HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Jin firgitatciyar ƙarar da faruq yayi yasa ta mike da gudu har tana fadi ta haura saman ɗakin na sa.

Tsayawa tayi cak gabaki ɗaya ji tayi komai na jikinta ya daina aiki ganin wannan mumunar yanayi da masoyin ta Habibin ta muradin rai ta yake ciki, zubewa tayi a gurin ta fashe da wani irin marayar kuka”.

Faruq kuwa tunda yayi wannan salatin ya zuɓe a gurin kallo ɗaya idan kayi masa zaka dauka a cikin haiyacin sa yake nan kuwa tuni ya daɗe dayin suman tsaye.

Lura da hakan yasa ta share hawanyan ta ruwan gora dake gefen ta ta ɗauka ta shafa masa a fuska ajiyar zuciya ya sauke yana kiran Wallàhi yana raye bai mutu ba……

 

*Rashin comment yasa gabaki ɗaya bana da gwarin guiwar typing, idan kuka gyara nima na gyara* ????????????

 

*Safnah Aliyu jawabi* 08136746004

????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_

2️⃣9️⃣

_*A lizard decided to jump from the top of a tree. All animals were shouting ‘it’s impossible’. Because the lizard was deaf, he thought they were cheering. He jumped and landed safely. Moral: Be deaf to negative people and you will succeed*_

 

________Jini ne malele a ɗakin duk bangwan ɗakin shatin jini ne alamu anyi kokawa kafin a samu nasara akan sa, jini ke fita ta hanci sa da bakin sa harshan sa sun zazzago wuyan sa  kamar anyi masa yankan rago, ƙarasawa gurin faruq yayi da rarafe ɗago kansa yayi yana kuka.

“Aboki wallàhi ba zaka mutu ba in sha Allah karka min haka bana fatan ganin ranar mutuwar ka, in sha Allah kai ne zaka fara ganin nawa gawar”.

Jin yanda yake sambatu cikin kuka tace,”Mu kai shi asibiti dan Allah”.

Sai a sannan zancan asibiti ya faɗo masa,da gudu ya fita yana kiran mai gadi. ɗaukar sa sukayi suka saka cikin mota da gudu ya bar harabar gidan ,banda kuka babu abinda suke har suka isa cikin asibtin, wannan karon baban asibiti suka nufa dashi wanda dama tuni shine baya kaunar zuwa a cewar sa”asibiti ɗaya ya kamata talaka da Mai Kudi su rinka zuwa”.

Babu ɓata lokacin akan shiga bashi taimakon gaggawa,kiran Mummy Faruq yayi yace ta same su asibiti *Musaddam* babu lafiya.

Duk yanda Mummy ta kai da zurfin ciki ko kuma dakiya saida ta zubda ƙwalla kuma ta faɗa musu abinda ke faruwa saidai har yanzu bata faɗa musu dalilin faɗawan shi cikin wannan hali ba, alƙawarin data ɗaukawa Muhammad yana nan acikin jinin ta.

Kafin kace me, asibiti ya cika da ƴan uwa da abokin arziki kowa dai Fatah shi Allah ya bashi lafiya.

Sai da Dr suka kwashi tsawan a wannin akan sa sannan babban su ya fito dan gaya musu halin da ake ciki, cikin sauri Faruq da Mummy suka nufi Dr suna tambayar sa jikin *Musaddam* ɗin.

Share gumin fuskarsa yayi yace,”Tabbas nayi mamakin wannan al’amari dan kuwa abin akwai sarkakiya wato bayan mun shiga dashi sai mukayi ƙoƙarin ganin mun bashi gudumawa irin namu na Dr,amma bin mamaki shine duk inda muka ɗinke sai ya ƙwance,kusan rabin awa muna abu ɗaya, ganin haka yasa na yanke shawarar yin karatu duk da kuwa gurin babu tsarki amma wannan kamawa tayi.

Allah cikin ikon sa ina karantu ina dɗinkewa kuma baya ƙwancewa kamar yanda yayi  a baya,saboda haka dole sai kun tashi tsaye da addu’a,sadaka da dai sauran su, dan kuwa wannan ba ciwon asibiti bane ba”

“Yawwa kuma ga shawara akwai bukatar kuyi nisa dashi daga duk inda kuka san yana da matsala kuma ince suka samu saɓan ko da mutum ɗaya ne daga ciki su, Allah ya bashi lafiya”.

Cikin sauri mummy ta tare shi tana cewa “Dr Fatan dai yanzu jinin ya tsaya, ya maganar ciwu kan  dake jikin sa”?

Murmushi yayi dan ko ba’a faɗa ba wannan soyayya da ruɗewa sai uwa baya goya marayu yace”karki damu Hajiya in sha Allah”.

Godiya tayi masa sannan ya shige office ɗin sa.

Sauke ajiyar zuciya Mummy tayi tana karanto.

“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un”

“Karki damu Mummy in sha Allah komai zai zo mana cikin sauƙi tunda ya farfaɗo da yardar Allah”.

“Allah yasa”.

“Kinji abinda Dr yace yanzu menene mafita”.?

“Wallàhi bana da kowa acikin duniyar nan daga Allah sai kai da ƙanwar sane kawai kuka san wannan zancan, gudun kar itama ta faɗa ciki hali irin wanda yake ciki yanzu yasa nayi nisa da ita daga garin nan gabaki ɗaya, Faruq ka taimaka min idan akwai inda kake tunanin zamu kai wannan yaron mu kai shi dan Allah”.

Kuka Mummy take sosai kamar ranta zai fita.

Matsowa gurin *Ummi” tayi ta kama hannun mummy itama kuka take.

Da mamaki Mummy tace,” *Ummi* na daga ina kike? Waya faɗa miki muna nan, ko dai kema wani kika kawo”.?

Sosai Faruq ya shiga ruɗu ganin yanda Mummy take tambayar ta alamu sun nuna sun san juna.

“Mummy dama kin san tane”.?

“Eh a anguwar mu suke ai”.

“Ikon Allah to ai itace wacce nake faɗa miki cewa ɗiyar gwaggo ta wacce take masa addu’a”.

Baki buɗe Mummy take kallon ta wani irin runguma tayi mata a tare suka fashe da kuka mai cin rai.

Ɗago kanta*Ummi* tayi tace”Yaya Faruq duk na saurari abinda kuke tattaunawa idan babu damuwa mu tafi gida muyi wa Umma bayani idan yaso sai mu kai shi gun Ka’ka  tunda shima yana maganin irin wannan lalurar da yardar Allah”.

Dafe kansa yayi yace,”Kash wallàhi shafi na mance da zancan sa, babu lokaci tashi mu tafi”.

Fatan alkairi Mummy tayi musu Sannan suka tafi,koda sukayi wa Umma bayani sosai ta jajanta lamari.

“Babu damuwa ai kuna iya zuwa fatan mu Allah yasa a dace  zan kira su na sanar dasu, amma dai dole sai dai ku tafi akan lokaci dan kuwa yanzu hanya babu kyau”.

“In sha Allah”.

“Umma nima zan tafi naga Ka’ka”.

“Shi  zaki tafi gani ko kuma jinya zaki tafi”.

Murmushi kawai duk sukayi ita kuwa sai wani sun_sunkuyar da kai take.

Koda suka koma asibiti hannu suka sa aka salame su da alƙawarin Dr zai rinka zuwa har garin yana duba shi duk bayan kwana biyu.

Allah cikin ikon sa sun isa garin Suleja cikin abinda bai fi awa uku ba, Suleja gari  ne mai albarka gari mai tarin ni’ima sosai *Ummi* take son zuwa garin saboda abubuwan burgewa da al’adun garin ,saidai kasancewar wannan zuwan bana Lafiya bane yasa sam bata ma kula da abubuwan dake burge ta game da wannan gari ba.

Nesa da cikin garin akwai wani ƙauye mai suna Caza, Wannan ƙauye ya tara malamai  kama dana addini   kai harma dana zamani shiyasa Mazauna cikin wannan ƙauye suka fita da ban acikin wannan gari.

Tun daga shigowar ka zaka fahimci Allah ya azurta su da shuke shuke masu mattukar burgewa da sha’awa.

Tar ba mai kyau suka samu Kasancewar an san da zuwan nasu haka yasa aka amshe su cikin aminci.

Cikin zauran gidan akwai ɗakuna biyu cikin ɗaya daga ciki aka sauke su wanda ya kasance a gyara tsaf,babu abinda ke tashi a ciki sai kamshi mai  sanya salama ga ruhi.

Wani tsoho na hango wanda kallo ɗaya zaka masa ka fahimci alhamdullah tsufa tayi kyau duk da kuwa yayi sama da shekaru ɗari da goma, amma babu firgici irin na tsufa babu rikici babu hayani alhamdullah duk hakan sun samu ne saboda yaranta ta gino bisa tafarkin tsoron Allah da riko da Alkur’ani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button