HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Wata dabara ce ta faɗa masa cikin sauri ya ɗibi ruwa yayi Addu’a a ciki ya watsa masa, wani firgitatciyar ƙara daya sake saida gidan ya girgiza, daidai wannan lokacin ne wannan hayakin ya fice daga gidan Faruq.

Sauke ajiyar zuciya yayi ganin yana ya kwanta yana fitar da wani irin wahalallan numfashi.

 

Gyara masa kwanciyar yayi sannan ya hura masa addu’a shima ya kwanta,bawai dan bacci ba,a a kawai da dan samun hutu.

 

*******

Mummy kuwa gabaki ɗaya kasa bacci tayi saboda tsananta buguwa da zuciyar ta yake, tashi tayi ta ɗauro alwala ta fara gabatar da Sallah, addu’a sosai tayi akan ɗanta dama al’ummar Annabi baki ɗaya, gabaki ɗaya ji take sam bata cikin natsuwar ta, “Shin a wani hali kake ɗan? ” Nayi kewar ka sosai da sosai ina fatan Allah ya haɗa fuskar mu da alkairi.

Da haka barci yayi awan gaba da ita.

 

Koda garin Allah ya waye gida Faruq ya nufa bayan ya kulle*Musaddam* a gidan, yana zuwa kuwa ya tarar dashi kwance a falo suna bacci, sosai abin ya bashi mamaki dan kuwa daga *Ummi* har Aunty Sadiya babu malalaciya a cikin su.

Tashin su yayi ta hanyar kiran sunan su ɗaya bayan ɗaya, Sadiya tana haɗa ido dashi cikin sauri ta miki kamar zata faɗi ma tana cewa,”Barka da dawowa”.

Murmushi yayi yace,”ki dinga bi a hankali da kanki kinji dai na fadi miki”.

Kwaɓe baki tayi tace,”yanzu daga dawowa Sai faɗa”.?

“Yaushe nayi miki faɗa”.?

“Yanzu mana”?

“Zaki fara rigima ko”?

“Idan banyi maka ba wa zanye wa”.

Kallon ta yake cikin natsuwa can yace,”Kin faɗa lafiya kuwa”.

Sauke ajiyar zuciya tayi ta labarta masa duk abinda ya faru, sosai wannan abin ya bashi mamaki mattuka, jiki na rawa ya karasa gurin *Ummi* yana cewa,”Wai da gaske kece kika kori aljannu a cikin gidan nan a daran jiya”?

Murmushi kawai *Ummi* tayi mishi.

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sake yana sake godiya ga daya sama masa mafita…..
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

*NOT EDITED*

2️⃣7️⃣

_*You Need to Understand This. When Someone Betrays You, It’s a Blessing. Imagine Going Through Life Not Knowing That Someone Had Bad Intention Towards You. It’s the Almighty’s Way of Exposing Them. Be Grateful and Move on. It Won’t Be Easy but Remember It Could Have Been Worse!*_

 

______”Yaya Faruq ka bani labarin abinda ya same shi”.

“Ƙwantar da hankalin ki shalele yanzu yakike ji”.?

“Bana jin ƙomai ni dai dan Allah ka faɗa min abinda ke faruwa dashi”.

Labarta mata abinda ke faruwa yayi kamar yanda ya faɗa musu a gida “innalillahi wa inna ilaihi raju’un kawai *Ummi* take maimaitawa gabaki ɗaya ji tayi wani irin zazzaɓi mai zafi ya rufe ta,daurewa tayi tace,”Dan Allah ka kaini gun…

Dakatar da ita yayi cikin sauri yana mata nuni da motsin da *Musaddam* yayi.

Tashi tayi ta ƙarasa daidai inda yake ƙwance, da kai take karanto ayoyin Alkur’ani mai girma yanda kasan yana rike a hannun ta, karatu take tana hawaye Masu mattukar ciwo *Ummi* bata tsagaita da karatu ba saidai taji *Musaddam* yana tari cikin sauri ta nufi kitchen ta ɗibo masa ruwa,samun sa tayi a zaune yana ƙarewa falon kallo.

Wani irin zabura yayi lokacin da suka haɗe ido baki buɗe yake kallon ta so yake ya tuna da inda ya taɓa ganin wannan fuskar amma ina duk yanda ya so tuna wannan haliltar amma abu ya faskara.
Sunkuyar da kansa yayi kawai saboda sara masa da yake.

“Ga ruwa kasha Yaya*Musaddam*”.

Wani irin bugu ƙurjin shi yayi da yaji wannan murya dafe kansa yayi da ƙarfi jin yanda hajijiya yake son  ƙwantar dashi idanuwansa sunyi ja jazur, “Yaya*Musaddam* ka ƙarɓa ka sha dan Allah zaka samu sauki in Sha Allah”.

Haka kawai yaji sam ba zai iya mata musu ba,ƙarɓa yayi yasha yana lumshe idanuwansa” murya a dashe yace,”Nagode sosai”.

Murmushi tayi kawai tana mai jin daɗin yanda ya amsa babu musu, aje cup ɗin yayi daidai da dawowar faruq daga masallaci,sosai yayi mamakin ganin cup a hannun sa da alama ruwa yasha.

“Shalele ruwa kika bashi ne”.

Murmushi kawai tayi tace,”Eh Yaya”.

“Alhamdullahi Alhamdullahi Alhamdullahi”.

Allah cikin ikon sa har zuwa yamma babu abinda ya sake faruwa saidai Babu abinda yake cewa sosai zuciyar sa da ƙwaƙwalowar sa suke zabatar dashi da son tuno inda ya taɓa ganin wannan haliltar amma ko sau ɗaya bai tuno komai ba.

Kusan 5:pm ta miƙe tana cewa,”Yaya Faruq zan tafi gida kaga yamma ta gabato ga ruwan addu’a can na ije masa cikin gora dan Allah ka tabbatar yasha kafin yayi bacci kuma ka shafa masa ta ko’ina a jikin sa in sha Allah zakuyi  bacci cikin sallama”.

Godiya yayi mata sosai sannan ya bata kudi ko zata samu ta hau adaidaita, kin ƙarɓa tayi har ta kai bakin kofa taji kamar ana kallon ta cikin sauri ta juya, idanuwan su ne suka sarƙe dana juna murmushi ta sakar masa tana cewa,”Kaci abinci Kaji Yaya na”.

Hakanan yaji sam ba zai iya kin amsa mata ba, Nodding da kai kawai yayi yana lumshe idanuwan sa, sosai yake jin rashin daɗin tafiyar ta so yake ta zauna ganin ta dajin Muryar ta yana saukar masa da natsuwa.

Suna fita ya tashi ya nufi ɗakin sa, kallon kansa yayi a madubi sosai yayi mamakin ganin yanda suma yayi wa fuskar sa ado, tsaki yayi ya nufi toilet da niyyar yin wanka, daidaita ruwan yayi daidai yanda zai ishe shi wanka kamar ance ya sake kallon ruwan,jini ne mai kauri yana zuba da mugun ƙarfi, a firgice *Musaddam* ya fita daga toilet ɗin yana ambaton suna Allah.

Buɗe kofar ɗakin sa yake dan ya fita zuwa gun Faruq amma ina gabaki  ƙofar ta datse.

Duk yanda yaso ya buɗe kofar amma ina abu yaci tura,can bayan sa ya fara jin hucin iska cikin sauri ya juya dan ganin abinda ke faruwa, wani irin baƙin guguwa ne yake tashi can kuma ya haɗe guri ɗaya a hankali kuran ke washewa,wani irin baƙin aljanine ya baiyana, gabaki ɗaya fuskarsa babu ko kyawun gani , idanuwan sa ja jazir yana da ido ɗaya atasakiyar kai bayan guda biyu dake saman fuskar sa.

Harshan sa kuwa har ƙasa. Sosai *Musaddam* ya tsorata ganin wannan haliltan tsabar ruɗewa ma kasa furta komai yayi banda zufa babu abinda yake.

Cikin wani irin murya mara daɗin ji wannan aljanin yace,”Kayi kuskure mafi girma a rayuwar ka, wanda ina mai tabbatar maka sai kayi daka sani mara adadi, kana zaune lafiyar ka ka tashi ka janyo wa ƙanka masifu irin wanda baka taɓa gani ko ji ba, hana wannan yarinyar zuwa gidan nan shine kawai samuwar sauki daga cikin azabar da muka tana da maka, wannan gargaɗi ne idan kuma ba haka ba sai kayi daka sanin zuwan ka cikin wannan duniya”.

Yana gama faɗan haka ya ɓace ɓat, dube dube ya shiga yi yana karantu wasu ayoyi daga cikin Alkur’ani mai girma, buɗe kofar yayi yaji ta abuɗe da gudu ya fita daga ɗakin yana kiran sunan Faruq.

********
Koda ta isa gida da gudu ta faɗa jikin Umma tana kuka.

Da mamaki tace,” ke lafiyar ki kuwa”?.

“Umma bashin da da lafiya sosai wallàhi duk kaminsa sun sauya, ya rame yayi baki gabaki ɗaya baya cikin haiyacin sa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button