MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Zubawa Umma tayi sannan ta nufi toilet tayi wanka, tana fitowa ta iske Maimuna zaune tana jiran ta, murmushi tayi tace,”na ɗauka ba zaki samu zuwa ba ai”.
” Waina na zo ci ba zuwa asibiti ba”.
Ruwan dake cikin bikitin ta ɗiba zata watsa mata tana cewa,”Dama naji a jikina kwaɗanyi ne ya kawo ki”.
Duk kansu dariya sukayi sannan suka shige ciki nuna mata kula *Ummi* tayi tace,” Maƙwaɗaiciya dama ga naki can zan biya ta gidan ku na baki”
Da mamaki Maimuna tace,”Bayan fushi kike dani shine zaki wani wayance min”?
Matsowa kusa da ita *Ummi* tayi tana cewa,”Wallàhi sam bazantaɓa yin fushi dake ba Maimuna koda kuwa laifi kika min balle kuma duk abinda kika yi kinyi ne dan kare min mutunci na da martaba ta, Saboda haka babu abinda zance sai godiya”
Murmushi kawai Maimuna tayi bata sake furta komai ba har suka gama cin abinci, sallama sukayi wa Umma suka kama hanya, sosai take cike da jin daɗin ganin *Musaddam* da zatayi ƙila ma ya tashi a bacci yanzu haka dai ta yi ta saƙe sake a ranta har suka isa asibitin.
Ganin babu kowa a waje yasa suka nufin ɗakin bakin su ɗauke da sallama, saidai me babu kowa a dakin alamar dai an sallame su ko kuma sun canza ɗaki. , Suna tsaye ɗaya daga cikin malaman asibiti ta zo take faɗa musu an sallami *Musaddam* nanfa farin cikin *Ummi* ya sake nin kuwa.
Jiki na rawa suka nufi gidan Abin mamaki duk rokon da sukayi wa mai gadin gidan dan su shiga fir yaƙi, sosai rai *Ummi* ya ɓaci kallon mai gadin tayi tana cewa,”Malam idan ba zaka bari mu shiga ba babu damuwa amma dan Allah kaje ka faɗawa mummy cewa wata tana sallama da ita”.
Ko kallon inda su *Ummi* suke bayi ba ya shige cikin ɗakin sa.
Kusan awa biyu *Ummi* da Maimuna suka kwashe a wannan guri suna roƙon mai gadi daya bari su shiga su gaishe da *Musaddam* ganin suna damun sa yasa ya kore su daga Kofar gidan ma gabaki ɗaya.
Wani irin ɓacin rai ne wanda *Ummi* bata taɓa jiba tsayin rayuwar ta yayi mata dirar miƙiya, har suka isa gida babu wanda ya yayi Magana da ɗan uwan sa.
Suna shiga gida *Ummi* ta shige ɗakin ta hade da garƙame wa da sakata.
Bayani Maimuna tayi wa Umma sannan ta tafi gida zuciyar ta cike da alhinin halin da take ciki.
Sallah ne kawai yake fitar da *Ummi* daga ɗauki, share ta Umma tayi dan kuwa tana so ta koyi juriya da kuma ɓoye damuwa.
Magrib nayi Abba ya shigo gida yake shaidawa Umma cewa,” Yawwa kuwa na mance ban faɗa miki ba, wannan yaron Faruq ya kira ni ɗazu yake shaida min cewa a tura *Ummi* na zuwa gidan sa ta taya Halima ƙwana”.
Sosai Umma ta ji daɗin wannan bato dan ko babu komai damuwar *Ummi* zata ragu…….
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_
2️⃣5️⃣
_*No matter how much broken your heart is, try to fill it with positivity and believe that Allah is always with you. Sometimes in your lowest moments when you feel most helpless, Allah reveals a treasure to you when you least expect it! Be patient and Trust him.*_
_________ Tashi Umma tayi ta kira *Ummi* dan ta sanar da ita zuwan ta gidan su Faruq.
Sosai itama tayi murna duk da kuwa sosai hankalin ta yake a tashi rashin ganin *Musaddam* a yau cikin abinda baifi mintina ba ta gama shirin ta tsaf cikin riga da sikit kalan baƙi da fari.
Sallamar su Umma tayi Abba da kansa ya daura ta a adaidaita sahu ta nufi gidan su Faruq.
Koda ta isa samun Aunty Sadiya tayi a bakin get ɗin gidan duk jikinta dai rawa yake,tura get ɗin da *Ummi* tayi yasa ta zabura tana kiran”innalillahi wa inna ilaihi raju’un”.
Da mamaki *Ummi* take kallon ta tace,”Aunty menene”?
Sauke ajiyar zuciya Sadiya tayi ganin *Ummi* tace”Alhamdullah sai yanzu”.?
Har yanzu da mamaki take kallon ta tace,”Aunty menene yake faruwa na ganki a firgice kalli kafarki babu ko takalmi fa wai lafiya kuwa,”?
“Hmmm kedai bari wasu abubuwa ne suke tsora ta ni a cikin gidan nan wallàhi”.
Duk yanda *Ummi* taso riƙe dariyar ta abu ya gagara fashewa da dariya tayi tace,”Yau da kanki kike furta kalmar tsoro ba kince babu abinda ke baki tsoro a rayuwar nan ba”.?
Dungurin ta Sadiya tayi tana cewa,”Ke Kinga ni babu ruwa na da Wannan shirmen nan na ku ke da Yaƴan ki”.
Itama dariya tayi tace”To ai abokin wasa nane Kinga dole muyi wasa,karki manta da Abba na da hajiya uwa ɗaya uba ɗaya suke Kinga kuwa wasa ya wajabta a tsakani na dashi”.
“Wai sake faɗa min kike bayan kuma na sani”?
“Eh mana gara na jaddada miki ai”.
Wannan dalilin yana ɗaya daga cikin abinda yasa Aunty Sadiya da Ummi suka shaƙu sosai da sosai, kasancewar *Ummi* akwai barkwanci ita kuma Aunty Sadiya akwai sauƙin kai.
Ciki suka shiga *Ummi* bakin ta ɗauke da addu’a dan kuwa tabbas ta fahimci akwai matsala a cikin gidan.
Koda ta shiga cikin bata daina Addu’a ba duk da kuwa bata so Aunty Sadiya ta fahimci akwai matsalar.
Saida sukayi sallah sannan suka ci abinci har ila yau dai zuciyar ta ɗauke da tunanin sahibin ran ta.
A hankali barci ya fara fisgar su, tashi*Ummi* tayi ta tayar da Aunty Sadiya dan su shiga cikin ɗaki su kwanta, wani abin mamaki gabaki ɗaya idanuwan idanuwan Aunty Sadiya abuɗe suke saidai babu abinda ke motsi a jikinta, kora mata idanuwa sosai * Ummi* tayi tana nazarin ta murmushi tayi tace,”lallai akwai damuwa”. Komawa kitchen tayi ta ɗaura ruwa a wuta,saida ruwa yayi lam lam sannan ta fito falo, har yanzu jikin Aunty Sadiya a haka yake babu wani sauyi.
Hankali a kwance ta fara karantu wasu ayoyi cikin Alkur’ani mai girma, sosai Muryar ta yake amsa kuwa cikin gida,duk wani lungu da sako na gidan saida ya amsa da wani irin amo mara daɗin ji, sosai ganin haka yasa *Ummi* ƙara sautin karatun ta.
Wanin irin guguwa mai ƙarfin gaske ne ya taso, jin hucin sa yasa *Ummi* ta ƙara sautin Muryar ta, nan nan da nan guguwar ta ɗauke bat.
Bata daina karantu ba har saida taji Muryar Aunty Sadiya tana kiran sunan ta, murmushi tayi tace,”Har kin tashi”.?
“Daga duniyar mutuwa ba, wallàhi ina jin muryar ki amma bana iya motsa koda yatsan hannu na ne, innalillahi wa inna ilaihi raju’un wai menene yake faruwa, ina Yaya na? Waiyo Allah na, kuka Aunty Sadiya yake sosai ganin haka yasa *Ummi* ta zauna kusa da ita tana rarrashin ta, sosai jikinta yayi zafi kallon ta tayi tace” Aunty Sadiya Tun yaushe kika fara jin irin wannan abubuwan a gida”?
Shiru tayi yana nazari can tace” Gaskiya jiya ne kawai na fara jin irin wannan abun.
Daga nan babu wanda ya kuma cewa da ɗan uwan sa ƙala, har gari ya waye idanun su biyu babu wanda yayi baccin kirki saboda tsoro.
*******
Cikin wannan dare kuwa sosai Faruq ya shiga tashin hankalin ganin yanda *Musaddam* yake wani irin ihu da gurnani kira yake yana cewa,”Ki daina ƙonani zan fita daga jikin sa, tun yana magiya a hankali har ya koma hana yi da ƙarfin gaske, gabaki ɗaya jikinsa yayi shatin bulala ta ko ina, tsabar ruɗewa Faruq rasa inda zai tsaya yayi idan yayi nan ya dawo ya shiga nan.