HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Ɗaga wayar tayi tace, “Assalamu alaikum, ɗana kana lafiya?”

Muryar Faruq har wani rawa yake don kuwa jin muryar Mummy kaɗai ya isa gane halin da take ciki yace, “Mummy nayi imani cewa ke uwa ce wacce ko wani ɗa zai yi burin samu a matsayin bango abin jingina, tabbas akwai abinda yake faruwa wanda sam ba ki ba zai iya furta su ba, Mummy kina ina ne yanzu haka?”

Cike da jarumta irin na uwa tace, “shin wani abu ya faru da sanyin idaniyata ne?”

Sauke ajiyar zuciya Faruq yayi ya zayyano mata duk abinda ke faruwa.

“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un!!!” kawai Mummy take iya furwa, godiya tayi wa Faruq sannan ta roƙe shi alfarmar tsayawa da *MUSADDAM* har zuwa wayewar gari.

Babu ko musu Faruq ya amince, domin kuwa ransa ne kawai ba zai iya bawa *MUSADDAM* ba don kuwa shi ɗin mutum ne mai tausayin na ƙasa da shi, kullum burin sa shi ne farantawa wanda suke tare,  rintse idanuwansa Faruq yayi yace,” kullum ina addu’ar Allah ya nuna min ranar da zan rama maka halacin da ka min *MUSADDAM* amma na rasa saboda babu abinda ba ka da shi, hakan yasa kullum nake ji a jikina cewar kana bina ba shi, alhamdullahi lokacin biyan ka yayi duk da kuwa da na san ba zan taɓa iya biyan ka ba abokina amma duk rintsi sai na yi ƙoƙarin gano ɓarakar dake tsakaninka da mahaifiyar ka sannan kuma sai na ga cewa na daidai ta ku”.
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

2️⃣3️⃣

 

 

*_When your turn finally comes, you’ll see why the delay was inevitable; why you had to wait. Remember, you can’t grow into a butterfly overnight, there is a process attached to it. Embrace every part of it because the process teaches us some valuable life lessons!_*

 

 

 

________Komawa cikin gidan yayi ya gyarawa *Musaddam* ƙwanciya haɗe da tofa masa addu’a.

Haurawa ɗakin sa yayi dake can saman beni ya ɗauko ɗaya daga jallabiyoyinsa ya saka, sam ba ya wani jin daɗin jikinsa, abubuwa ne cike a kansa wanda babu mai warware masa sai shi kansa *Musaddam* ɗin.

Bayan ya kira matar sa Sadiya ya shaida mata cewar ba zai samu dawowa gida ba saboda wani uzuri da ya riske shi, fatan alkairi kawai tayi masa tare da addu’a. Alwala yayi ya shiga gabatar da Sallah tare da miƙa ƙoƙon baran sa ga Allah madaukakin sarki.

Faruq ba shi ya tashi daga kan sallayar nan ba sai da aka idar da sallar Asuba. Duk da yawan baccin dake idanuwan sa, amma haka yayi ƙarfin halin tayar da *Musaddam* don yayi Sallah.

Allah cikin ikon sa kuwa ya miƙe saidai sam baya wani jin ƙwarin jikinsa, saida ya ɗauro alwala sannan ya nufi sashin sa yana mai jiro istigifari ganin makarar da yayi.

Saida ya idar sannan ya tuna da cewar Faruq ya gani acikin gidan, “To yaushe kuma Faruq ya shigo cikin gidan bansani”?

Saukowa falo yayi yana bin Faruq da kallon mamaki yace,”Aboki nayi mamakin ganin ka da asuba haka”.

Da mamaki faruq yake kallon sa yace,”Anan na ƙwana ai”.
Dafe kansa yayi yace,”Amma baka kyauta ba aida ka tafi gida yanzu haka ka bar min ƙanwa na ita kaɗai a gida”.

“A a ina ka mance akwai karamin*musaddam* a cikin ta”.?

pillow dake kusa dashi ya ɗauka ya jefawa Faruq yana cewa,”Ai har ma kasan wani iri zata haifa kenan”.?

Murmushi Faruq yayi yana cewa,”Au ajiya tace ai dole na sani”.

Shiru *Musaddam* yayi yana kallon hotonan Mummy dake yashe a ƙasa duk sun farfarshe cikin sauri ya isa gurin hoton yana kallon su da mamaki yace,”Faruq wanene ya fasa min hoton m….. Wani irin haske ne ya girta idanuwan sa,gabaki ɗaya *Musaddam* ji yayi ya kasa furta koda um ne, addu’a yake son yi amma ina.

Faruq da idanuwan sa yake kansa tunda yaji yana tambayar yanda akayi hotunan mummy suka fashe, ganin yayi shiru yasa ya nufi gurin shi cikin saurin yana tambayar sa,” Abokina yaya dai”.? Cikin sauri ya janye hannun sa daka jikin *musaddam* saboda wani irin raɗaɗin zafi daya ratsa jikinsa, da mamaki yake kiran sunan sa amma ina ko ƙirfa idanuwan sa *musaddam* bayayi.

Tashi Faruq yayi da niyyar ɗebo ruwa ya shafa masa Kamar yanda yayi masa jiya, saidai kash tun kafin faruq yayi nisa ya fara jin kururuwar sa yana kiran “Wallàhi sai na kashe ki yau azzalumar mata”.

Duk yanda Faruq yaso rike shi ina abu yaci tura, gabaki ɗaya saida sukayi ɗaiɗai da kayan falon komai a fashe yake dan kuwa kasa riƙe shi Faruq yayi, gabaki ɗaya ya gama jiwa kansa ciwo.

Cikin ikon Allah dabara ya faɗuwa Faruq kallon *Musaddam* yayi yace kana son ganin mummy ko”.?

Jiki na rawa musaddam ya ƙara so gurin Faruq shake masa wuya yayi yace” Tana ina ka faɗa min ko kuma kai na kashe ka”?.

Sosai lamarin ya kuma bawa faruq tsoro da tausayi gabaki ɗaya jikin *musaddam* yayi zafi kamar garwashin wuta, idanuwan sa sunyi ja. Wasu irin jijiyoyi masu kauri ne sukayi wa fuskarsa ado.

Baki na rawa yace,”Tana wancan ɗakin, Mummy tana wancan ɗakin’.

Jifa da faruq yayi da gudu ya haura ɗakin sa dan nanne Faruq ya nuna masa,ganin haka yasa Faruq ya miƙe cikin sauri duk da kuwa yana mattukar jin zafi a jikinsa saboda jifa dashi da *musaddam* yayi, cikin sauri ya nufi ƙofar ɗakin, ganin musaddam yayi sai dube dube yake yana kiran “ina kika shiga kika ɓoye kan ki”.?

Ganin haka yasa Faruq saurin janyo ƙofar ya garƙame da key, sosai yake jin yanda *musaddam* yake buga kofar yana kiran yau zaki mutu yau sai na kashe ki. Fashewa da kuka yayi yana mai jin ciwo da tsana mafi muni ga duk wanda ya aikata haka akan wannan bawan Allah mai ciki da tausayi da jin ƙan na ƙasa dashi.

 

Ganin haka ba mafita bane yasa faruq miƙewa cikin sauri ya fita daga gidan , bai tsaya ko ina ba sai family House ɗin su mummy,kallon ɗaya yayi mata yaji wasu zazafan hawaye suna zarya a kuncin sa, gani haka yasa itama ta fara kuka, ƙwantar mata da hankali yayi yace,”tabbas wannan sharrin aljannai ne Mummy amma nayi miki alƙawarin zamu shawo kan matsalar da yardar Allah”.

Fatan nasara Mummy tayi masa sannan ta bashi number wani malami wanda ya ƙware sosai wajen magance matsala irin ta mutanan ɓoye.

Sallama yayi mata ya shaga motar sa, saida ya shiga gida yayi wa Sadiya bayani sannan ya nufi gun wannan malamin. Allah cikin ikon sa kuwa malamin ya yarda zasu tafi gidan a tare yanzu, dan kuwa ahali irin na su *musaddam* babu wanda zasu ni mi taimako ayi jayya dan kuwa suma kullum jira suke suga mai niman taimako dan su taimaka masa.

Koda suka tafi har yanzu *musaddam* yana cikin wannan yanayi saidai zuwa yanzu har muryar sa ta dashe ba’ajin ihun nasa sosai.

Buɗe kofar faruq yayi malamin ya shiga, kallon ɗaya yayi masa yasan tabbas akwai matsala mai girman gaske a tattare dashi.

Fitowa yayi yana jinjina al’marin bayan yayi wa *musaddam* ɗin addu’a harya samu yayi barci.

“A gaskiya matsalar wannan yaro babban matsala ce wacce dole tana mattuƙar so a magance ta ciki sauri gudun kar abin yafi haka, idan muka yi la’akari da cewar kace wanda yayi jiya bai kai wannan ba ko”.?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button