MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

***********
Ko da *MUSADDAM* ya fita daga asibitin rasa inda ya nufa yayi don kuwa gabaki ɗaya ma ba ya tunanin komawa gida, ga wani irin tsanar Mummy da yake ji yana masa yawo cikin zuciyar sa, tunawa da Faruq abokinsa da yayi ne yasa ya juya kan motar ya nufi gidan sa.
Sai da ya kai kofar gidan sannan ya kira shi, ringing ɗaya kiran yayi Faruq ya ɗaga.
“Ka fito waje ina jiran ka”.
Yanayin muryar sa kawai ya isa shaida masa cewa babu lafiya.
Da sauri ya fita yana addu’ar ALLAH yasa dai lafiya.
A cikin motar sa ya same shi zaune ya kifa kan sa.
Buɗe motar yayi ya shiga, kusan mintina goma babu wanda yace da wani ƙala a cikin su.
Can Faruq yace, “inn muryar ka kawai ya isa shaida min cewa kana cikin matsala, sai dai ka sani ita dama rayuwa haka take babu yadda za a yi mu rayu ba tare da an jarabe mu ba, Karka manta da cewa ALLAH da kansa yana cewa, “shin za kuce kun yi imani ne ba tare da an jarabce ku ba?” Don haka koma mene ne matsalar ka *MUSADDAM* ka ɗauka yana daga cikin jarabawar da ALLAH yayi alƙawarin yiwa bayin sa masu biyayya a gare shi ne”.
Sauke ajiyar zuciya *MUSADDAM* yayi yace, “mu je ka kai ni gida”.
“Ok”.
Fitowa daga motar *MUSADDAM* yayi ya koma ɗayan ɓangaren.
*********
Mummy kuwa fitowa tayi daga ɗakin tana sharar hawaye, kallon ta Safnah tayi tace, “Mummy mene ne jikin Yaya *MUSADDAM* ɗin ne”?
Girgiza kai Mummy tayi tace, “Tashi mu tafi gida kawai”.
Da mamaki Safnah tace, “Mummy gida kuma wai mene ne yake faruwa?”
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_
2️⃣2️⃣
_*Sometimes the Almighty removes a particular person from your life because the relationship no longer serves any purpose. There’s no more positive growth. Learn to recognise it. Don’t run after that person who is not meant to be part of the next journey of your life. Move on!*_
__________Tashi Safnah ta yi suka bar asibitin.
Mummy kuwa banda tasbihi babu abinda take. Wani irin matsanancin ciwon kai take ji kamar kanta zai rabe gida biyu ya fita daga jikin wuyanta saboda tsabar raɗaɗin da take ji, rintse idanuwanta tayi tana furta,”Subhanallahi! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”.
Kallon ta Safnah tayi tace,” Mummy lafiya”.
“Kaina ke ciwo” ta ba ta amsa a gajarce, cikin kuma sauri. Don ko maganar idan ta so tayi ciwon ne ke daɗa ta’azzara.
” To mu tafi gida ki sha magani sai ki kwanta ki huta”.
“A’a, kawai mu tafi can gida”.
“Gidan Umma babba kike nufi wai?”.
Daƙyar mummy ta buɗe baki tace,”eh, can”
Da mamaki Safnah tace, “amma Mummy kin san ba ta son ganinki cikin damuwa ko, ganinki a haka sai ita ma hankalin ta ya tashi”.
Murmushin ƙarfin hali kawai Mummy tayi ta shiga mota tare da yi wa kanta masauki a kujerar baya ganin haka yasa ita ma Safnah ta tsuke bakinta ta shiga ta ɗaya kofar ta zauna a gefenta direba ya ja suka tafi.
**********
*MUSADDAM* kuwa tunda suka baro gidan Faruq babu wanda ya furta ko da kalma ɗaya a cikin su.
Ganin haka yasa Faruq yayi ta saƙe-saƙen abinda ya jefa *MUSADDAM* cikin wannan hali.
Ko da suka isa gidan har maigadi ya rugo a guje zai buɗe musu kofar get ɗin, cikin sauri kamar wanda aka tsikara da allura *MUSADDAM* yayi saurin dakatar da maigadin, da mamaki Faruq yake kallon sa yace,”Mene ne kuma abokina? Shin akwai abinda kake ɓoye min ne? Ni fa tunda na ganka cikin damuwa kuma har ka zo gida na wallàhi nasan akwai matsala don a iya sanina ba ya ga mahaifanka wallàhi zan iya yin rantsuwa babu wanda ya sanka kuma yasan halin ka kamar yadda na sani, karka manta fa kai kake faɗa mana cewa,” duk ranar da wata damuwa tasa ka kasa jurewa ko ka kasa faɗawa Mummy to fa gurin mu zaka zo…..”
“…..Ganin ka cikin wannan halin shiya tabbatar min cewa baka faɗawa Mummy abinda ke damun ka ba, nayi imani da tuni ta zama sillar gushewar damuwar ka *MUSADDAM* “.
Ɗago kansa *MUSADDAM* yayi wanda a yanzu yake jinsa kamar zai faɗo ƙasa yace,” Faruq ka shigar da ni gida don Allah”.
Yadda *MUSADDAM* yake magana kaɗai ya isa shaida maka irin jin jikin da yake.
Buɗe get mai gadin yayi suka shiga, samun guri Faruq yayi, yayi parking ɗin motar.
Fitowa *MUSADDAM* yayi yana dafe kansa saboda tsananin sara masa da yake.
Da haka suka nufi falon da zai sada shi da ɗakin sa, wani irin abu ne mai hasken gaske ya gifta a gabansa, buɗe baki yayi da niyyar yin addu’a amma ina ji yayi ko yatsun ƙafarsa ba zai iya motsawa ba sam. Taɓa shi da faruq yayi ne yasa ya ji kamar an kwance shi.
Da wani irin ɓacin rai yake kallon Faruq, can kuma yace, “ina wannan azzalumar matar? Wallàhi sai na kashe ta yau dole sai na kashe ta babu abinda zai sa na bar ta da ranta yau ɗin nan”.
Gabaki ɗaya mamaki da al’ajabi su ne suka yiwa hanjin Faruq dirar miƙiya tare da hana shi iya sarrafa gangar jikinsa don yayi motsi, ganin yadda *MUSADDAM* ya haura sashin Mummy da gudu yasa Faruq bin bayansa shi ma a guje yana kiran sunan sa.
Dukan ɗakin Mummy yayi da ƙafa yana faɗin, “sai na kashe ki yau”.
Nan da nan kofar ta buɗe, babu kowa a cikin ɗakin sai ƙarar AC dake tashi komai na ɗakin fari kal, babu abinda kake shaƙa sai ƙamshi mai saukar wa rai da ruhi salama.
Aikuwa ganin babu kowa yasa *MUSADDAM* fara yin fatali da komai na ɗakin, duk yadda Faruq yaso riƙe *MUSADDAM* abin ya ci tura, “wannan lamarin ba na wasa ba ne” abinda Faruq yake iya furtawa kawai kenan.
*MUSADDAM* bai saurara ba sai da yayi ɗaiɗai da kayan ɗakin, sannan ya fita yana jan wani irin mugun tsaki.
Bin ɗakin da kallo Faruq yayi yana tuna lokacin da suke makaranta, kullum a zaune saman sallaya suke iske Mummy da yadda *MUSADDAM* yake zuwa da gudu ya rungume ta fuskokinsu fal haske cike da fara’a. “To wai shin me ya shiga tsakaninsu?”
Haka kawai Faruq ya riski kansa da zubda hawaye, fita daga ɗakin yayi ya nufi ɗakin *MUSADDAM* abin mamaki sam ba shi a ɗakin.
Ƙarar fashewar abu yasa ya nufi inda ƙarar ke fitowa, abin mamaki gabaki ɗaya *MUSADDAM* ya Farfasa duk hotonan Mummy dake falon.
Janyo shi faruq yayi cike da hasala yace, “Wai kai wani irin sakarai ne? Mene ne ke faruwa da kai haka? Hotunan Mummy fa kake fasawa bayan kayi fatali da kayan ɗakin ta, wai ina Mummy take meke faruwa ne kamin bayani”.
Dafe kansa *MUSADDAM* yayi yana cewa, “Allah Faruq yau da hannun na zan kashe matar nan, idan ban kashe ta ba, ni mutuwa zan yi zan iya mutuwa wayyo kai na Faruq kaina zai fashe ka taimake ni”.
Gabaki ɗaya Faruq fita daga hayyacin sa yayi ganin yadda jikin *MUSADDAM* yake girgiza kamar mazari.
Kitchen ɗin gidan ya nufa ya ɗebo ruwa a karamar roba, yana zuwa da bismilla ya fara shafa masa a kai.
Wata irin ajiyar zuciya *MUSADDAM* yayi mai ƙarfin gaske, nan kuma jikinsa ya sake, taro shi Faruq yayi yana kiran suna sa” *MUSADDAM*, ganin numfashi sa yana sauka dakyau yasa ya shimfiɗar shi a gurin.
Fito da wayar sa yayi ya kira number Mummy, jiki na rawa ta miƙe duk da kuwa tsabar ciwon kai da faɗuwar gaban da take ji wanda ya kai ga sai da aka sa mata ruwa a gidan don tace babu asibtin da za ta tafi maganin ta shi ne yarda da ita kawai take so *MUSADDAM* yayi.