MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“Ina kallonku kuke yin komai a tare da ƴan uwan ki, ranar da bakin ki kika ce min akwai abinda ya faru ke da yayyen naki kawai kuka magance damuwar ba tare da sanin mahaifan ku ba, saboda haka ki sani nima ina so na ji irin wannan abinda duk masu ƙannai da kuma ƴan uwa suke ji”.
Tashi umma tayi ta share mata hawaye tana cewa, “Karki damu kin ji *Ummi* na? Da akwai abubuwa da dama wanda idan da ALLAH zai buɗe mana dalilin rashin samuwar su a gare mu, wallàhi da mun yiwa ALLAH godiya, ki sani sam ALLAH ba azzalumin bawansa ba ne, da yawa suna da ƴan uwa, amma kullum cikin tashin hankali iyayen su suke wasu kuwa ba su da yara da yawa amma kullum cikin farin ciki suke.
“Da yawan lokuta ALLAH yana hana mu wasu abubuwa ne saboda babu abinda zasu haifar mana sama da damuwa, nima kaina ban cire rai daga rahamar ALLAH buwayi gagara misali ba, don haka ki daina kuka kin ji *Ummi* na.
Share hawanyenta *Ummi* tayi tana cewa, “nagode wa ALLAH daya ba ni uwa kamar ki Umma na, insha ALLAH ba zan sake yin kuka saboda haka ba”.
“Yauwa yar albarka, to maza ku tafi kuma banda rawar kai, ki riƙe mutuncin ki a duk inda kike ina miki fatan alkairi kuma kice mata ina gaisuwa”.
“Za ta ji insha ALLAH Umma na.
Da haka suka fita daga gidan. *Ummi* kuwa tana fita daga gida ta ji duk wani farin ciki da zakwaɗin zuwa gidan su *MUSADDAM* ya ɓace mata ɓat, babu abinda take ji sai yadda kirjinta ke bugawa da sauri sauri, dafe gurin tayi tana karanto duk wani Addu’a da yazo bakinta a lokacin
Sosai Maimuna ta lura da sauyin yanayi daga *Ummi* kamar ta tambaye ta kuma amma tayi shiru.
Tunda suka fara tafiya babu wanda yace wa wani ƙala har suka isa kofar gidan, bugawa sukeyi bakin su ɗauke da sallama cikin sauri mai gadin gidan ya leƙo, bayan sun gaisa Maimuna take faɗa masa “gurin Mummy suka zo”.
Sauke ajiyar zuciya mai gadi yayi yace, “ALLAH sarki ai kuwa yanzu Hajiya ta fita sun kai *MUSADDAM* asibiti bashi da la…..
Wani irin zabura *Ummi* tayi baki na rawa tace,” Wani asibiti? “menene ya samu *MUSADDAM* ɗin? “Dan ALLAH*MUSADDAM* yana ina? “Ina *MUSADDAM* yake”.?
Duk lokaci ɗaya*Ummi* ta jero masa wannan tambayar tana mai zubda hawaye da mamaki mai gadi yake kallon ta dan kuwa irin kukan da kuma tashin hankalin da *Ummi* ta shiga tofa ko mummy ba ta shiga irin sa ba”………
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
*_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_*
_*You don’t have to discredit someone to feel good about yourself. Be the one who fixes something that’s not right in others without telling the whole world about it. Do things quietly away from the limelight. Let your heart smile at your deed! And the Almighty knows!*_
_______ Ko da mai gadi yayi musu kwatancan asibitin cikin sauri *UMMI* da Maimuna suka nufi can cike da zulumin abinda ya faru da shi *MUSADDAM* ɗin.
*******
Ko da Dr. Nasir ya fito kwantar wa Mummy da hankali yayi yace, “tabbas akwai babbar matsala sakamakon bugawa da zuciyar sa tayi lokaci ɗaya, da alama duk abinda ya sashi cikin wannan hali to fa abu ne wanda bai tsammaci zuwan sa ba, Alhamdullahi dai yanzu mun ɗan yi masa wasu dabaru wanda muke saka ran insha ALLAH nan da yamma zai farfaɗo”.
Kuka sosai Mummy take tana cewa, “yanzu kana nufin *MUSADDAM* ɗana ba ya cikin hayyacin sa? Innalillahi wa inna ilaihi raju’un…ALLAH ga baiwar ka nan wacce tayi imani da kai kuma ta miƙa dukkannin lamuran ta gare ka, ALLAH ka fi ni sanin daidai domin kuwa kai ne ka halicce mu bakiɗayan mu, tabbas na san ALLAH ba ya ɗorawa bawansa abinda ya fi karfin sa, na yi imanin cewa Allah ka san zan iya jurewa ne yasa ka jarrabe ni. ALLAH ga ɗana ALLAH ka kula min da shi”
Tasowa Safnah ta yi har zuwa inda Mummy take zaune tare da rike mata hannu tana cewa, “donn ALLAH Mummy ki yi min bayanin abinda yasa Yaya *MUSADDAM* cikin wannan halin idan kin sani”.
Share hawayen ta Mummy tayi tace, “ban sani ba, ban san abinda ta nuna masa ba, shin kunnuwan ki sun jiye miki abinda yayan ki yake furtawa a kaina kuwa?”
“Shin dama akwai shakku ko kuma rashin yarda a tsakani na da ku ban sani ba? Wallàhi duk abinda wannan matar ta nunawa *MUSADDAM* babu shakka sharri ne mafi girma, ALLAH ka dube ni duba irin wanda kake wa bayin ka salahai, ALLAH ka fitar da ni daga cikin wannan halin”.
Share mata hawaye Safnah tayi tace, “ki daina kuka Mummy wallàhi ko a jikina ban ji cewa abinda matar nan ta faɗa wa Yaya *MUSADDAM* gaskiya ba ne, kuma nayi miki alƙawarin ganin na shawo kansa idan har ya farka”.
Shafe mata kai Mummy tayi tace, “kar ki damu kuma ki daina kuka ka da kanki yayi miki ciwo”.
Daidai nan *Ummi* suka shigo asibitin da gudu *Ummi* ta faɗa jikin mummy tana kuka sosai Mummy tayi mamakin ganin ta cikin wannan yanayin ɗago kanta tayi tace,” *Ummi* na mene ne? “Me kika zo yi a nan waye ba shi da lafiya?”
Share hawaye *Ummi* tayi tace, “na tafi gida kamar yadda nayi miki alƙawarin zan zo, shi ne maigadi yake faɗa min cewa *MUSADDAM* ba shi da lafiya”.
Da mamaki Mummy take kallon ta ganin yadda take kuka da iya ƙarfin ta, idanuwanta har sun kumbura da alamu tayi kuka sosai, tace,” dama kin san *MUSADDAM* ne?”
Nan fa *Ummi* ta duburburce gabakiɗaya ta ma mance da mummy take magana, “a’a a’a…Mum…Mummy ban ..san shi ba, kawai dai maigadi ne ya faɗa mana sunan shi kuma yace mana ɗanki ne”.
Share mata hawaye Mummy tayi tace, “eh *MUSADDAM* ɗana ne, ayya…to…daina kuka kin ji ‘yata, ai jikin na shi da sauƙi, au shi ne kika yi ta kuka har haka? Ko dai dama *Ummin* Mummy ragguwa ce,”?
Su ne kanta *Ummi* tayi tace, “a’a Mummy na”.
“Yauwa to daina kuka kin ji?”
Sai a sannan *Ummi* da Maimuna suna samu damar gaishe da Mummy.
Cike da dakiya da kuma ɓoye damuwa ta amsa musu, sai dai da za’a buɗe zuciyar ta a lokacin tabbas za a same ta da sabon ciwo yana mai zubda jini.
Har kusan sallar la’asar Maimuna da *Ummi* suna cikin wannan asibitin, sosai Maimuna take son tafiya gida, *Ummi* kuwa gabakiɗaya ta ma mance da zancen zuwa wani gida lol????
Kallon su mummy tayi bayan sun idar da Sallah tace, ” *Ummi* ya kamata Ku tafi gida haka nan, tunda kin ce Umma ba ta san da zuwan ku asibiti ba, kin ji?”
Haɗa girar sama da ta ƙasa *Ummi* tayi tana shirin yin kuka, buɗe ba ki ta yi za tayi magana cikin sauri Maimuna ta murza mata hannu tana cewa, “shikenan Mummy za mu tafi insha Allahu gobe za mu dawo”.
Tsabar jin zafin mitstsinin da Maimuna tayi mata sai da tace,”auchhhh”.
Murmushi Mummy tayi tace, “yauwa ku gaishe min da Umman ku kin ji?”
“INSHA ALLAH” *UMMI* tace tana jin wasu hawaye suna neman gangaro mata.
Sosai rigimar *Ummi* yake burge Mummy don kuwa *Ummi* ba baya ba wajen rigima.
A hanya kuwa cinye Maimuna da masifa ne kawai *UMMI* ba tayi ba cewa take, “Gabakiɗaya na gama lura dake duk wani abinda kika lura yana bani farinciki ke kullum hassada kike nunawa, amma wallàhi ya kamata ki sani cewa,” *MUSADDAM* ya fi min gida da zan tafi yanzu, don kuwa ko da na tafi babu wani walwala ko kuma natsuwa da zan samu, kuma sanin kanki ne gani na cikin wannan halin, ta yarda hankalin Umma zai yi idan kuwa hakan ta kasance yasin ba zan taɓa yafe miki ba”.