MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“Eh Allah gafarta Malam”.
“Yawwa to yanzu zan tafi gida na dawo in sha Allah zanje na ɗauko masa wani magani wanda wanka kawai zaiyi dashi in sha Allah wannan magani duk inda ake amfani dashi tofa aljanna basu zuwa gurin da izinin Allah”.
Godiya sosai Faruq yayi masa, saida Faruq ya tare masa adaidaita sannan ya koma cikin gidan.
Abin mamaki har kusan yamma babu Malam babu labarin sa, da mamaki faruq yake kiran number sa amma shiru ba’a ɗauka ba, gashi.
*musaddam* shiru bai farka ba har yanzu, babu abinda yafi ɗagawa
Faruq hankali sai rashin cin abinci da *Musaddam* baiba.
Tashi yayi dan zuwa duba malamin, tun daga farko layin Faruq ya fara cin karo da jama’a, wanda kallo ɗaya zaka musu ka fahimci suna cike da alhini, ganin Kofar gidan malamin nan a ciki yasa yaji gabansa ya tsananta faɗuwa.
Cikin sauri ya ƙarasa ganin jama’ar gurin suna alwala, abin mamaki malam ne kwance cikin makara za’ayi masa sallah, tsabar ruɗewa saida Faruq ya zauna, gabaki ɗaya likafanin malam a jiƙi yake da jini, alamu sun nuna hatsari yayi.
Kuka sosai Faruq yake kaman ƙaramin yaro. Tsayawa yayi akayi wa malam Sallah aka sadashi da gidan shi na gaskiya sannan Faruq ya shiga motar sa bakin sa ɗauke da addu’a dan kuwa jin lamarin yanda malam ya rasa ransa kawai ya isa shaida maka mutuwar sa tana da nasaba da rashin lafiyar *musaddam*
Tafiya Faruq yake a hankali dan kuwa yanzu gabaki ɗaya lamarin ya fara ba shi tsoro…….
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_
*It might not be obvious to you now, but greater things are being planned for you. You’re always given the test before the reward. You’re always given the struggle before the strength. Hardships always come before the ease. Keep trusting the Almighty. The blessings will follow.*
________ A hankali kuma cikin nutsuwa Faruq yake tuƙin nasa, yayin da a can zuciyarsa kuwa banda addu’a babu abinda yake, Allah cikin ikon sa har ya isa gida babu abinda ya same shi. Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya samu guri yayi parking ɗin motar ta sa a gurbin da ya saba ajiyeta.
Zaune ya iske Sadiya ta yi jugum da ita. Ko da ta gan shi da gudu ta faɗa jikinsa tana kuka, rungume ta yayi yana cewa, “duk kewar ce haka?”
Girgiza masa kai tayi tana cewa, “tun da ka fita ɗazu na fara jin sabon yanayi a cikin gidan nan, gabaki ɗaya tsorata ni ake, tun ina jin motsi har na fara ganin giftawar abu, gaskiya ni dai ba zan kwana cikin gidan nan ba”
Kwantar mata da hankali Faruq yayi yace,”ki yi haƙuri lokuta da dama gudun matsala ya kan sa tayi ta bibiyar rayuwar mu, amma idan muka tsaya muka fuskance ta to fa a hankali komai zai daidaita, ki tuna babu abinda ya fi karfin addu’a kin ji tawan?”
Share hawayen ta tayi tana cewa,”shikenan ai tunda kana nan babu tare da ni ba wata matsala yanzu ba na jin tsoro tunda ga sadaukina a kusa da ni”.
Murmushi kawai yayi yace, “Yanzu dai muje ki ba ni abinci na ci kuma ki zubawa *Musaddam* na kai masa”.
Buɗe baki tayi da niyyar yin magana, shi kuwa cikin sauri ya haɗe bakin su guri ɗaya don sam ba ya so yayi mata ƙarya kuma ba zai taɓa faɗawa wani halin da *Musaddam* yake ciki ba.
Da wannan salon nasa ya mantar da ita ma abinda ta so faɗan, sai kawai ta biye masa inda a ƙarshe ita ma ta basar da zancen.
Sai da yayi wanka ya shirya sannan yaci abinci, kallon ta yayi yace, “ki kwantar da hankali ki kin ji tawan idan da halin za ki ga na dawo idan kuma babu zan kira miki shalele ta zo kin ga sai ku ƙwana tare ko?”
Tsalle Sadiya tayi tana cewa,”don Allah kawai ka yi zaman ka a can ka kira min shalele ta zo”.
Da mamaki yake kallon ta yace, “wai kina nufin kin fi son shalele a kaina?”
Rufe fuskarta tayi tace,”a’a ni dai ban ce ba kawai gani nayi kamar da gaske ba dawowa za kayi ba”.
“Shikenan duk yadda ake ciki zan kira ki”.
Da haka suka rabu.
Yana shiga cikin motar sa kuwa ya ɗaga wayar sa, ringing ɗaya kiran yayi aka ɗauka, ganin yadda yake magani cikin ladabi ya isa nuna maka cewar koma da wa yake waya to fa yana da matsayi a gurinsa.
Sallama yayi masa yana kara jaddada godiyar sa a gare shi.
Koda Faruq ya dawo abin mamaki samun *Musaddam* yayi zaune a kujera yana cin abinci.
Kallon juna sukayi na ‘yan wasu mintuna sannan yace, “ka wani tsaya min a kai, samu guri ka zauna mana malam”.
Zama yayi yana kallon yadda yake tsakurar abincin, sosai ya rame idanuwansa sun shige ciki, ganin yadda Faruq yake kallon sa yasa ya yace, “Wai abokina lafiya kuwa?”
“Me ka gani?”
Murmushi *Musaddam* yayi yace, “damuwar ɗan Nigeria kenan tambaya akan tambaya”.
Alhamdullahi kawai Faruq yake nanata wa, “wa ya kawo maka abinci?”
“Dafawa nayi sanin kanka ne ba na sayen abinci komai daɗinsa tunda ga m….
Wani irin ƙarar buguwa Faruq ya ji wanda sam ba zai ce wannan buguwar na mene ne ba, shi kansa idanuwan sa sun rufe a hankali yake buɗe idanuwansa, ganin babu *Musaddam* a inda yake zaune yasa yayi saurin miƙewa yana dube-dube, can hanyar kofar falo Faruq ya hango shi a yashe, jini na fita ta hanci da bakin sa, jini ne sosai ga goshin sa harya tashi, saboda buguwa da yayi.
Da gudu Faruq ya isa gunsa dan kawo masa ɗauki, cikin wani murya mai mattukar razanarwa *Musaddam* yace,” tabbas idan ka ƙaraso guna zan kashe ka wannan babu makawa, dan kuwa hannun ka yana azabatar dani a duk lokacin daka taɓi jikina”.
” Wannan faɗan ba naka bane ba, ka ni sance kanka da wannan lamarin, kayi gudu iya ƙarfin ka gudun ceton rain ka, babu wanda zan raga wa muddun aka nimi shiga gona ta
Gabaki ɗaya banda rawa babu abinda jikin Faruq yake yi, gabaki ɗaya tausayin *Musaddam* ya gama mamaye masa zuciya.
Komawa da baya Faruq yayi ganin yadda *Musaddam* ya nufo kansa gadan gadan, kursiyu ya fara karantowa yana hura masa, duk da jijjiga da ɗakin yake sannan
ga jinin dake fita hanci da bakin sa sai yawa yake ƙarayi, ganin haka yasa Faruq kara sautin karatun sa, nanfa *Musaddam* ya yanke jiki ya faɗi.
Da gudu Faruq ya ƙaraso gurin sa yana kiran sunan sa ganin jinin dake fita hanci da bakin sa sun dauke kamar babu wani abinda ya zuba daga cikin sa.
*********
*Ummi* kuwa washa gari tunda sanyi safe ta tashi ta fara soya waina bayan tayi miyar ta mai rai da lafiya, soya wainar take da kula gudun karya ƙo ne, duk abinda *Ummi* take Umma tana kallon ta, samuwar farin cikin *Ummi* shine samuwar farin ciki kuma da natsuwar su..
Kallon ta tayi tace,” Umma na fatan kin tashi lafiya?”
“Lafiya kalau wannan sammako haka duk na zuwa asibitin ne,”?
Sunkuyar da kanta *Ummi* tayi tana mai jin kunyar mahaifiyar ta.
Ganin haka yasa ta shiga ɗakin dan bata damar cigaba da abinda take, sosai kuwa taji daɗin haka ko babu komai akwai kunya tsakanin ƴa da uwa….
Saida *Ummi* ta gama suyan wannan wainar sannan ta sakawa Abba nashi, tabarma ta ɗauko ta shimfiɗa masa,haɗe da ɗibo masa ruwan wanke hannu, farin ciki ne mara misaltuwa ya cika zuciyar Abba dan kuwa *Ummi* ita ɗaya ta maye masa gurbin rai goma koma fiye da haka.