MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Da mamaki Maimuna take kallon ta tace, ” Yanzu *Ummi* ni ce nake bakinciki dake? “Sam ban taɓa tunanin kallon da kike min ba kenan, amma don ALLAH kiyi hakuri nayi abinda nayi ne domin kare miki mutuncin ki, na farko Umma ba ta san abinda yake faruwa ba, idan baki mance ba cewa tayi ki riƙe mutuncin ki komai tsanani, karki mance kusan awannin mu huɗu a cikin wannan asibitin, shin kin yi tunanin Umma ko sau ɗaya?”
Kin yi tunanin cewa aƙalla akwai abinda za ta bukata kama daga ɗauko min, ajiye min? Haba mana *Ummi* ba fa cewa nayi karki dawo gobe ba? Zaman ki a gurin *MUSADDAM* ba yana nufin warke watsa ba ne ba *Ummi* kawai addu’a za ki masa”.
“Kuma don ALLAH ki yi hakuri idan akwai abinda nayi miki”.
Maimuna tana kai wa nan tayi tafiyar ta tana sharar hawaye. Sosai jikin *Ummi* yayi sanyi don kuwa ita kanta shaida ne kan irin son da Maimuna take mata.
Cikin sauri ta tari gabanta tana cewa,” Kiyi haƙuri don ALLAH wallàhi nima kaina ban san dalilin da yasa bana iya jure yin nisa da *MUSADDAM* ba”.
“ke kanki shaida ce kan tsananin son da nake yi wa *MUSADDAM* Maimuna don kuwa ina da tabbacin za ki iya ba wa wasu labari” soyayyar *MUSADDAM* ya zame min kamar numfashin da nake shaƙa, ke ma kuma kin san haka, don ALLAH ki min uzuri don ALLAH, wallàhi karki so ki ji yadda nake ji, ji nake kamar mutuwa zanyi idan har wani mummunar abu ya sami *MUSADDAM* wallàhi ina ji a jikina *MUSADDAM* yana cikin wani hali Maimuna, fashewa da kuka *Ummi* tayi dan kuwa sosai take cike da damuwar rashin lafiyar sa…….
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_
2️⃣1️⃣
*_If you have nothing good to say, remain silent. Each time you open your mouth to speak, you’re letting others know the state of your mind & what’s in your heart. If your heart is filled with bitterness, it will come out in your words. Be mindful of what’s going on inside you!_*
_______Kallon ta kawai Maimuna tayi tace, “ALLAH ya zaɓa mana abinda ya fi zama alheri”.
Jiki a sanyaye *Ummi* tace, “amin”.
Da haka suka rabu.
*Ummi* kuwa tana shiga gida ta faɗa wa Umma duk abinda ke faruwa, sosai Umma ta jajanta mata don kuwa ta san yau *UMMI* sai a hankali, aikuwa jiki a sanyaye ta ƙarasa wunin wannan ranar.
********
Can a asibiti kuwa *Ummi* suna tafiya Safnah ta matso kusa da Mummy tana cewa, “Mummy a ina kika samo waɗancan yaran?”.
Murmushi Mummy tayi tace, “yara fa naji kin ce, kin girme su ne?”
Girgiza kai Safnah tayi tace, “Don ALLAH Mummy a ina kika samo su”.
Kafin Mummy ta buɗe baki Dr ya karaso gurin yana cewa, “Hajiya bismilla ya farfaɗo”.
Jiki na rawa Mummy ta miƙe da sauri suka nufi ɗakin.
Ƙwance suka same shi idanuwan sa a lumshe sai dai ba bacci yake ba duba da yadda idanuwan sa suka ƙiftawa.
Matsowa kusa da shi Mummy tayi tana cewa, “Son…..” ɗaga mata hannun da yayi ne yasa tayi shiru zuciyar ta yana mata wani irin bugawa cike da fargaba, nan da nan kuma hawaye suka fara zuba daga idanuwanta.
Sake buɗe baki tayi tace, “Son akwai buƙatar muyi magana fa…”
Wata irin tsawar da ya daka mata sai da shi kansa Dr Nasir ɗin ya rikice da mamaki yake kallon sa don kuwa ya kasance family Dr ɗin su tsawan shekara da shekaru, inda a tsawon wannan shekarun kuwa babu abinda yake gani a tare da wannan ahali face so da kaunar juna, to yanzu kuma wannan sauyin daga ina?”
Matsowa kusa da *MUSADDAM* yayi yace, “kwantar da hankalin ka *MUSADDAM* Mummy ce take maka magana fa, ko dai akwai inda yake maka ciwo ne?”
Buɗe idanuwan sa *MUSADDAM* yayi wanda suka rikiɗa daga launin fari suka koma kalar ja.
Kallon sa kawai ya isa shaida maka cewa baya cikin hayyacin sa, sake lumshe idanuwan sa yayi.
Ganin haka yasa Dr juyawa gurin Mummy yace, “Hajiya fatan dai komai lafiya?”
Murmushi tayi mai ciwo tace “karka damu babu komai Dr. Nagode sosai da sosai ALLAH ya bar zumunci”.
“Amin, amma Hajiya idan babu damuwa zanso ki faɗa min abinda yake faruwa kila akwai wani taimako da zan iya miki….” Sam babu wanda ya lura da tashin *MUSADDAM* daga wannan katifar kawai sai jin hannun sa saman wuyar Dr suka yi, matse shi da bangon ɗakin yana wani irin huci, duk yadda Dr yayi don ganin ya cire hannun *MUSADDAM* daga wuyar sa, abin gagara ya yi.
Mummy kuwa sai kuka take tana rokon *MUSADDAM* da ya sake masa wuya, kallon sa *MUSADDAM* yayi yace, “mene ne alaƙar ka da family na? Shin kai Dr ne ko kuma ɗan jarida?”
Murya a daƙushe yace, “ka yi haƙuri wallahi kuskure ne ba zan sake ba Oga *MUSADDAM* amin aikin gafara don ALLAH”.
Wurgi da shi gefe *MUSADDAM* yayi sannan ya koma ya sanya takalman sa tare da ficewa daga asibitin yana sambatu.
Kallon Dr kawai Mummy tayi tace, “Kayi haƙuri Dr”.
Daga haka ba ta sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin.
Sauke ajiyar zuciya Dr yayi yace, “ALLAH ka fi ni sanin abinda ke faruwa cikin wannan ahalin, ALLAH ka yayyafa musu ruwan sanyi cikin dukkannin matsalar dake damun su”
***********
Suwaiba kuwa da farin ciki ta koma gida, nan ta samu Inna Salma zaune ta tsufa sosai don kuwa ko tashi ba ta iya wa, ganin Suwaiba yasa ta washe baki tana dariya.
Musayar murmushi Suwaiba ta mayar mata haɗe da samun guri ta zauna.
Inna Salma tace, “Fatan kin samu nasara wannan karon? Don kuwa ban shirya jin akasin haka daga gunki ba”.
Gyara zama Suwaiba tayi tace, “tabbas idan ban samu nasara ba to fa hakan yana nufin ba daga jini da jijiyar ki na fito ba, kamar yadda nayi alƙawari kuma tabbas babu shakka na cika burina. Na tarwatsa ahalin Muhammad ta yadda nan da ƙarni dubu ba zasu taɓa dawowa kan hanya ba, yau nayi abinda tun tasowata nake da buri Inna”.
Dariyar mugunta suka bushe da ita a lokaci guda, gyara zama Inna Salma tayi tace, “tabbas yau kin tabbatar min da cewa ke jini na ce kuma nayi alfahari da kasancewar ki ‘ya ta domin kuwa kin haifu”.
Kallo ɗaya zaka musu ka fahimci suna cike da tsantsar farin ciki, da haka Sale ya zo ya same su, ƙwashe duk abinda ya faru suka faɗa masa.
Da mamaki yake kallon Suwaiba yace, “wai dama har Ɗan Kande ya gama wannan aikin ne”.
“Sosai kuwa”
“Au shi ne kuma ba ki faɗa min ba?”
“Gani nayi kamar baka da niyyar cikawa inna burin ta ne ai”.
“Haka na faɗa miki”.
“to koma mene ne dai ai aikin gama ya gama ko yaya”.
“Eh haka ne amma wallàhi ban ji daɗi ba naso ace tare muka tafi”.
“Karka damu Yaya yanzu dai ahalin Muhammad tuni sun gama muddin suka taka wannan gidan”.
“Wai kina nufin harda na cikin gidan kin gama”.
“La Yaya kar dai kace duk labarin da nake ba ka hankalin ka baya guri na”.
“A’a kawai dai nayi mamaki ne”.
“Aikuwa babu wani abin mamaki anan tunda abinda muka daɗe muna buri ne”.
“Haka ne kam”.
Kallon su Inna Salma tayi tace, “tabbas kun cika min buri na kuma in Sha ALLAH duk abinda kuke buri zaku samu”.
(Allah ka tsare mu da aikin jahilci, amin)