga nan *Ummi* ba ta tsaya bata lokaci ba ta sake yin wanka, feshe jikinta da turarurruka masu ƙamshi tayi, bayan ta gama saka wa jikinta wata koriyar atamfa wacce tayi ɗas a jikinta, janyo farar hijabinta tayi ta saka, wow sosai *Ummu* tayi kyau abin ta, tana fitowa Umma tace, “masha  Allah kin yi kyau abinki ƴar auta ta, buɗe baki *Ummi* za tayi maganar Maimuna ya dakatar da ita tana tace, “wallahi ni dai kin ga tafiya ta gida zan yi tunda sake tsayawa za ki yi”.

Kallonta *Ummi* tayi tace, “shin kin kuwa san ƙaɗaicin dake tattare da rashin ɗan uwa? To bara ki ji dalilin da yasa na daina zuwa gidan ku, na daina zuwa gidanku ne saboda yadda nake ganin kuna wasa da dariya a tare da ƙannen naki da yayyen naki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button