MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Babu buƙatar tambayar yasa tace,”yanzu yana ina shi, kuma wani irin ciwo ke damun sa”.?
Yanda Faruq ya faɗa mata haka ta ƙwashe ta faɗa wa Umma,sosai ta jinjina lamarin dan kuwa lamarin akwai rikitarwa.
Bata haƙuri tayi sannan ta sake ƙarfafa mata guiwa kan taimaka masa “kuma idan Abban ki ya dawo zansa yayi masa addu’a a ruwa ki kai masa in sha Allah”.
Godiya tayi wa mata sannan ta tashi ta shige ɗaki dan canza kaya.
**********
“Wai ni kuwa ko dai zuwa birnin zanyi dan na gane wa idona abinda ke faruwa dan kuwa naji shiru har yanzu”.?
“To nima dai maso nayi miki magana amma ganin kinyi biris da al’amarin yasa nima nayi shiru tunda dama ku nake wa tanadi”.
“A a akan me zanyi buris da ganima alhalin ya halasata aci”? “Tab ai mune akan gaba dan ƙwasan rabon mu, ita kuma wannan mayyar na tabbata wannan yaron tuni yayi barzahu da ita, wai ita mutumiyar kirki aikuwa nasan yanzu tana nan tana yabawa aya zakinta”.
“Wallàhi duk itace tayi sanadiyar rushe wancan tsarin nawa lokacin tun ina da sauran ƙarfi a jiki, koda yake ai ko yanzu nice ke da ikon tafiyar da al’amura cikin gidan dan kuwa yanzu kamar a tafin hannu na suke”.
Juyawa gefe Suwaiba tayi tana kallon ɗayan gefen gidan cikin zuciyar ta kuwa cewa take,”Tab ɗijam wai itace take tafiyar da al’amuran gidan, wallàhi da zarar na samu abinda nake nima wallàhi filo zansa na matse ki, yo me ake da ke kinci lokacin ki kina nema ki ci namu mtssss aikin banza”.
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_
2️⃣8️⃣
“_*You need to quit worrying about what people think. Honestly, it doesn’t matter. They’re entitled to their thoughts. At the end of your life, you’re not going to stand before people and give an account of what you’ve done. You’re going to stand before the Almighty.*_
_____Kiran sunan Faruq kawai yake cikin firgici, jin kamar kiran bana lafiya bane yasa faruq tashi cikin sauri ya tare shi gabaki ɗaya a kiɗime yake jikinsa kuwa banda rawa babu abinda yake, riƙe masa hannu yayi yana masa nuni da ɗakin sa, zaunar dashi yayi yace,”Ƙwantar da hankalin ka babu komai”.
“Faruq Al..jan..ni.”
Tashi yayi ya ɗauko masa wannan ruwan goran babu musu kuwa ya ƙarɓa ya shanye tas.
Ko cikakkiyar minti ɗaya ba’ayi ba ya fara barci.
Jinjina karfin wannan addu’a yayi sannan ya haura saman ɗaki nasa dan ganin abinda ya firgita*Musaddam* haka.
Babu komai cikin ɗakin komai a gyara yake tsaf kamar babu mai shiga ɗakin, zuban ruwa yaji daga toilet hakan yasa ya nufi toilet ɗin kai tsaye.
Nan ma babu komai, kashe ruwan yayi sannan ya fice daga ɗakin bayan ya ɗaukar masa bargo.
Saida yabi lungu da saƙo na gidan da addu’a sannan ya kwanta.
Tun da *Ummi* ta farka da asuba bata sake komawa bacci ba, waina mai ɗankaran daɗi ta soya Umma kuma tayi mata miyar taushe wanda yaji manshanu da tan taƙwashi ,saida suka gama tas sannan ta dama kunun tsamiya babu abinda ke tashi cikin kunun nan sai ƙamshi.
Wanka tayi ta sako duguwar rigarta mai kyau.
Cikin natsuwa ta fita daga gidan bayan tayi sallama da Umma har ta kai kofar gida umma ta ƙwalla mata kira, dawowa tayi cikin shagwaɓa tace,”Umma”.
“Au fushi makike kenan ko? To jeki dama ruwan addu’a da Abban ki yabani ne nake son na baki ki kai masa, amma shikenan tunda bakya so”.
Da gudu ta ƙaraso gun Umma tana cewa,” ayi hakuri abani Umma na”.
Dariya duk sukayi Sannan ta miƙa mata ruwan addu’a ahade da sake jaddada mata yanda za’ayi amfani dashi.
Koda ta isa gidan suna kwance a falo da alama barci suke salamar ta yasa Faruq miƙewa yana mata sannu da zuwa, saida ta gaishe shi sannan ta nimi guri ta zauna.
“Yaya Faruq fatan dai babu abinda ya faru bayan tafiya ta”?
“To alhamdullah tunda an samu sauƙi ba kamar da ba”.
“Alhamdullah yanzu kunci wani abin ne”.?
“A a Kinga babu yanda za’ayi na tafi na barshi a cikin wannan halin ina tsoron abinda zai faru bayan fita ta”.
“Kenan babu abinda kaci”
“Eh Wallàhi tun jiya rabo na da abinci shalele”.
“Allah ya baka lada Yaya Faruq.”
“Amin shalele na”.
Murmushi kawai tayi ta miƙe ta shiga kitchen, ɗauko plate da cup tayi ta zubawa Faruq waina da kunun tsamiyar da tayi, tunda ta buɗe kular kamshi ya mamaye falon.
Tsokanar ta ya shiga yi ita kuma tana zullewa dan kuwa addu’ar ta bai wuce ganin farkawar*Musaddam* ba.
Kwance yake yayi lamo, sumar fuskar sa sunyi yawa amma kuma sun ƙara wa fuskar sa kyau da cikar zati, leɓen bakin sa sun bushe amma duk da haka laushi da sheƙin su basu gushe ba, idanuwansa a lumshe suke zara_zarar suman idanuwan su sunyi luf_luf dasu, saidai kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ya rame kuma fuskarsa ta kara haske.
Shi kuwa *Musaddam* tun sallamar da tayi na farko ya farka dan kuwa da tunanin ta ya kwana haka yasa yana jin Muryar ta ya farka, duk wani motsi na ta a idon sa take yana kallon ya ta kasar ido, buɗe wannan wainar yasa yaji wani mugun yunwa ya taso masa,motsawa yayi yana salati kamar lokacin ya farka, ganin haka yasa tayi wani ajiyar zuciya wanda saida Faruq ya juya ya kalle ta.
Sunkuyar da kai tayi dan kuwa bata so ya ɗago ta.
“Aboki ka tashi lafiya”.?
“Lafiya ƙalau alhamdullahi fatan kai ma haka”?
“Alhamdullahi ga abinci sauko ka ci”.
“Haba malam daga tashi na”?
“Eh mana ai babu sanya abinda kafi so ne ai”.
“Malam Karka mayar dani acici mana”.
Gabaki ɗayan su dariya suke banda ita dan kuwa sunne kanta tayi jikin hijabin ta tana wasa da yatsar hannun ta daga sama taji yana cewa,”Ƙanwa ta yau babu gaisuwa ne”?
Gabaki ɗaya *Ummi* ji tayi ina ma ƙasa ta buɗe ta shige ciki abinta tsabar kunya,wai ita fa jira take idan suka gama magana sai ta gaishe shi.
“Kayi haƙuri gani nayi kuma magana shiyasa, ina ƙwana ya jikin naka fatan dai ka samu lafiya yanzu”?
Da mamaki yake kallon ta can yace,”Duk wannan tambayar wani ɗaya kuma lokaci ɗaya da wani baki zan amsa to”?
Murmushi tayi tace,”Amin afuwa dan Allah”.
Shidai Faruq shiru kawai yayi yana sauraron su yana kuma godiya ga Allah daya haɗa jikin su lokaci ɗaya,dan da jinin bai haɗu ba ko albarkacin magana ba zata samu daga *Musaddam* ba,hakan kuma yana nufin samu matsala gurin shan duk wani abu daya fito daga hannun ta.
Tashi tayi ta ɗauko masa plate shima ya zuba masa, kallo ɗaya yayi wa wainar yaji duk yunwan kwanakin da yayi sun dawo sabo, miƙewa yayi ya shiga ɗakin sa dan wanke hakuran sa.
Shiru shiru babu *Musaddam* babu labarin sa abu kamar wasa har kusan tsawan mintina talatin, kallon Faruq tayi tace,’Yaya gaskiya ina ji a jikin na babu lafiya shirun sa yayi yawa”.
Murmushi faruq yayi yace,”Tunda kin matsa bara na duba shi,amma idan *Musaddam* ne yana iya yin awa ɗaya yana wanka ba damuwar sa bane ba”.
“To ni dai kawai ka duba”.
“Shikenan shalele idan ya koro ni ai sai na rama akan ki”.
Murmushi kawai tayi duk da kuwa yanda take jin zuciyar ta na bugawa da mattukar karfi, koda Faruq ya tafi kasa zama tayi tana ta kaiwa da komowa.